JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 24

Washegari da safe Abuturrab ya sauko downstairs wajajen karfe takwas, jin motsi a kitchen ya fasa shiga kitchen din ya xauna parlor, bayan kusan minti ashirin Jiddah ta fito, tana ganinsa ta yi kasa da kanta kamar munafuka, ta nufi jikin kujera ta durkusa, a hankali tace “Ina kwana?” hararanta yake, taki yarda ta hada ido da shi ta mike tayi wucewarta sama, sae a sannan ya tashi ya wuce kitchen din, wanke wanke ya ga tayi ta goge ko ina na kitchen din, fridge ya bude ya dau apple uku ya dau karamin plate ya daura a kai sannan ya fita ya koma ya xauna yana cin apple din yana danna wayar sa, danna bell aka yi, ya kalli kofar da mamaki, can ya mike ya nufi kofar ya bude, ido hudu yayi da Aunty a tsaye ta hade girar sama da ta kasa, gabansa ya fadi sosai, ya kalli El-Basheer da ya xauna saman kujeran dake balcony din ya daura kafa daya kan daya, bangajesa Aunty tayi ta shiga parlon, ya bi ta da ido sannan ya kalli El-Basheer fuska daure, mikewa El-Basheer yyi yace “She only said in rakata anguwa, and i never knew nan xata xo” Wani kallo Abuturrab yyi masa ya juya ya koma cikin parlon, tsaye ya tadda Aunty fuskar nan nata babu alamar wasa, yyi kasa da kai da ladabi yace “Ina kwana Aunty?” tace “Ban kwana ba Aliyu, ina yarinyar take?” Yyi kasa da murya yace “Aunty dama ai anjima kika ce in kai ta can gidan ko” Cikin tsawa tace “Ta fito yanxu mu wuce, na hutassheka ba sai ka kai ta ba” a hankali yace “Toh” Daga haka ya fara wucewa sama, ta bi sa da harara tana girgixa kafa, sai da ya haura sama ya d’an juyo ya kalleta ganin bata ganinsa, ya nufi dakin Jiddah da sauri, Tana gyaran gado ya shigo, ta mike tana kallonsa, ya hade rai yace “Mu je” Tana kallonsa tace “Ina?” Fixgo hannunta yyi ta xaro ido tana kallonsa har suka fita dakin, ganin bangarensa ya nufa taki ci gaba da tafiyar tace “Me xanyi…” wani kallo ya jefa mata, hakan yasa ta ci gaba da tafiyar, parlonsa ya kai ta, ya bude kofar balcony yana kallonta yace “Shiga” da mamaki tace “Saboda me” shigar da ita balcony din yyi yana kallonta da kyau yace “Idan kuma so kike Auntyna ta tafi dake sai ki 6ara baki kiyi kuka har ta ji ki” Daga haka ya kulle kofar, ya sa makullin a aljihunsa, ya fita parlon a stairs ya hadu da Aunty, tace “Ta kasa sakkowa ne har yanxu xaka shanya ni a parlor” With confusion yace “Aunty I don’t know, na duba dakin da take ban ganta ba, amma jiya Maimoon ta xo, ban san ko….” Wani tsawa tayi masa tace “Ni xaka raina ma wayo Aliyu?? Xuwa kayi ka boyeta?” Ya marairaice yace “Boyeta kuma Aunty, a ina xan boyeta ki shiga duk inda xaki shiga ki duba, ni fa jiya sai kusan sha biyu na dawo gidan nan, i don’t know ko sun tafi tare da Maimoon, and tunda gari ya waye ban fito ba sai ynxu da ku ka xo” Bangajesa tayi ta nufi saman, dakin Jiddah ta fara budewa, hankalinta yyi mugun tashi ganin dakin kamar na amarya ga gaban mirror taff da kaya masu tsada, ta bude press, nan ma taga uban kaya, shi dai yana tsaye yana kallonta, ta juya tana kallonsa… Da sauri yace “Ko biyar dina babu a nan Aunty, Umma ce da Abba da uncles dina duk suka yi wannan siyayyan, ki tambayi Ummi ma” har bathroom sai da ta bude bata ga Jiddah ba, Juyawa tayi ta fita ta shiga sauran dakunan nan ma bata ga alamarta ba, fita tayi ta tafi bangarensa, iya dubanta bata ga Jiddah ba, kofar Balcony din ta murda, Abuturrab dake tsaye bakin kofa duk yana kallonta, yyi kasa da murya yace “I can’t find the key to that place, balcony ne ai kin sani” Da ido ya bi ta har ta fita parlonsa, snn ya bi bayanta, Jiddah dai na tsaye balcony din, lkci lkci take satan kallon mutumin dake xaune a daya building din, da ta saci kallonsa kuma sai su hada ido, daga karshe ta canxa position dinta, sai bayan minti talatin Aunty ta bar gidan bayan ta ta66atar da gaske Jiddah bata nan, don ta duba ko ina, Ba tare ta koma da El-Basheer ba bayan ta amshi makullin mota tayi wucewarta, Ko kallon El-Basheer Abuturrab bai yi ba ya shige parlor, mikewa El-Basheer yyi ya bi bayansa, Abuturrab ya xauna saman kujera, El-Basheer ya xauna yana facing dinsa yace “Now tell me d truth, Ina yarinyar take?” Abuturrab yace “You encouraged Aunty to my house right?” El-Basheer yace “Not at all, bata ma ce min nan xata xo ba, sannan me yasa baxa ka bari ta koma gidan naku ba tunda ba matarka bace, or ka kaita bauchi” Abuturrab yace “Ohkk, saboda duk banyi niyya ba” El-Basheer ya shafa kansa sannan ya mike yace “Ohk then, anjima xan koma Bauchi in sha Allah” Abuturrab yace “Allah ya tsare” Kofa El-Basheer ya nufa, Abuturrab ya bi sa da kallon gefen ido har ya fita sannan ya tashi ya kulle kofar parlon da makulli ya wuce sama xuwa part dinsa, ya ciro makullin a aljihunsa ya bude kofar, daga kai tayi suka hada ido, ganin taki motsawa yace “Baxa ki fito ba” bata ce komai ba ta bi ta gefensa ta shigo parlon ya kulle kofar…..

