HALIN GIRMA 20

Halin Girma 20
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Gaban Iman din ne ya dinga faduwa sanda taji tashin algaita da bud’a a lokaci daya, rik’e hannun Mamma tayi tamau bayan sun dawo daga wajen su Abba da wajen Gaji. Zaunar da ita Mamman tayi tace tana zuwa Amaani tayi saurin dawowa ta manne kusa da ita hakan ya saka ta dan ji dama dama. Mukullin motar da Abba ya damka mata a hannun ta da wasu abubuwan ya sakata shiga yanayin da ta shiga, har yanzu bata bar mamakin yadda abubuwan suka sauya salo ba, wanda bata taba tunani ko hasashen hakan zai faru da ita ba.
Bayan kamar minti biyar sai ga Mamma nan ta dawo ta kalli sauran tace
“Matar nan bata da kirki sam, bansan me yake damunta ba, amma ni dai na fad’a mata lallai ta shirya tazo ta kai Iman dakin ta, idan ma wani abun ne yake damun ta ko hassadace ita ta sani, na dai bata girmanta.”
“Toh ai Mamma kina gani kinsan bakin ciki take, dama kin kyale ta kawai mu kadai mun isa.”
“Ai ba haka ake ba, mu muka zo muka same ta kuma duk tsiya dai itace marikiyar Iman din.”
” Toh yanzu zata je din ko yaya?”
” Ban san mata ba wallahi, na dai fita ai ni dai,ruwanta taje ruwanta taki zuwa, babu abinda za’a fasa.”
” Wallahi kuwa, Allah ya kyauta.”
” Amin.” Tace tana zama.
Kayan Iman din aka gama fitarwa, aka saka a booth din motocin, sannan suka shigo da kansu su uku, suka ce sun zo daukar amaryar su, akayi barkwanci dai tsakanin su da su Mamma sannan suka fita su kuma su Mamma suka fito da Iman din.
A harabar gidan suka hadu da Mama, ta yafa mayafi ita da Aunty Muhibba, kallo daya Mamma tayi mata ta dauke kai suka fice, bayan su suka bi, suka tarar an gama tsara mutanen kowa ta samu mota ta shiga, kowacce mota da kayyadadden mutanen da za’a saka kuma kowa ya samu an shirya komai yadda ya kamata.
Motar amarya ce kawai ta rage sai guda daya da tazo a karshe, wasu ne suka shiga dayar tare da Aunty Muhibban sai Mamma da Mama suka shiga ta amarya suka sakata a tsakiya kamar yadda ake yi. Chan jikin kofar motar Mama ta makale taki yarda ta rabi Iman din, jawo ta sosai Mamma tayi jikin ta ta dora kan Iman din a saman kafadarta ta kwanta sosai.
Lamido Crescent suka nufa in da nan ne ainihin gidan Iman din, sojojin da ke zube birjik a gaban gidan ya saka mutane sake jinjina lallai Babba ne Muhammad din, gida ne hadadden gaske wanda dama chan a nan Muhammad din yake amma an masa gyara sosai da ba zaka taba cewa ba a lokacin aka gina shi ba. Tsaruwar gidan da yadda aka kawata faluka da dakunan gidan da kaya na alfarma ya kusan saka Mama shan k’asa, ta rik’e hannun Aunty Muhibba dan da gaske ta tsorata da yadda taga gidan. Falo biyu ne daya sama daya k’asa sai dakuna biyu a sama, uku a k’asa kuma kowanne Masha Allah kaya ne aka zuba na alfarma, kar Azo batun kitchen wanda duk yadda Mama ta kai ga kure siyayyar ta sai taga ta raina kanta, komai na ciki unique ne ga wasu shegun electronics wasu ma bata san menene amfanin su ba. A daddafe ta daure ta shiga ko ina dan yadda kowa ya zura ido a kanta kowa so yake ya ga yadda zata shiga dimuwa ko ma ta kasa rik’e bakin cikin ta har ta nuna a samu abin fad’a.
Basu wani jima a gidan ba suka fito, dama saboda dai su san gidan Iman din tunda yanzu ba anan za’a fara kaita ba, masarauta zash dan suna da shagalin bikin da zasuyi su ma.
