BAKAR INUWA 44

Chapter 44
44
……….Su dukansu fuskokinsu washe suke da fara’a da farin ciki. Gasashshen naman rago ne a banƙare a tsakiyarsu. Sai lemuka masu tsada da daɗi ajiye
gaban kowa. Gaba ɗayansu hankulansu nakan tv da ake nuna abinda ke faruwa a ƙauyen Kauci na ƙaramar hukuma Gaman. Cikin ƙyalƙyalewa da dariya Mr MM ya kai
tsokar nama daya cako da pork spoon bakinsa yana faɗin, “Wato ranka ya daɗe dabarar nan taka tayi ɗari bisa ɗari, yaje ya dawo yana farin cikin samun na
sarori sai yaci karo da ƙyaƙyƙyawar tarba ta musamman”.
Kwashewa sukai da dariya baki ɗayansu, Alhaji Haladu Gwandu dake dariya harda hawaye ya ce, “A to ba gani yake shi yanada dabarar shinfiɗa aiki ba ta
hanyar ɗaura ƴan uwansa matasa kan manyan muƙamai, to sai yayi aikin mugani. Basai da zaman lafiya a ƙasar talakan zai ga aikin ba?”.
Wata dariyar suka sake kwashewa da ita. Sai dai banda oga kwata-kwata da yake murmushi kawai yana cin namansa shima. A cikin God fathers ɗin nasu ɗaya ya
tsaida dariyarsa ya ajiye wuƙar daya yanko wani ƙaton nama ya ɗauka da hannu yakai baki. “Ai indai mune baima ga komai ba. Sai mutuwar fitinannen tsohon
kakan can nasa ta tabbata nan da kwanaki uku, a kuma ranar plan B zai bayyana shima, yanda mutuwar Alhaji Hameed Taura bazatayi tasiri a zukatan mutane ba
balle ya samu addu’a da nuna tausayawa”.
Dariyar suka sake tuntsirewa da shi. Forma president ya ce, “Wa yaga gaba kura baya sayaƙi. Bashi gani yake mulkin wasan yara bane ba, zai yabawa aya
zaƙinta. Yanzu nan fa ina shirin fitowa ma nakejin wani ƙishin-kishin ɗin gulma, wai da yayi niyyar bincike akan kwangilolin da muka bada, sai dai ya
dakatar dalilin wani abu da ba’asan tabbaci ba………”
Vice president Alhaji Yaro glass ya karɓe zancen forma president da faɗin, “Wannan maganar kam tabbas ce, sai dai nima ina kan bincike miye dalilin
hanashi fasa binciken. Dan yanzu haka ma gobe za’a zauna da masu kwangilan meeting tare da J.P.S”.
“What!! Alhaji Haladu Gwandu (Mahaifin Amnah) Ya faɗa aɗan razane. Dan kuwa akwai yaronsa a cikin wanda aka bama kwangilolin, kuma tabbas yau kusan
kwanaki uku yana kiransa bai samu damar ɗaga wayar tasa ba saboda busy da yayi…..
“Wlhy da gaske haka zancen yake”.
Alhaji yaro glass ya faɗa a yanayin takaici da jin ɗaci. Waya Alhaji Haladu Gwandu ya lalubo a aljihun babbar rigarsa. Da sauri ya shiga laluben lambar
yaron nasa. cikin sa’a kuwa bugu ɗaya ya ɗauka tamkar dama kiran nashi yake jira. Ko sauraren gaisuwar tasa baiyiba ya jeho masa tambaya. Sai dai amsar daya
bashi tai matuƙar firgitashi ya saki baki da hanci yana saurare har yaron nasa ya gama bayanin saƙon da suka samu na kira da ga ofishin Minister.
A hargitse ya ajiye wayar bayan sun kammala yana faɗin, “To tunda ya fasa binciken kiran ubanmi yasa Minister ɗin yake musu?”.
“To wa ya sani”.
Cewar Alhaji Yaro glass.
A harzuƙe Forma President ya ce, “Amma ya kamata ace irin waɗan nan abubuwan kana ƙoƙari saninsu Alhaji Yaro. Kasan kuwa wanene Ramadhan da Alhaji Hameed
Taura?!!…”
“Haba Alhaji Usama ya zakaga laifina? Bayan kaima kasan yaron nan komai yinsa yake a ƙudundune, daga shi sai matsiyacin cos ɗin nan da nafi tsana fiye
da komai yanzu a duniya. Sai ko shegen kakansa ɗin nan da ubansa da nasan sune masu bashi shawara sama da mashawartansa na mulki…..”
