DIYAM 11
DIYAM
By
Maman Maama
Episode Eleven: Family
Daga asibiti gida suka taho gaba-daya. Suna zuwa Alhaji babba da kawu Mamman suka zo, Kawu Mamman yace “zamu tafi da Amina can gidan
Alhaji Babba ta zauna tayi wanka a can” Alhaji babba ya kara da cewa “zata zauna a can sai yarinya tayi kwari, daga nan asamu a basu magungunan mayu da kambun baka saboda rigakafi” Baffa dai bai ce komai ba, Ummah kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayenta dan gudun kar Baffa ya gani ransa ya kara baci.
Daga zuwa wanka sai da nayi wata hudu a duniya kafin mu dawo gida. Inna ta gaya min cewa a cikin watanni hudun nan duk juma’a sai Baffa ya saka Ummah ta shirya ita da Sadauki sun taho dan su ganni amma ko da sau daya ba’a taba barinsu sun wuce ko da gate din gidan ba. Kuma ko sau daya bata taba gaya wa Baffa cewa ba a barinsu su shiga ba. Sai ranar nan ya dawo daga garage dinsa ya samu Sadauki yana ta kuka shi wajen kanwarsa zaije sai Baffa ya tambaye shi “ba jiya kaje ka ganta ba?” Sadauki ya girgiza kai yace “ai ba’a barmu mun shiga ba, kullum in munje koro mu ake yi ace Alhaji Babba yace kar a barmu mu shiga” to jin haka ne fa sai Baffa ya tafi gidan Alhaji Babba ya samu uwargidansa Hajiya Babba yace “wannan idan auren kuke da niyyar rabawa sai ku fada min in aiko mata takardarta, idan kuma kuna son acigaba da auren to lallai a mayar min da iyalina gidana” jin haka yasa Inna babu shiri ta fara harhada mana kayan mu dan tasan halin Baffa.
Yadda tsarin gidan mu yake shine, ta garage ake shigowa daga nan sai dan karamin fili mai bishiyar umbrella da flowers a sides, sai bandaki a gurin. Daga nan zaka shiga karamar kofa zuwa tsakar gida. A tsakar gida kana shiga kofar palon Inna ne a farko, babbab palo ne da dakuna guda biyu suna facing juna. Dakin Baffa kofar sa tana kallon palon Inna, an yi stairs a kofar dakin Baffa da niyyar yin dakuna a saman dakunan sa, amma kuma ba’a samu damar karasawa ba. Dakunan umma kuma suna daga can ciki saboda daga baya aka sayi fili akayi su aka shigo dasu, suma kuma exactly tsarin na Inna ne. Sai kitchen da toilet a tsakar gida.
Ina so ka fahimci wani abu guda daya. Allah ya dorawa Ummah sona kamar yadda take son mahaifina, soyayya ta gaskiya marar algus a ciki. Tun da muka koma gida sai ya zamana koda yaushe ina gurinta, in dai har Inna zata ajiyeni to kuwa Ummah zata daukeni in ina hannun Inna ne dai ba zata iya cewa ta bata ni ba. Wannan yasa sau da yawa Inna ko aiki zatayi sai ta goya ni tace “bazan ajiyeki ba kar waccan mayyar ta dauka”. Hausawa su kance mai da wawa, amma wannan baiyi aiki akan Inna ba, ita idonta ya rufe akan kishin Zainabu.
Sadauki har dakin Inna yake biyo ni, Inna ta kore shi amma yaki tafiya in ta hankada shi sai ya zauna a bakin kofa yayi ta kuka shi a bashi Diyam dinsa. Ni kuma tunsanda na fara gane mutane babu wanda nake murnar ganinsa irin Sadauki. Dana fara rarrafe kuwa daga na tashi zan tsallake Inna tana bacci in tafi dakin Ummah ita kuma ta dauke ni ta bani abinci tayi min wanka da kwalliya ta gyara min dogon gashina ta goya ni, Ummah har kaya tasiya min ta ajiye a dakinta saboda in tayi min wanka ta saka min tunda Inna ba zata bata ba. Ummah macece mai tsafta sosai da kwalliya.