Karfe biyu saura Jiddah ta sauko parlor sbda yunwan da taji take ji, tun bayan tafiyar su Aunty Abuturrab ya sa ma gidan makulli ya koma parlon bangarensa, wayarsa dake saman center table ne ta ji yana vibrate, kallon wayar ta dinga yi sannan ta karasa ta duka ta dauka tana kallon screen din, Cikin few seconds tayi kokarin hade rubutun screen din wayar, “Blossom” katsewa kiran yyi aka sake kira, kamar ance ta juya suka yi ido hudu da shi a tsaye ya rungume hannu yana kallonta, daburcewa tayi xata mayar da wayar ta ajiye masa nan bakin center table din ya fado kasa, ta mike a tsorace tace “Dama kiran ka ake” karasowa yyi ya dau wayar fuskarsa daure yana duba screen din, juyawa tayi da sauri xata bar wajen yace “Tsaya nan…” Tsayawa tayi amma ta ki kallonsa, Sternly yace “Baki da hankali ne?? Ba na hanaki ma shigowa parlon nan idan ina nan ba? Ko don kinga ina kyale ki??” Tayi narai narai da ido tace “Kitchen xanje sai naji wayar na kara” Tsawa yayi mata yace “Ina ruwanki da wayar? Ko ke kika ajiye min a nan?” Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, on a serious note without bothering ko ta gane turancin nasa ko bata gane ba yace “Naga kina neman fara wuce boundaries din ki a gidan nan, to bari kiji, daga yau, i mean daga yanxu da kike tsaye nan kada ki sake shigo min parlor idan ina gidan nan, idan kin tashi da asuba kafin in fito da safe dama ki girka duk abinda xaki girka na safe da rana ki kai dakin ki, karfe biyar na yamma ina sama, sai kiyi amfani da wannan opportunity din ki sakko ki dafa abinda xa ki ci da daddare, kafin shidda ki tabbatar kina dakin ki…. Am i clear?” Ita dai kanta na kasa, ya mata wani tsawa yace “Baki ji na ne?” Ta dago kanta hawaye cike idonta tace “Toh” Yace “Get out.. Tafi ki ban waje” Juyawa tayi a hankali ta wuce sama, ya xauna yana sake kallon wayar tasa da screen ya tsage. Abuturrab bai yi mamakim k’in daga kiransa da El-Basheer yyi ba, don ya kirasa ya fi sau biyu yaki dauka, Da yammacin ranan Abuturrab na operating laptop dinsa a parlor aka danna bell, wani faduwa gabansa yyi ya mike yana kallon kofar, bayan few seconds ya isa kofar yace “Who is there?” Muryar Umma yaji tace “Ni ce” Ya d’an buda ido da mamaki sai kuma ya bude kofar, lkci daya kuma yyi pretending as if he wasn’t even surprise yana murmushi ya bata hanya, yana shafa kansa yace “Welcome Umma, sannu da xuwa” Ta shigo parlon tace “Unexpected visit… Ban ce xan xo ba ko?” Yace “Ai ba sai kin ce min ba Umma, ya hanya?” Ta xauna saman kujera tace “Alhmdlh, ina jiddar?” Ya d’an kalli sama sannan yace “Tana sama” daga haka ya wuce sama, calmly ya bude kofar dakinta, xaune ya ganta can karshen gado ta takure waje daya, tana ganinsa ta sauke kafarta ba tare da ta yarda ta sake kallonsa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja yyi, kana ganinta kasan kuka tayi sosai, ya hade rai yace “Wani abu aka maki da kika xauna kike kuka?” Ta girgixa masa kai kawai, ya dinga mata wani kallo kafin yace “Tashi ki wuce bandaki ki wanke fuskarki ynxu” sauka tayi daga kan gadon ta shiga bathroom tayi yanda yace, yana tsaye dakin har ta fito yace “Dauka Hijab din ki” Ba musu ta dau hijab din ta saka, yana son mata warning ko da umma xata yi mata wani tambaya ta bata positive answers but ya fasa sanin cewar baxa ma ta ce da umman komai ba, kofa ya nuna mata alamar ta fita, ta fita dakin ya bi bayanta, wuce ta yayi, ya riga ta sauka downstairs, Yana kallon Umma da murmushi fuskarsa bayan Jiddah ta sakko parlon yace “Daxu take kuka umma wai in kai ta wajen ki, but yau xa mu wuce kano and ina wani aikin shi yasa ban kai ta ba” Umma dai bata ce masa komai ba sai kallon Jiddah da ta nufo ta tana murmushi a sanyaye tayi, dukawa tayi kusa da ita a hankali tace “Umma sannu da xuwa” Umma na kallonta tace “Me ya sami idonki?” Abuturrab yace “Kuka tayi, wai in kai ta can gida wajen ku, nace ba yau ba” Still Umma bata kallesa ba, Jiddah dai kanta na kasa tana wasa da fingers dinta,

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button