KannywoodLabarai

Ku daina haihuwar ‘ya’yan da ba za ku iya kula da su ba Nafisa Abdullahi

Fitacciyar tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta yi kira ga masu haihuwar ‘ya’ya ba tare da kula da su ba da su guji yin haka.

Ta bayyana haka ne a wasu sakonni da ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Asabar BbcHausa ta rawaito.

“Ku daina haihuwar ‘ya’yan da kuka san ba ku da halin kula da su,” in ji Nafisa.

Ta kara da cewa Allah zai tuhumi mutanen da suke haifar ‘ya’ya ba tare da sauke nauyin da ya dora musu ba.

A cewarta: “Kun ga dukkan mutanen da ke haifar ‘ya’yan da ba su ji ba ba su gani ba, domin kawai su aika da su almajiranci, kuma su ci gaba da haifar karin ‘ya’ya, Allah sai ya saka wa yaran nan!!!”

Ta bayyana matukar bacin ranta kan yadda wasu iyaye suke tura ‘ya’yansu ‘yan shekara biyu zuwa uku almajirci.

Tauraruwar ba ta ambaci sunayen wadanda take yi wa wannan gargadi ba, sai dai dama ba sabon abu ba ne yadda a kasar Hausa ake tura kananan yara almajirci.

Wannan lamari ya dade yana bata wa mutane da dama rai, musamman ganin cewa wasu na zargi ana amfani da irin wadannan yara wajen aikata laifuka.

Martani

Sai dai kalaman tauraruwar sun jawo martani daban-daban inda wasu suke yaba mata yayin da wasu suke sukar ta.

Da yake tsokaci, M.M Dambatta, ya jinjina wa tauraruwar sannan ya ce “har yanzu na kasa fahimtar yadda uba zai aika dansa dan shekara biyar domin ya kula da kansa da sunan almajirci. Ya kamata a tsayar da wannan lamari.”

Shi ma IAOgundele ya ce haihuwa barkatai ba tare da lura da ‘ya’ya ba ita ce sanadin matsalolin rashin tsaro da ke addabar Najeriya yana mai cewa “albarkatun da ake da su sun gaza ciyar da yawan mutanen da ake haifa.”

Sai dai Murtala Ubale ya tambayi tauraruwar cewa “wacce gudunmawa za ki bayar dan a daƙile cigaban hakan?”

Shi kuwa Autan Gwaggo cewa ya yi “kina kwance a kan gadonki, kina wani cewa Allah sai ya saka ma yaran nan.”

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button