Labarai

Buhari Yayi Gargaɗi Ga Shugabanni Jam’iyar Apc Dasu Daina sa’in’sa A Tsakanin Su

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi gargaɗi ga shugabanni da ƴan jam’iyar APC da su daina nuna wa juna yatsa da sa-in-sa a junansu, yayin da jam’iyar ke tunkarar babban taron ta na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris.

An ruwaito cewa APC ta sake nutsa wa cikin rikici bayan da gwamnoni 19, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai su ka hamɓarar da kujerar shugaban kwamitin riƙo na jam’iyar, Gwamna Mai Mala Buni, inda a ke zargin da umarnin shugaban ƙasa su ka aikata hakan.

Daga bisani sai Buhari ya ja kunnen ƴan jam’iyar da su ci gaba da jajirce wa da haɗa kai domin jam’iyar ta ci gaba da tafiya a kan gwadabenta na nasara da ta ke kai.

Buhari ya kuma buga misali da jam’iyar adawa ta PDP, inda ya ce duk karfin ta a ƙasar nan amma yanzu ta yi ƙasa.

A sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce APC ta kwashe kusan shekaru 8 tana mamaye sauran jam’iyyu sabo da ta buɗe kofar ta ga duk wanda yanke so ya shigo da ga wata jam’iya, babba ko karama.

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button