Ƙasurgumin malamin da ke yiwa ƴan bindiga tsibbo a Zamfara ya shiga hannu


Malamin mai suna malam Adamu kuma limamin juma’a a garin Ajjah da ke cikin gundumar Wonaka ta ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara, ya shahara sosai wajen yiwa ƴan bindiga shirka suna yin yadda suke so a wannan yankin, ya kuma sha yin iƙirarin cewar muddun yana raye to babu yadda jami’an tsaro zasu samu nasarar shiga dajin domin yaƙar ƴan ta’adda.
Kama wannan malamin ya biyo bayan kama wata mata da aka yi ɗauke da sassan jikin bil’adama a garin Ruwan Ɓore tana ƙoƙarin yin tsaffi a yankin, wanda bayan kama ta ne ta tabbatar da cewar shine ya turota da waɗannan abubuwan, haka zalika wata majiya ta tabbatar da cewar malamin ne ya kitsa yadda aka hallaka kwamandan ƴan sa kai a wannan yankin da ake kira (Ɗan Mudi)
A yanzu dai ana cigaba da tatsar bayanai daga bakin malamin, kafin daga bisani a gurfanar da shi domin fuskantar hukunci kan laifin da ya aikata.
[ad_2]