Lokacin dana fara magana kalmar dana fara iyawa itace “Sadauki”, sadauki ya bani labarin cewa ban ma iya fadi sosai ba dan “sholoki” nake cewa, shi kuma sai ya sakani a gaba yayi da dora min kamar karatu, “ki ce Sadauki” ni kuma sai ince “Sholoki” a haka a haka har na iya, ranar dana fadi sunansa dai dai yaje ya dauko bankinsa da yake taron kudi a kasan gadon Ummah ya fasa ya tafi bakin asibitin Murtala ya sayo min yar tsanar roba ya kawo min a matsayin gift. Na karba ina murna, yace “to wanne suna zaki saka mata?” Nace “Shubeya” (Subay’a) sunan wata jaririya da aka haifa a makotanmu a lokacin. Tun daga ranar kullum ina rike da shubeya ta, hatta bacci tare da ita nake yi har nayi wayo.
Akwai ranar da bazan manta ba duk da kankantata. Ina wasa da Shubeya a tsakar gida Ummah kuma tana wanki Inna tana kitchen tana girki. Wata yarinyar makota ta shigo tace min “Diyam wai babyn waye wannan?” Ta nuna Shubeya, nace “yata ce, yata ce ni da mijina Sadauki”. Ai kuwa sai ga Inna da saurinta ta fito daga kitchen tace min “me kika ce Diyam?” Na sake maimaita mata tunda ni a lokacin bansan ma ma’anar kalmar miji ba, nan take inna ta ciro bulala a bishiyar tsakar gidan mu ta daga skirt dina ta ringa tsula min a kafafuwana ina ihu tana cewa “zaki kara cewa Sadauki mijinki?” Ummah ta ajiye wankin hannunta ta rugo da gudu takwace ni daga hannun Inna ta shige dani dakinta ta rufe kofa. Inna ta ringa bugun kofar amma taki budewa sai ma dauka na da tayi ta kaini toilet ta wanke min kafafuna da suka tashi suka yi rudu rudu, ta shafa min vaseline ta kwantar dani akan gadonta tare da Shubeya ta.
A waje kuma bayan Inna ta gaji da bugun kofa sai ta dauki waya ta kira gidan Alhaji Babba cewa ga Ummah nan ta dauke ni ta shige dani daki ta rufe kofa ita bata san me take yi min ba. Nan da nan sai ga gwoggona da nake cewa Aunty Fatima wadda akayi dace taje gidan a lokacin, da Adda Zubaida babbar ‘yar Alhaji babba wadda a lokacin take zawarci, da wadansu da suke yammata a lokacin suka zo gidan mu suka yi ta bugun kofar Ummah, ai kuwa tana budewa suka rufe ta da duka Inna kuma ta shige ciki ta dauko ni tana duba lafiya ta, a lokacin Baffa ya shigo rike da hannun Sadauki daya dauko daga makaranta, yana shigowa yaga abinda ya faru ya nemi ba’asi kowa ya bashi side din story dinsa, a take zuciya ta ciyo shi ya rubuta wa Inna takarda saki daya, ya kuma karbe ni daga hannun ta ya mika wa Ummah ni.
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da har yau Inna ta kasa mantawa a rayuwar gidan mu. A lokacin sai da Hardo da kansa yazo har kano ya sasanta maganar sannan Baffa ya mayar da ita amma da sharadin kar wanda ya kuma daga hannu ya dakar masa mata. Bayan wannan Inna ta rage tsangwamar Ummah sosai sai dai ba za’a taba kiran zamansu da zaman lafiya ba.
Shekara ta biyar a duniya Inna ta haifi kanwata, Asma’u, tun daga nan kuma shikenan babu wata haihuwar. Sadauki bashi da kokari a makaranta, dan yana daga yan karshe karshe a position a ajinsu, amma kuma Allah ya bashi fasaha a kan kere-ƙere. Wannan yasa kullum daga ya dawo daga school zai shirya yabi Baffa zuwa gareji, kafin wani lokaci Sadauki yasan kan mota sosai dan zai iya kunce inji ya mayar ya hada, duk minor gyaran da aka kawo wa Baffa sadauki ne yake yi kuma ya gyaru sosai. Ina iya tuna lokacin da Baffa yake cewa “Sadauki da ace ni mai kudi ne da kasar waje zan kaika kayi karatu, tunda karatun kasarmu duk theory ne kai kuma kafi gane practical”.
