Labarai

Yadda Matar Abba Kyari Ta Sume A Kotu

Matar shahararren dan sanda, DCP Abba Kyari, da ke fuskantar zargin fataucin hodar Iblis ta yanke jiki ta fadi a sume a kotu.

Matar tasa mai suna Ramatu Kyari, ta sume ne a yayin da aka sake gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a safiyar Litinin kan zargin fataucin hodar Iblis.

Ta sume ne jim kadan bayan alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya dage yanke hukunci kan bukatar da Abba Kyari da suaran mutane shida da ake zargin su tare suka gabatar na bayar da belinsu a gaban kotun.

Alkalin kotun ya sanar da haka ne bayan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da ke karar su ta nemi kotun ta yi watsi da bukatar, tana zargin idan aka ba da belin su, za su iya tserewa da Najeriya ko su ki halartar zaman kotu Aminiya ta rawaito.

Jami’an NDLEA na wucwea da mijin nata da sauran takwarorinsa daga kotun bayan zaman ne aka ga Ramatu ta yanke jiki ta fadi a kasa.

Nan take wasu daga cikin jami’ai da lauyoyin hukumar suka dauke ta ranga-ranga zuwa wani ofishi domin ba ta kulawa.

Wata daga cikin matan da suka zo kotun tare ta bayyana wa kafar yada labarai ta Channels cewa Ramatu na fama da cutar Asma.

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button