HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 18

 Halin Girma    18

Hafsat Rano

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**************

Shigowa Mamma tayi, ta same ta a tsaye ta ma rasa abinda zatayi. Hannun ta, ta kama ta zaunar da ita, ta bud’e jakar da suka zo da ita ta ciro turare me dadin kamshi na daban ta fesa mata, ta duba fuskar ta sannan tace

“Ki kwantar da hankalin ki dan Allah,bari na duba kayan da yan matan nan suka kawo, ba za’a rasa alkyabba ba. ”

Fita tayi sai gata ta dawo tare da daya daga cikin yan matan, ta russuna har k’asa ta gaida Iman din da gabatar da kanta da sunan ta Ummimi sannan ta matsa daga gefe,

” Tashi ta taimaka miki ta saka miki. ”

Mamma tace tana murmushi, wani banbarakwai Iman taji, ta tashi cikin sanyin jiki yarinyar ta hau saka mata alkyabbar cikin k’warewa. Ji take tamkar mafarki, kamar zata farka taga komai yana yadda take. Har ta gama gyara mata, ta kawo sauran kayan ta sassaka mata ta fito sosai a gimbiyar ta mamaki be bar ta ba.

   

   Khadija da Zahra ne suka shigo, kusan sa’annin Iman din ne a family, doki ya saka su zuwa suka Iman din suma su bawa idon su abinci, suna shigowa dakin suka ganta cikin shigar da tayi masifar mata kyau, shigar alfarma.

   Hoto Zahra ta ciro waya ta hau daukar ta, kala kala har da videos dan dole ne yau followersa dinta na Instagram su kara kiyayarta.

   Kiran ta ya sake yi dan da gaske ya matsu ya ganta, irin matsuwar ba don idon sirikai ba, da dumbin jama’a da sai dai kawai ta ganshi a duk ma in da take.

   Mamma ce ta dakatar da hotunan haka, tace suyi mata rakiya zuwa in da Muhammad din yake, ko tace Yarima Muhammad dan sunan kam be chanchanci a dinga fadar sa haka nan kai tsaye ba.

    Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, haka ta tashi tana turo baki. Tare suka fito da biyu daga cikin hadiman yan matan nan, suna daga bayan ta suna take mata baya, domin da gaske Ammi tayi musu gargadi akan surukarta ta, su kula da ita da komai nata

    Suna zuwa daf da seat room din suka soma jin hayaniyar maza,amma ba irin hayaniyar da zaka ji ba irin ta wasu mazan marasa aji da tsari. Hayaniya ce ta nuna farin cikin su da taya murna cikin ilimi da wayewa. Ji tayi kamar ta koma da baya, dan yadda ta tsani taro na maza har ya zama tana ciki, bata san kalar kunyar da zata sha ba, dan da alama dukkan su masu surutu ne. Bata dai ji muryar uban gayyar ba, ta kamo addu’a ta soma yi har ta samu nutswar ta 

“Iman.” Ya kirata yana karasowa wajen, tare suke da Habib da abokin sa Sadeeq. Murmushi tayi masa

“Uncle Khalil, ashe kazo.”

Murmushin yak’e ya maida mata, ya tuna da warning din da Moh ya kada masa, duk da yayi kokari matuka be saba ka’ida ba, yanzu ma dole ce ta sakashi zuwa tun da dai ba zai ki zuwa daurin auren Zeenat ba.

“Nazo Iman, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya.”

“Amin.” 

Ta amsa a ciki tana jin babu dadi, lokaci daya yanayin sa ya sauya, yayi saurin barin wajen yana yin gaba, suka gaisa da Sadeeq da Ya Habib sannan suka wuce zuwa in da zasu.

   Sallama Ummimi tayi daga kofar, ta sanar da zuwan Iman din kamar yadda yake a tsarin masarauta, murmushi Moh yayi me aji, ya mike da kansa yana hararar su Ja’afar

“Amaryata tazo dan Allah muna bukatar privacy.”

Dariya suka kwashe gaba daya, ya hade rai da gaske ba da wasa ba,su ka hau tsokanar sa amma yayi fumfurus yace wallahi sai sun fita. Musaddik ne yace

“Ai ka bari ta shigo mu gaisa ko? Sai mu fita daga baya.”

