
Alkalin ya daure shi watanni 4 ne bayan ya amsa laifin sa na balle wani shago inda ya saci taliya da indomi, da kuma kudi.
Alkalin ya ba shi zabi akan ko dai ya biya N10,000 ga ko wanne cikin laifuka biyu da aka tuhume shi da su ko kuma ya kwashe watanni 4 a gidan yari Abuja.
A ranar Alhamis, babbar kotun shari’a ta Gwagwalada da ke Abuja ta yanke wa wani dalibi mai shekaru 19, Hillary Yunana, watanni 4 a gidan gyaran hali akan satar taliya da indomi daga wani shago.
An tuhumi matashin wanda mazaunin kauyen Bassa ne da ke kan titin jirgin sama a Abuja da laifin balle shago da kuma sata, Daily Trust ta rahoto.
Alkali Sani Umar ya yanke masa hukunci ne bayan ya amsa laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa sannan ya nemi rangwame.
Alkali Umar ya ba matashin zabi akan ko dai ya biya N10,000 ga ko wanne laifi da ya yi ko kuma ya yi zaman gidan yari na wata bibbiyu ga ko wanne cikin laifukan sa guda biyu.
A cewarsa, zai yi zaman gidan yarin ne dodar inda ya shawarce shi da kiyaye aikata makamancin wadannan laifukan nan gaba.
Matashin ya saci taliya guda 7, indomi 5 da kuma N10,000
Alkalin kamar yadda Vanguard ta bayana ya ce wannan hukuncin zai zama izina ga duk wadanda suke tunanin aikata makamancin hakan.
Tun farko lauyan mai kara, Abdullahi Tanko ya sanar da kotu yadda matashin ya balle sannan ya afka shagon Gift Ugochukwu a ranar 4 ga watan Maris.
Tanko ya ce saurayin ya saci taliya guda bakwai da kuma indomi guda biyar tare da kudi N10,000, gaba daya komai na N13,000. A
cewarsa, laifin ya saba da sashi na 346 da 287 na dokar Penal Code.
Daga Hausa Legit
[ad_2]