NOVELSUncategorized

DIYAM 12

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twelve: My Brother, My Friend.

“Diyam, ba zaki cigaba da cin abincin nan ba sai nazo ko?” Na daga kai ina kallon Inna da take zazzare min ido
cike da barazana. Na debi shinkafa a chokali na kai bakina ina taunata da kyar saboda koshin da cikina yayi ji nake kamar zanyi amai. Na shawabe fuska “Inna wallahi na koshi, nasha tea, naci bread, naci kwai, bazan iya cin shinkafa ba kuma amai zanyi” tace “kiyi aman, sai ki zo ki cigaba da ci” na kalli kofa da sauri saboda motsin mutum dana gani, ta gefen labule na hango Sadauki sanye da uniform dinsa, muna hada ido yayi min alamar in taho da hannunsa, na ture abincin na sunkuci jakata zan fita Inna ta fizgoni ta dangwarar akan kujera tace “in kika fita daga dakin nan sai na yanke kafafuwanki” ta harari kofa tace “bakin munafuki, babu inda zakuje tare” ta kara dangwara min kwanon shinkafa a cinyata.

Muryar Baffa na jiyo a tsakar gida “kai kai kai, Sadauki wai baku tafi ba har yanzu? Ai kun makara, ina Diyam din?” Nayi saurin ajiye kwanon amma hararar da Inna ta jeho min yasa na dauka na cigaba da rikewa. Baffa ya leko yace “ke Diyam, ki fito ku tafi mana kin makarar dashi zaki sa a dake shi” Inna tayi charaf tace “ya tafi kawai kar a hukunta shi a makarantar su. Diyam bata gama karyawa ba” na ajiye kwanon nace “na gama Baffa, tun dazu na gama Inna ce ta hanani fitowa” na zagaya ta gefenta na fice daga dakin da sauri na rungume sadauki shi kuma ya dauke ni ya dora akan kekensa muka tafi. 

Haka mukayi ta fama kullum ba fashi, kullum sai inna tayi ƙoƙarin hanani bin Sadauki ni kuma sai na nace na bishi. Shi zai kaini har class dinmu yaga na shiga sannan ya tafi tasa makarantar. A lokacin dana kara girma kuma sai ya daina dorani a keken sai dai mu tafi a kafa yana jan kekensa a hannu har sai ya kaini sannan shi kuma ya hau ya tafi tasa. Haka islamiyya ma tare za muje, in asma’u ta biyo ni sai in korata ince tabi yaran makotanmu. Sadauki shine yayana, shine abokina, shine kawata, shine abokin shawarata, duk da cewa a lokacin akwai yarinta sosai dan haka duk shawarar ta shirme ce, shima kuma tunda ba wani girmata yayi sosai ba haka zai bani amsar shiririta.

Duk kawayena, na boko dana islamiyya sun san Sadauki, wadda bata sanshi a fuska ba kuwa to tabbas tasan sunansa saboda da wahala in muna hira in iya hada sentence guda ba tare da sunan sadauki ya fito a ciki ba. Duk kuwa sanda wani a ajin mu ko ajin gaba damu yaci zalina ko na tsokani wani ya dake ni to tabbas sai jikinsa ya gaya masa in ya shiga hannun Sadauki, wannan yasa ake shayin tabani ko a yaran unguwa sai dai in na tsokani yaro yayi hakuri dan dole dan sun san cewa sadauki ƙashi daya ne dashi. 

Bashi da surutu sam, he is a good listener rather than a talker, ko a gida in dai kaji yana hira to dani ne, ko da Baffa, amma ko Ummah basu cika zama suyi doguwar hira ba. Yana da zuciya da fada in an taba shi ko an taba ni, amma ni din ko daga min murya baya iyayi balle yayi min fada. Kuma duk zuciyar Sadauki, bai taba daga kai ya kalli Inna in tana gayawa Ummah magana ba, sai dai ka gani a fuskarsa cewa ransa ya baci amma ba zai mayar mata ba. Yana da kazar kazar sosai kuma baya zama guri daya, in har baya makaranta to yana gareji in kuma baya can to yana gida yana aiyuka, zai share gidan mu tas ya gyara wa Baffa dakinsa ya wanke masa mota. Watarana nace masa “Sadauki kai baka gajiya ne? Ka kwanta ka huta mana” Sai yace “wa kika taba gani yayi achieving wani abu a kwance? In kana son wani abu you have to work hard to earn it”. 

