Ya Kamata A Fara Yi Wa Duk Mai Mace Daya Bulala Har Sai Ya Kara Aure’:; Bello Yabo

Babban malamin addinin musuluncin da ke Jihar Sakkwato, Sheikh Bello Yabo, ya yi kira ga gwamnatin da ta fito da dokar a wani bidiyonsa da a yanzu ya karade dandalan sada zumunta musamman a Facebook.
Malamin ya bayyana cewa ya taba karantawa cewar a wata kasa ana zane duk wanda ya kai wasu shekaru da mata daya har sai ya kara wata matar.
Hakan ce ta sanya malamin ya yi kira da Gwamnati da ta kirkiri wannan dokar a Najeriya ta zane duk wani mai mata daya har sai lokacin da ya kara aure.
Har ila yau, Malamin ya bayyana cikin raha cewa mene ne amfanin namiji ya auri mata guda, inda kuma a cikin raha ya yi kira ga ‘yan Najeriya a kan kada su sake zaben duk wani dan siyasa mai mata daya.
Sai dai wannan lamari ya jawo tafka muhawara a shafukan sada zumunta inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu a kan jawabin malamin, inda wasu take suka yi wa malamin raddi wasu kuma suka nuna goyon bayansu a kai.
Wasu kuma ba su mayarwa da malamin wani martani ba, sai dai sun yi kira ga gwamnatin akan cewa bayan sanya dokar kuma ta kirkiri wata dokar ta bai wa su magidanta wani kudi na musamman domin cefanen yau da kullum.
Ga bidiyon maganan da malam yayi game da kara mata
[ad_2]