Ranar nan ya dawo daga makaranta na tafi da guduna na rungume shi ina masa oyoyo, ya ciro alawar da ya siyo min da kudin taran sa, wadda yasan in dai ya shigo babu ita to sai nayi masa rigima, na karba nace “Nagode Sadauki” ya kamo kunnena yace “daga yau hamma Sadauki suna na” na gyada kai ina murza kunnen da yaja, Ummah ta harare shi tace “sai son girma kamar gwambo, ga kuma mugunta” ni dai na wuce dakin Inna da sauri na kai mata sweet din nace ta bude min. Ta karba tana tambayata “waye ya baki?” Nace “hamma Sadauki ne” ta kamo kunnena da sauri tana daga muryarta yadda Ummah zata ji daga waje tace “hamma wa? A gidan uban wa ya zama hammanki? Babu hadin danga da garafuni kar in kara jin kince masa hamma” na saka kuka saboda zafin da kunnen yake min nace “na daina Inna” ta sake ni na fita da gudu gurin Ummah ina share hawaye na, ta dauke ni ta dora akan cinyarta ta bude min alawar tana rarrashina. Daga ranar ban kuma cewa Sadauki hamma ba shima kuma bai kuma cewa in gaya masa ba
Shekarar da aka saka ni primary Sadauki ya shiga secondary, dan haka a lokacin Baffa ya siya masa keke yake zuwa akai. Ni kuma Baffa ne da kansa yake kaini a motarsa tunda makarantar mu babu nisa kafin ya fita amma ranar nan sai na saka rigima nace ni a keken Sadauki zan ke tafiya, nan take Sadauki yace “Baffa ka barta, kaga hanya daya ne sai in ajiyeta in an taso kuma in biya in dauke ta” Inna tace “kaji mugunta, salon kake kayar da ita a hanya kullum? In banda mugunta ga motar ubanta sai ace ta hau keke? To ba zata hau din ba” na makale kafafa ina kakalo hawaye, Baffa ya tsaya yana kallon Inna saboda yaji zafin maganar ta amma saboda muna gurin sai kawai yace “bishi ku tafi, Allah ya kiyaye hanya” Ummah tace “ka bi a hankali, kar kaje kana wannan rawar kan naka ka jefa ta a kwata” ni kuwa sai tsalle da murna, ya dora ni a gaban sa ya saka na rike kan keken sannan ya taka keken muka tafi. Muna barin layin mu na saki kan keken na fara kokarin mikewa tsaye, ya rike ni da hannu daya yace “ki zauna Diyam, zaki fadi fa” na ture hannunsa “ka tsaya kaga abinda zamuyi, irin na titanic, nice rose kaine jack” na mike na bubbude hannayena, ai kuwa kafin yayi managa na zame zan fadi, garin rikeni shima ya biyo ni sai gamu a kasa a kan kwalta, guiwowina duk sun daddauje goshina ma haka. Na dage kuwa tun karfina na ringa zunduma ihu, yayi rarrashin duniyar nan naki inyi shiru, haka ya dauko ni da hannu daya ya jawo keken da daya hannun muka taho gida.
A bakin gate muka tarar da Baffa yana shirin fita. Yana ganin mu ya taho da saurin sa ya karbe ni a hannun Sadauki ya dora ni a saman mota yana duba ciwon da naji. Tun kafin Sadauki ya bada labarin abin da ya faru sai ga Inna ta jiyo kuka na ta fito da sauri tana cewa “ai dama sai da na fada, yaron nan babu komai a zuciyarsa sai zallah mugunta, gashi nan yaje ya jefar min da yarinyar ya cuce ni” Baffa ya juya kanta shima da nasa fadan sukayi tayi, basu san sanda Ummah ta fito ta dauke ni ta wankemin ciwon da naji ba ta chanza min kaya sai ji sukayi tace “baban Diyam ko zaka kaita chemist a duba ciwon sosai?” Baffa ya juyo yana kallonta yace “Allah yayi miki albarka Zainab” tayi murmushi tace “ameen, Nagode”. Sannan ta cewa Sadauki “kaima sai ka bisu a duba hannunka” sai a lokacin duk muka lura cewa shima yaji ciwo a hannunsa yana ta jini, yayi saurin nuna jarumta ta hanyar cewa “babu komai” amma Baffa ya tilasta masa sai da ya bimu.
Na jima da wannan tabon a goshina, duk wanda ya tambaye ni sai ince “Sadauki ne ya kayar dani a keke”.
Writing……