Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 46

Chapter 46
46

…………Tun Raudha na irga sakanni harta koma mintuna, kamar wasa suka cinye rabin awa. Data yunƙura zata tashi Ramadhan zai sake ƙanƙame mata hannu, ga

kansa bisa cinyarta. Fahimtar kamar barcin nasa baiyi nauyi ba yasata haƙuri ta sake bashi lokaci harda jingina da fuskar gadon, cikin rashin sa’a itama

barci yay a won gaba da ita a wajen mai nauyi dan a gajiye take yau ga rashin barcin jiya cike da idonta dama.

    A hankali ya fara buɗe idanunsa da sukai masa nauyi irin na mai farkawa a barci da rashin jin daɗin jiki. Alhmdllhi zazzaɓin ya jima da sauka. Hakama

ciwon kan kaɗan-kaɗan yake jinsa shima yanada alaƙa da maganin murar da bai gama sakinsa ba dan barcine taf a idanunsa. Sabo da tashi sallar asuba akan

lokacinta ya sashi farkawa. Hanunta da ke riƙe a nasa fuskarsa a kai ya ɗan tsurama ido, tun yana kallonsa dishi-dishi cikin ɗan hasken lamp har idonsa ya

dai-daita. Zuciyarsa ce ta ɗan motsa na alamar mamaki, yay saurin ɗaga kai ya dubi sama. Itace kuwan da gaske, kuma akan cinyarta kansa yake. Ta ɗan zama

kaɗan ta kwanta saɓanin da da take zaune. Sai dai a kallo ɗaya ya fahimci kwanciyar batai mata daɗi dan a matuƙar takure take a wajen. 

    Idanunsa ya dafe tare da cije haƙoransa ya tura yatsun hanunsa cikin sumar kansa. ‘Ya ALLAH’ ya faɗa a hankali cike da jin haushin kansa. Dan ya gama

fahimtar lallai anyi abun kunya a daren jiya. Inhar irin sambatun daya san yanama Anne idan yana zazzaɓi yay mata itama to shikan dai yagama ganin takansa,

raini kuma tsakaninsa da yarinyarnan ya samu gurbin zama. ‘Ni Ramadhan miya shiga kaina ne wai?’.

   Ya sake faɗa a fili lokacin da yake tashi zaune hanunsa dafe yaɗan karkata yana kallonta. Duk da takaicin kansa da yake ji hakan bai hanashin jin

tausayinta ba. Shi kansa ya sani idan shine bazai iya juriyar kwanciya haka ba dan kawai wani yaji daɗi shi. Jin za’a tada salla ya sashi miƙewa ya sakko a

gadon da ƙyar, sai da Raudha ta tabbatar ya shiga bayin sannan ta buɗe ido a hankali. Tun motsawarsa itama ta farka, ta ɗaga hanunta da yay matuƙar tsami da

ƙyar taɗan yarfar, wani irin azaba ya ratsata. Saurin riƙewa tai da ɗayan tana cije baki. Da ƙyar ta iya tashi dan kafaɗarta zuwa wuya suma duk a riken

suke. 

     Cikin dauriya ta fita a ɗakin zuwa nata dan shima taji motsin ruwa alamar wanka yake. Itama da gasa jikinta ta fara, duk da ba saki hanun da wuyan

sukai ba haka ta daure bayan idar da salla ta nufi kitchen. Tunda ta fito ma’aikatan gidan daketa fitowa domin tsaftace sashen ke zubewa suna gaisheta. Babu

sa’anta a cikinsu, ta tabbatar kuma ko’a ilimi sun fita, dan haka take matuƙar jin nauyin wannan girmamawa da suke mata. Sai dai tana dauriyar dannewa da

amsa musu a dake dan wani girman idan ALLAH ya baka dole kai haƙuri ka riƙe.

    A kicin ɗin ma duk zubewa su kuku sukai suna gaisheta, sukam har sun tsaftace ko’ina sunama ƙoƙarin fara ɗora abinci ne. Tambayar mi zasu dafa tayi,

suka sanar mata. Babu abinda ya kwanta mata da yanayin mara lafiya, dan haka tace suyi iya wanda za’aci kawai. Ita kuma ta fara ƙoƙarin haɗama Ramadhan da

taimakon Agnes da ita kaɗaice kuku mace a cikinsu. Haka kawai nutsuwar Agnes ɗin ke burgeta. Gata dai ba muslma ba amma bata da rawan kai, kuma bazaka taɓa

ganinta da shigar banza ba. Haka farce da ƙarin gashi duk bata sakawa.

