Labarai

Martanin Ali Nuhu Da Falalu A Dorayi Kan Kalaman Ladi Cima

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Instagram na ta ce-ce-ku-ce kan wasu kalamai da ɗaya daga cikin ƴan wasan Kannywood ta yi na cewa ana biyanta naira dubu biyu zuwa dubu biyar a duk lokacin da ta yi fim.

A hirar da BBC ta yi da ita a cikin shirin Daga Bakin Mai Ita, Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ta kasa mallakar muhalli shi ne tun daga lokacin da ta soma wasan kwaikwayo a zamanin mulkin Yakubu Gowon, ba ta taɓa samun kuɗi a dunƙule dubu ashirin ko talatin ko hamsin idan ta yi fim ba.

Me daraktoci da furodusoshin Kannywood ke cewa

Dangane da wannan lamari, BBC ta tuntuɓi wasu daga cikin daraktoci da furodusoshin Kannywood kan iƙirarin da Ladin Cima ta yi kuma sun yi mana ƙarin bayani.

Falalu Ɗorayi

Falalu Ɗorayi yana daga cikin manyan daraktoci a Kannywood kuma yana daga cikin daraktocin da ke saka Ladin Cima a cikin fim. A cewarsa, ya yi mamaki dangane da kalaman Ladin Cima inda ya ce tun da yake sa ta a fina-finai, bai taɓa biyan ta ƙasa da dubu ashirin ba inda ya ce yana biyanta talatin zuwa arba’in.

“Ba a yi kwana goma ba na yi aiki da ita kuma abin da na bata shi ne naira dubu talatin,” in ji shi.

Ya bayyana cewa a girma irin na Ladin Cima da yadda ake kallonta a matsayin kaka a Kannywood babu wanda zai biya ta hakan idan ba yara ƙanana waɗanda suke tasowa ba.

Falalu Ɗorayi ya bayyana cewa bai taɓa samun matsala da ita ba “hasali ma haka kawai ta kan kira ni ta ce wane ya ba ni kuɗi ta yi mani godiya ta kuma ce na kira shi na yi mashi godiya”, in ji shi.

Ya ce haka kawai idan mutum ya yi mata alkhairi tana kiransa ma ta faɗa masa inda kuma ya ce a lokacin da ta samu matsalar muhalli ta samu kuɗi daga wurin ƴan Kannywood sun fi miliyan guda.

Ya bayyana cewa ko a fim ɗin Gidan Badamasi ta yi masa sin biyar inda ya biya ta dubu araba’in.

Ali Nuhu

Haka zalika BBC ta tuntuɓi Ali Nuhu inda ya ce ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, kuma a cewarsa ko aikin da ta yi masa na ƙarshe a fim ɗin Alaƙa duba arba’in suka biyata.

Ya bayyana cewa bai kamata ta yi musu kuɗin goro ba duk da a cewarsa akwai masu biyan jarumai dubu biyar.

“Ka san wasu suna yi wa jama’a yadda suka ga dama ne, wani sai ka ga ya kyautata maka wani kuma ka ga bai kyautata maka ba.

“Ya kamata idan mutum yana bayani ya rinƙa bambancewa ya ce wasu suna kyautata mana ya kuma ce wasu ba su yi ,” in ji Ali Nuhu.

Ali Nuhu ya ce kalaman da Ladin Cima ta yi sun ja masa zagi sosai a wurin jama’a domin fim ɗin baya-bayan nan da tayi tare ta yi da shi.

Ali Nuhu ya ce bai ga laifin ɗan kallo da ke zaginsa ba saboda watakila bai san yadda abin yake ba.

BBC ta sake tuntuɓar Ladin Cimma

Sakamakon irin ce-ce-ku-cen da wannan lamari ya jawo, BBC ta sake tuntuɓar Ladin Cima.

Ta ce mutane ba su fahimci kalamanta ba duk da cewa akwai fina-finan da ake biyanta dubu biyu zuwa biyar amma akwai furodusoshin da su kan kalli darajarta su yi mata alkhairi a fim.

A cewarta, ba ta taɓa kallon furodusa ta ce masa ga abin da zai biya ta ba.

Ta ce akwai ƴan Kannywood da suke kyautata mata a ko yaushe kamar su Ali Nuhu da Falalu Ɗorayi da Hadiza Gabon da dai sauransu.

Ta ce “Ali Nuhu ya kan je gidana ya yi mani alkhairi kuma babu abin da bai yi min ba,”. Haka kuma ta ce Hadiza Gabon a kwanakin baya ta ba ta kyautar dubu 300.

A cewarta, gidan da take ciki a yanzu ƴan fim ne suka siya mata bayan matsalar da ta shiga a kwanakin baya.

Daga bbchausa

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button