Kin yarda Mama tayi ta koma motar amarya ta fad’a wajen Aunty Muhibba dan komai zai iya faruwa idan ta zauna gata ga Iman din. Bata taba tunanin kalar wannan daukakar ga Iman din ba. Sai gashi in da Iman din taje ko zata je nan gaba bata isa ta taba kai wa wajen ba har abadah. Tayi mata nisan da za’a iya cewa ya kai tsakanin nisan sama da kasa.
Bata kara raina kanta ba sai da ta gansu a cikin masarautar, babbar masarauta irin ta Kano, da bata kawo kanta a ciki ko da wucewa tazo yi kuwa bata taba hasashen kasancewar ta ba.
Wani tsari akayi na tarbar su, wanda ya sake bawa mutane mamaki, kana kallon fuskokin kowa zaka tabbatar da yadda suke ciki. Sanda suka isa bangaren Fulani kakar Moh din da kanta ta taso ta rungume Iman a jikinta, ta kuma zaunar da ita a kusa da ita, jikokin ta sauran suka hau dariya suna tsokanar ta, ta biye musu suka dinga yi kamar ba matar sarki ba, duk da ba kowa ne aka bari ya shiga wajen ba, iya makusantan Iman din ne daga Mamma sai Mama sai dangin Abba su biyu sai Amaani da take makale da Iman din, sauran mutanen a wani babban falo aka ajiye su aka shiga gabatar musu da nau’ikan abinci kala-kala na gida dana kasashen ketare.
Sun dan jima a shashen Fulanin mutane daban daban manya wanda suka zo bikin suka dinga zuwa suna ganin Iman din, kunya kamar ta nutse ta dinga boye kanta wanda hakan ya saka suka kara son ta kowa ya dinga yabon ta yana yaba sa’ar da Moh din yayi.
Rakasu bangaren Moh din Fulani ta saka akayi, wanda dama chan aka ware wa Iman din da wanda zasu tayata zama kafin gobe yan uwan ta su dawo shagalin da za’a yi a babban Hall din gidan da tun a ranar an gama tsara shi an kawata shi.
Two bed room ne sai falo da kitchen, tuni masu kula da shashen sun gyara komai, daya daga cikin dakunan aka kaita, sannan su Mamma sukayi mata sallama aka bar mata Amaani, khadija, Zahra sai su Amira, duk dai yan matan aka bari a zuwan su Mamma sai su dawo gobe. Kamar zatayi kuka haka taji da zasu tafi amma kasancewar ta me dakiya ta daure kawai tayi shiru tana cigaba da kallon komai tamkar almara.
A falon su Amira suka zauna bayan sun raka su Maman sun dawo suka dasa kallo da hirar gidan Iman din da irin yadda aka karbe su a masarautar. Tana jin su sama sama bata fito ba sai ma tayi kwanciyar ta saman gadon dakin tana shakar kamshin da ta tabbatar da kamshin sa ne dan shine kamshin da ko da yaushe take jin sa yana yi.
Tana kwance taji kamar motsi, ta daga kai ta duba, sai taga kofa a jikin karshen bangon dakin wanda sai ka lura sosai zaga gane don ta saje da kalar curtains din dakin. Budewa taga kofar tayi, ta mike daga kwanciyar da tayi da sauri kafin ta gama daidatuwa har ya shigo, cikin shigar bakin dogon wando da riga armless, cikin mamaki take kallon sa har ya shigo cikin dakin gaba daya. Mikewa tayi tsaye lokacin da ya karaso daidai in da take. Ya saka hannu ya shafi gefen fuskar ta.
“Wai tsoro kika ji?”
Da ka ta amsa, ya rik’e ta ya zauna a gefen gadon sannan ya zaunar da ita a daidai kusa dashi, k’asa kallon sa tayi, ya zuba mata ido yana kallon ta kamar a ranar ya soma ganin ta. Farin cikin da yake ciki a yau din mara misaltuwa ne, ba zai iya tafiya adamawa be sake ganin ta ba shiyasa kawai ya hakura da zuwan sai da safe.