Labarai

Zamu Tsara Yadda Zamu Fitar Da Ma Taimakin Shugaban Kasa Jam’iyyar Pdp

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar batun wanda zai zama abokin takara wato mataimaki ga Alhaji Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa da PDP ta tsayar a zaben 2023, ya ɗauki sabon salo.

Jam’iyyar PDP tare da haɗin guiwar ɗan takaran sun shirya wasu matakai da zasu taimaka wajen zakulo abokin takara wanda masoyan PDP da ‘yan Najeriya zasu karɓe shi hannu biyu.

Majiyar ta kara da cewa kwamitin gudanarwa na PDP na ƙasa karkashin shugaba, Dakta Iyorchia Ayu, da kwamitin amintattu karkashin Sanata Walid Jibrin suna kokarin cusa mutane daban-daban.

Shugaban Amintattu Sanata Walid Jibrin, a wata sanarwa ya ce kwamitinsa a shirye yake ya taimakawa wa ɗan takara wajen zakulo amintaccen mataimaki daga yankin kudancin Najeriya.

“Kwamitin mu zai taimaka wa Jam’iyya da kuma wazirin Adamawa shi kansa domin zaƙulo amintaccen mataimakin shugaban ƙasa daga yankin kudancin Najeriya.”

Kwamitin Amintattu (BOT) ya yi hannun riga da kwamitin gudanarwa (NWC ) Amma majiyar ta ƙara da cewa taimakon da BOT ya shirya bada wa zai iya yin hannun riga da tsarin kwamitin gudanarwa NWC wanɗanda ke kokarin jan ragamar ɗauko wanda zai takara da Atiku a 2023.

Gwamna Wike na jahar Ribas shi ne ya zo na biyu a bayan Atiku Abubakar da kuri’u 237 kuma yana daga cikin mutanen da ake hasashen ba mukamin.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button