Da kai ya amsa ya koma ya zauna yana jin rawanin da ke kansa ya soma gundurar sa. Shigowa sukayi bayan sun saka Iman din a tsakiya, idanun ta da tayi kokarin saukar dasu k’asa sosai suka shiga cikin nasa, da sauri ta dauke idon ta, ta zauna su Zahra suka sakata a tsakiya. Gaishe su sukayi suma suka amsa sannan suka gaisa da Iman din da take amsa musu ciki ciki dan ji take kamar ace fit ta fice saboda tsoro.

“Capt. Lets snap please.” 

Wani abokin sa Gbenga yace yana kallon sa

“Ok sir.” Yace yana tashi, taimaka mata Zahra tayi, ta isa wajen da yake a tsaye, daga gefen sa ta tsaya, sai taji kamar ana saka abu ana bubbuge mata kafafunta. Hannun ta taji yana laluba ta cikin babbar rigarsa, ta daga kai da nufin kallon sa, shima a lokacin kallon ta yake, Ja’afar yayi sauri ya dauki scene din, hoton yayi masifar kyau, duk suka hau yabawa.

   Masifaffiyar kunyar da take ji ta hanata sakewa sam, duk da haka an dauki hotunan sosai sun fita, banda camera man suma wayoyin su duk babu na banza. 

   Wani irin laushi hannun sa da yake cikin nata taji,ta tuna kullum cikin safar hannu yake zuwa mata, duk sanda zata ganshi hannun sa da kafar sa, na sakaye, sai yanzu ta gani dalilin nasa na yin hakan.

  Mammatsa mata hannun ya dinga yi, ya hanata sakat ya sakata a  wani irin yanayi me wuyar fassarawa, gashi ya saka shi cikin rigar yadda ba wani wanda zai lura, sai da aka gama hotunan tas sannan suka fita suka barsu da nufin idan sun gama gaisawa sai su fito a shiga cikin gidajen ayi sauran hotunan a cewar Musaddik.

   Kamar me jiran kiris kuwa, suna gama ficewa ya saka dukkan karfin sa, yayi hugging dinta kamkam yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. 

   

“Alhamdulillah.” Ya furta yana murmushi

“Mrs Muhammad Ahmad Santuraki.”

Ya rada mata a kunnenta, ture shi tayi tana turo bakin ta gaba, ya tsaya yana kallon ta dan be taba sanin ta iya shagwaba ba sai yanzu

“Me yasa kayi haka?” 

Tace cikin dan daga murya ita a dole ya bata mata rai, riko ta yayi da sauri ya dora hannun sa akan lips dinsa yace

“Shssh… Ba’a dagawa miji murya babu kyau.”

Kokarin ture shin ta cigaba da yi amma sam ya hanata damar hakan, sai ma sake manne ta da yayi sosai da jikin sa suna shakar kamshin juna. Luf tayi ta daina motsawa kowa na sauraron bugun zuciyar dan uwan sa. Wajen minti daya suna a haka kafin ya saketa yana jan ta suka zauna a saman kujerar, ya rik’e hannayen ta yana kallon cikin idanunta 

“I promise you ba abinda kike tunani bane, zan miki bayanin komai amma ba yanzu ba, yau ranar farin ciki ce, let’s not discuss duk wani abu da be shafi ranar ba kinji matata? ”

Turo bakin ta sake yi, ya saka hannu ya shafa yana murmushi

” I love that. ” Saurin rufe fuskar ta tayi kunya na kamata

” Itama kunyar duk ina so, komai ma ni so nake kinji? Amma dai ki ajiye mana zuwa sanda zamu tare a gidan mu, ko nawa ne zan biya na siya. Bana so a samu matsala dan zai iya yin abinda ban shirya ba. ”

Da sauri ta gyara bakin ta, ta kuma gyara zama tana matsawa kadan, matsowa yayi ta sake matsawa ya sake matsowa kafin ta samu damar sake matsawa ya saka hannu ya tokare ta, ya matso da fuskar sa daf da tata, tayi saurin runtse idon ta tana jin kamar zata saki fitsari. Light kiss taji yayi mata a saman idonta dake a rufe.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button