Labarai

Akan dubu 6 matasa sun kulle mahaifinsu a ofishin Ƴan sanda a garin lere kaduna

Daga Aliyu Ishaq Saminaka

Wasu Matasa biyu sun kulle mahaifin su a ofishin ƴan sanda akan Naira dubu shida da suke zargin ya cinye musu, kamar yadda majiyar Alfijir Hausa ke samun wannan gibdadden labarin.

A jiya Alhamis wani lamari ya faru me kama da wasan kwaikwayo, a garin Unguwan bawa Saminaka ƙaramar hukumar Lere ta jihar Kaduna. Inda a samu wasu matasa yaya da ƙanin shi su kai mahaifin su ƙara ofishin JTF. A lokacin da hukumar JTF su zo a karanta musu waye ake son su kama su tuhume shi, sai su nuna baza su iya yin case ɗin ba sai dai zasu iya yi musu jagora zuwa ofishin ƴan sanda (Police station).

Matasan duk da hukumar JTF sun nuna baza su iya yin komai ba akan case ɗin ba, hakan bai sare musu gwuiwa ba! Su nausa ofishin ƴan sanda. Zuwan ƴan sanda ke da wuya su tasa ƙeyar mahaifin matasan zuwa caji ofis domin amsa tambayoyin.

Bayan anyi belin mahaifin yaran ya shaida mana cewa akwai kuɗin yaran dasu bashi dubu shida, da nufin zasu yi noma, sai zo daga baya akan ya basu dubu uku daga ciki da nufin shine suke son ya cika musu dubu ukun. Sai ya nuna shi bazai bayar ba daga nan ne sai su fara tunanin ko dai ya cinye musu kuɗin su ne. Daga ƙarshe kawai sai su yanke kai ƙarar mahaifin nasu shine kawai maslahar da kuɗaɗen su zasu fita cikin sauƙi.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button