    Komai suke Agnes a girmame take tayata duk da ta girmeta sosai, amma tsabar girmamawa Mommy take kiran Raudha. Tsaf suka kammala komai, Raudha zata

ɗauka basket ɗin Agnes ɗin tai saurin ɗauka cike da girmamawa. “No Mummy zan ɗauka”.

   Cikin ɗan Murmushi Raudha tai gaba dan bata son gwasale Agnes ɗin. A tare suka haura saman, Agnes zata nufi dining Raudha ta dakatar da ita ta amsa da

mata sannu. Kai tsaye ɗakin Ramadhan ta nufa, haka kawai murmushi ya suɓuce mata tunawa da abinda ya faru jiya dama abinda taji yana faɗa ɗazun, ta gama

fahimtar baya ƙaunar raini sam. A zuciyarta take faɗin (karka damu, indai Aminatu ce har abada babu raini tsakaninmu). 

   A fili kam sai tai knocking ƙofar kaɗan dayin sallama. Bataji an amsaba sai kawai ta tura ƙofar tana ƙarayi. Duk abinda take yana kwance yana jinta, sai

dai yay luf fuska a tamke dan kawai yasan tunda har jiya yay abun kunya ta gama samun hanyar rainasa. Raudha har zuciya bata kawo lanbo yay mata ba. Ta

ajiye basket ɗin ta fita.

    Da kallo ya bita harta fice.

  ★★Sai da ta kammala shirinta na fita tsaf cikin kayan mutunci sannan ta fito tare da kulle ɗakinta dan tasan a koda yaushe su Lubnah zasu iya dawowa

gidan. Koda ta koma ɗakinsa ta iskesa still kwance sai jikinta yay sanyi, duk zumuɗinta na son tafiya makarantar kuma sai ya fita mata a kai. Ajiye bag

ɗinta da hijjab tai ta nufi toilet, tsaftacesa tai ta fito ɗakin shima ta gyara iya inda bazata takura masa ba. Daga haka ta ɗauka bag ɗinta ta koma ɗakinta

dan ta haƙura da makarantar kawai tunda shima bazai fita ba.

    Acan waje tuni securitys ɗinta da jiya ta gudumawa suna falon ƙasa suna jiran fitowarta. Hakama driver ya shirya tun da wuri dan gani suke jiya

sakacinsu ne ya sata fita a gidan badasu ba. Basma ta kira ta sanarwa yau bazata shigo school ba. Daga baya sa nuna mata abinda aka kawai. Bata bama Basma

damar yin ƙorafi ba ta kashe wayar gaba ɗaya itama ta kwanta, dama barcine taf a idonta ga ciwon da jikinta ke mata akan kwanciyar jiya.

   Tunda cos ya ga takwas ta wuce shugaban ƙasa bai fitoba yasan murar jiya ta kwantar da shi kenan. Saƙo ya tura masa kawai ya cigaba da abinda ya dace dan

Alhmdllhi ma yau abubuwan da Ramadhan ɗin zaiyi duk ba masu tsawwalawa bane. Zaman meeting ne sau kusan huɗu duka kuma an riga an tsara wanda zasuyi zaman.

Abinda yake tilas saka hannu ne akan wasu takardu.


     Tunda su Basma ke bada labarin Raudha ta fara karatu a school ɗinsu zuciyarta ke a ƙuntace. Lallai ta sake tabbatarwa ɗanta baya tare da ita. Komai

daya shafesa sai dai taji a shanun ƴan talla. Tana cikin wannan yanayi Mardiyya tazo gidan, ɗiyarta ta biyu dake bin Ramadhan. Daga office take taga ya dace

ta biyo ta gaishesu dan rabonta da gidan tun bikin Ramadhan ɗin. Haka take ita bata da kwaramniya, ga haƙuri. Lokuta da dama mutanen gidan kan ɗauketa wadda

bata ɗaukar abu serious, sai dai kuma ba haka bane. Ita irin mutanen nan ne da babu ruwansu da shiga sabgar daba tasu ba, muguwar ƴar I don’t care ce ta

bugawa a jarida. Halayyarta ya saka bata wani shiri na’azo a gani da Gimbiya Su’adah. Yaranta huɗu, tare da mijinta suke aiki a companyn su na kansu da

sukai haɗin gwiwar ginawa ita da shi. Ba ƙaramin bala’i a lokacin taci ga Gimbiya Su’adah ba. Amma tai fumfurus ta shareta. Da farko robobi companyn ke

fitarwa, a hankali abubuwa suka kara bunƙasa takai har designes na wasu abubuwan daya shafi kayan kitchen suna sarrafawa. Kamar wasa sai gasu sun bunƙasa

suma ana kwatantasu a jerin manyan kamfanoni dake sarrafa abubuwa masu muhimmanci a ƙasar.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button