Mr MM zaiyo magana Oga kwata-kwata ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masu hannu. “Inaga wannan cece kucen ba shine mafita ba. Amma tabbas Alhaji Yaro
akwai sakacinka anan. Sai dai muma munada laifi da bamu ɗoraka bisa hanyar data dace ka dinga sanin komai da komai ba. Amma ka sani matarka tana ɗaya daga
ciki, dolene ta cigaba da kawo mana mike gudana a cikin gidan gwamnati ta hanyar matarsa tunda ƴa take a wajenta. Sauran magana kuma zamuyi daga baya idan
na kammala nazari, amma a dakatar da kashe Alhaji Hameed Taura ba yanzu ba”.
Cikin gamsuwa duk suka ɗaga masa kawuna, duk da a ransu suna son sanin dalilin dakatar da kashe Bappin, sai dai babu damar yin jayayya……..
__________________
A matuƙar ruɗe Raudha ta kai hannu tana riƙo na Ramadhan jikinta na rawa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, nasan wanda suka rasa ransu bazasu taɓa dawowa ba.
Sai dai akwai mafita da zata taimaka a taimaki wanda sukaji raunika da tsananta tsaro ga wanda ba’a cutarba”.
Duk da bai ɗago ya kalleta ba yanda ya dakata da yamutsa kan ya tabbatar mata yana saurarenta. Sai kuma ya ɗago ɗin ya zuba mata idanunsa. Hawayenta
tai saurin sharewa tana miƙo masa wayarsa data ɗakko. Sai kuma takai ɗayan hanunta ta share masa nasa hawayen shima da har yanzu suke sakkowa.
“Kasan yanayin ƙasarmu da ƙarancin kulawar da talaka yake samu akan harkar lafiya da tsaro. Lokuta da dama wasu a cikin jami’ai najin abu na faruwa sai
dai tsoro da rashin kayan aiki na daƙilesu akai taimako, wasu kuma son zuciya ke hanasu yin kowane irin yunƙuri. To kamar hakane ga jami’an lafiya suma.
Shiyyasa idan sakacin shugabanni ya haɗu da masu raunin taimako a jami’an lafiya ma yana ɗaiɗaita rayuwar talaka. Mafita itace yanzu ba wakili zaka saka ya
bincika ba ko ya bama C.P na jihar umarni, kai da kanka ne ya kamata kai magana da I.G da C.P ɗin zasufi jin tsoron tashi suyi abinda ya kamata suma bawai
su tura yara ba. Hakama asibitin da kanka ka kira Commissioner lafiya na jihar kai magana da shi dan ALLAH Ya Ramadhan……”
Ɗari bisa ɗari ya gamsu da maganarta, dan haka ya ɗago da sauri, wayar da take miƙa masa ya amsa yay dailing number cos. Kai tsaye yace, “Ka sameni”.
“Ranka ya daɗe yanzu haka ina cikin gidan nan ai”.
Cos ya faɗa da sauri gudun kar shugaban ƙasa Ramadhan ya yanke wayar. Duk da cos baya shigowa har nan yau dai ya bashi umarnin ya samesa. Cikin ƙanƙanin
lokaci kuwa sai ga cos ɗin. Saurin janye jiki Raudha tai daga rungumar da Ramadhan ya sake mata bayan yayi magana da cos. Sai dai hanunta ya riƙo cikin nasa
dole ta zauna a hanun kujerar da yake a zaune hanun nata rumtse a nasa.
COS ya rissina yana gaishe da Raudha data amsa a kunyace, dan yanda ya gansu da yanda yake bata girma har mamaki takeyi.
Cikin bada umarni Ramadhan yace, “Ina bukatar magana da I.G & commissioner of police na jihar, tare da commissioner lafiya”.
Kai Cos ya jinjina yana mai fara danna wayarsa. A taƙaice Cos yayma I.G bayani ya mikama Shugaban ƙasa Ramadhan wayar. Koda ya amsa bai wani tsaya
sauraren gaisuwar ɗin ba da jikinsa keta ɓari da ga can shi zaiyi waya da shugaban ƙasa. Kamar yanda Raudha ta bashi shawara haka yayi, yana gama kora masa
bayani cike da ƙasaita kamar bashi ya nema birkicewa ba yanzu ya miƙama COS wayar. Amsa yay da girmamawa ya sake kira masa C.P na jihar Kuddo da
Commissioner ɗin lafiya. Daga ƙarshe yasa aka kira Gwamna ɗin jihar shima inda Shugaban ƙasa Ramadhan ya balbalesa da masifa jin tamkar ma shi babu wata