Ranar nan, a lokacin ina primary 5, ina da shekaru goma da yan watanni sadauki kuma yana sha shida. Anti Hafsa, wadda muke kira da Mama tazo gidan mu, suna ta hira da Inna ni kuma ina kwance sun dauka bacci nake yi naji Mama tace “ni Addah kullum sai inga kamar kara ramewa kike yi, har yanzu kin ƙi ki kwantar da hankalinki kiyi ƙiba kema” Inna tace “hmmm Hafsa ina hankalina zai kwanta ne bayan wannan mayyar ta sakani a gaba, ita da wannan baƙin dan nata sun hana zuciyata hutawa sam” Mama tayi dariya tana riƙe baki tace “kai Addah, daga ni har ke fa mun sani cewa bafa mayyar bace da gaske, muna sane muke takewa kawai dan mu bata mata rai amma da mayyar ce da ba tini ta cinye ki ba ko ta cinye yayanki? musamman tunda ita bata haihu anan gidan ba?” Inna tace “to ai yanzu gashi danta ya chinye kurwar Diyam ko? kamar yadda ita kuma ta chinye ta baban Diyam, na rasa yadda zanyi da yarinyar nan, nayi fadan nayi nasihar nayi dukan amma abun ya faskara, gashi da shegen naci kamar jinin mayu, bana son mu’amalar yarinyar nan da yaron nan wallahi kullum gani nake kamar zai cutar da ita, kullum in suna tare sai inyi ta fargaba” Mama ta sake dariya tace “bafa mayen bane kin sani kuma. Yara ne, ki barsu suyi wasansu mana, ki kwantar da hankalinki kiyi tayi mata addu’a” Inna tace “idan ba maye bane ta bangaren uwarsa waye yasan waye shi ta bangaren ubansa? Ni fa tunda matar nan tazo gidan nan da yaron nan ban taba jin ko da sau daya ta ambaci mahaifinsa ko wani dangin mahaifinsa ba, ban taba ganin an kaishi dangin ubansa hutu ba. Ni ba dan makota sun tabbatar mun an daura mata aure anan bayan layi ba da sai ince anya ba shege bane ba? To ko ma dai ba shegen bane ba akwai wani mummunan abun da suke boyewa a game da mahaifinsa. Shi kuma babansu ko na tambayeshi cewa yake ina ruwana? Wai ai Allah ma ya hana mutum ya shiga abinda babu ruwansa” Mama tace “to yanzu menene abin yi?” Inna tace “yanzu ni dai so nake ki tambayi baban Diyam tunda wannan satin zasuyi hutu dan Allah ya baki ita da Asma’u duk ki tafi dasu gurin ki suyi hutunsu a can kona samu zuciya ta ta huta kafin su dawo”. Mama tace “au yanzu akan agolan kike so ki raba yara da gidan ubansu? To Allah ya sa ya bani din dan kinsan halin mijin naki ba wanda yake gane kansa sai zainabu abu, Allah yasa ma kar yace sai dai in hada har sadaukin in tafi dasu tare” ta fada tana tsokanar Inna, Inna tace “Allah ya kiyaye. Allah ya tsari gatari da saran shuka. Insha Allah ko kofar gidanki ba zai sani ba ballantana ya ga ciki”. Ni dai ina kwance ina jinsu, amma sai naji duk raina ya baci saboda babu abinda na tsana irin a kaini wani gidan, saboda bana so a raba ni da Sadauki.

Bayan ta tafi da daddare ina dakin Ummah muna cin abinci a plate daya dani da ita da sadauki. Tana ta loda min nama a gabana wai inci inyi girma in kamo Sadauki. Shi kuma yana ta min dariyar yadda na dage bil hakki nake cin abinci wai kamo shi zanyi duk kuwa da cewa a lokacin ya kusan yin biyu na a girma tunda ni bani da garun jiki shi kuma girma ne dashi. Nace da Ummah “Ummah menene agola?” Tayi shiru tana kallona bata ce komai ba, na cigaba “Inna naji ita da Mama suna cewa wai Sadauki agola ne, sannan kuma maye ne” Inna ta ajiye chokalin hannunta, Sadauki ya kamo hannuna yace “Diyam, agola shine yaron da aka haifa sai iyayensa suka rabu sai uwarsa tayi wani auren ta tafi dashi, mijinta kuma ya rike shi kamar dansa. Kamar ni kenan yadda Baffa ya rike ni amma ba shine ya haife ni ba” nace “to kuma da gaske kai maye ne?” yayi dariya yace “sosai ma kuwa. Yanzu ma sai in cinye ki” ya fada yana yi min chakulkuli ni kuma ina kyalkyala dariya nace “wayyo na tuba kar ka chinye ni” hararar da Ummah ta zabga masa ne yasa ya sakeni muna cigaba da dariyar mu sannan Ummah ta kalle ni seriously tace “Diyam, idan kinji innar ki tana hira da wani, ko cikin yan uwanku ko baffanku, ki daina zuwa kina gaya min kinji? Nima kuma in kinji ina magana da wani kar kije ki gaya mata. Babu kyau kinji?” Na gyada kaina. Asma’u ta leko tace “addah ki zo inji Inna” Ummah ta yafito ta tace “zo Ma’u kici abinci” Asma’u ta makale kafada, Ummah ta dauko cinyar kaza tace “zo ki karba” a hankali Asma’u ta shigo ta tsaya  daga nesa ta miko hannun. Ummah tayi charaf ta kamata ta dora akan cinyarta, tun Asma’u tana zillewa har sai gata dumu dumu tana lomar abinci. Muna cikin yi mata dariya nida Sadauki Inna ta shigo da saurinta, ta damki kunnena ta damki na Asma’u, a tare muka saki kara a haka ta fige mu har daki taja kofar ta ta saka sakata.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button