Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 55

Episode 55*

……….Yau ɗin ma dai kukan tasha sosai fiye dana ranar ma, a ganinta yauɗin ma babu banbanci da shekaran jiyan. Shidai aikinsa lallashi da jinjina

ragwantakarta, duda dai yasan shi ɗin bana wasa bane. Bayan sallar asuba koda ya nuna sake ziyartarta kuka ta saka mishi iya gaskiyarta tana roƙonshi idan

ya sake mutuwa zatai ita dai. Ta bashi tausayi ta bashi dariya kuma. Amma sai ya gimtse da nuna mata baifa san zancen ba a haka zata saba ai. Kuka sosai ta

dingayi tana yarfe hannaye kamar wata ƙaramar yarinya. ALLAH ne ya taimaketa Bappi yay kiransa zasuyi magana, dan dama shirin office zaiyi daga Taura house

can ya nufa. Ita kuma sai ƙarfe ɗaya zata wuce gaida su asabe daga can ta zarce gida.
       Badan yaso ba dole ya miƙe ya zura doguwar rigar jallabiya ya fita batare daya kalli Raudha dake maƙure cikin labule ba tana sharar hawaye. Ganin ya

fice ta faɗa toilet, wanka tayi da ƙara gyara jikinta dan ita dai harga ALLAH zafi takeji sosai. Yau dai anyi jarumta an shiga ruwan zafi tanata raki ita

kaɗai. Koda ta fito harta shirya ta gyara ɗakin bai dawo ba. Dan haka ta saka hijjab ta fita gaida jama’ar gidan.
     Kamar ko yaushe bata wani samu tarban arziki ga gimbiya Su’adah ba. Sai ma zageta tas da Lubnah da Aynah sukayi wai kwana uku batazo ta gaishe da Maah

ɗin ba. Bata da abin faɗa dan tasan ita mai laifi ce. Yau ma da taimakon Bilkisu ta baro sashen bayan ta zage Aynah da Lubnah duk da kuwa duk sun girmeta.

Masifa taitaima Raudha akan lokaci yayi da zata ƙarfafa ranta tabar zama su Lubnah na takata yanda suke so koda agaban Maah ne. Maah uwace, amma su ai

ƙannene a gareta koda sun girneta tunda kanen mijinta ne. Murmushi kawai Raudha tayi amma komai batace ba.
        Ƙin komawa tai part ɗinsu duk da Anne tace Ramadhan ya baro wajen Bappi, suna nan a falon suna taya Anne shirya table Ramadhan ya fito cikin shirin

office. Ɗanyar shaddace golden yollow a jikinsa daketa maiko harda babbar riga, sai dai bata cika girma ba dai-dai irin ta matasan zamani da suke yayi. Sai

baƙin takalmi chukka boot da hula tangaran daketa ɗaukar idanun mai kallon. Ko kunya babu ya miƙama Raudha dake ƙoƙarin gyara mayafinta agogonsa zenith

wai ta saka masa. Sai wani faman ɗaure fuska yake. Sai da taɗan dubi sashen da Bilkisu da Anne suke taga sun ɗauke idanunsu kamar basu san mike faruwa ba

sannan ta amshi agogon ta ɗaura masa kunya kamar ta nutse.
      Kona gode babu ya raɓata ya wuce zuwa dining. Ta ɗan bisa da kallo ranta fes dan gara wannan fushin da azabar da tasan zata sake ɗanɗana a hanunsa.

Anne ce ta sakata dole ta haɗa masa abinci, sannan suma suka zauna har Bilkisu da data karya anan.
     “Yaya kamar bakajin daɗi?”.
Cewar Bilkisu cike da kulawa. Anne da tun ɗazu hankalinta na kansa itama dai kallonsa tai. Ya ɗan yamutsa fuska da sake tsuketa. Sai dai komai baice ba.

Anne ce ta sake maimaita masa tambayar Bilkisun. Cikin ɗan haushi-haushi yace, “Kawai bana son fitar ne”.
     Ƴar dariya Anne da Bilkisu sukai da lallashinsa. Raudha kam da tasan ainahin fushin murmushi kawai tai taƙi yarda kuma su haɗa ido. Shi ya fara miƙewa.

Harya gama sallama da Anne zai wuce ya faki idonta ya sakarma Raudha ranƙwashi akai.
    Ba shiri ta saki karamar ƙara. Gaba yay abinsa ko waiwaye babu, Anne da komai ya faru akan idonta tace, “Mugunta dai babu ƙyau wlhy Ramadhan mita

maka?”.
      Ƙin tankawa yay, sai ya ɗagama Anne yatsunsa biyu alamar bye. Ita dai Bilkisu dariya kawai take ranta fal nishaɗi haƙarsu ta kusa cimma ruwa. (Batasan

tuni tacin ba itace bata da labari). Bayan mintuna kaɗan suka jiyo jiniyar tafiyar motocinsa. Hakan ya bama Raudha damar bararrajewa suka daura hira da

Bilkisu da Anne. Kusan ƙarfe goma baƙuwar Anne ta iso……
         Sosai kunya ta lullube Raudha lokacin da hajiya take bayanin kayan da Anne tasa aka kawo mata nagartattu haɗin sakwattawa birnin shehu tun daga

ƙasar Nigeria. Hajiya. Bata wuce ba sai kusan sha biyu, a lokacin Raudha ma ta mike taje tai shirin dan lokacin tafiyarsu ya gabato. Umarnin Anne ta bi na

zuwa yima su Gimbiya su’adah sallama. Bayan ta kammala da kowane part harsu Yafendo ta nufi part ɗin surukarta a ƙarshe. Ita kaɗai ta samu a falo hakimce

cikin kwalliya sai zuba kamshi take, duk da tasan bata kaunarta ta daɗe da bata lambar girma da yabo na iya tsara kwalliya da ado, dan sosai jikin gimbiya

Su’adah ke ɗaukar wanka, ƙyaƙyƙyawa ce itama gata fara tas masha ALLAH, matsalarta kawai bata fara’a kamar wata sojiya????.
      Kamar ko yaushe data gaisheta bata amsaba. Ta watsar da ita a durƙushe tsahon muntina, Raudha data ga karta makara tai mata sallama zata mike amma

saita dakatar da ita. Cike da gadara da tsanar data kasa haɗiyewa tata tace, “Kin dage sai kin zauna da Ramadhan duk da na nuna miki hanyar salama kin

runtse idanunki. Okay fine, sai ki shirya shigowar Aynah ku goga kishi, mai sa’a ta haye”.
     Wani irin dummm kunen Raudha ya ɗauka. Ta ɗan ɗago ido ta dubi gimbiya Su’adah. Sai dai wulaƙantaccen kallon data maka mata ya sata maida idanun ƙasa

dole. wani irin abune yake sukar zuciyarta mai zafi da batasan ma’anarsa ba. (Kishi?) kai ina na kishi bane, domin *babu so miya kawo kishi? maybe tsoro

no kawai. To amma abinda takeji baya kama da tsoro sai jin ɗaci. Dan har wata hajijiya takeji kamar tana yawo da kanta a sararin samaniya. Sai dai ta danne

a nutse taima Maah godiya da sallama ta mike ta fita duk da bata amsa mata ba.

        Gaba daya Raudha bata fahimtar komai a gidan hajiyar birni. Babu abinda ke mata kaikawo a rai da zuciya sai furucin Maah na auren Aynah da mijinta

zaiyi. Tabbas ko taƙi kota so ta yarda ta fara son shugaban ƙasa Ramadhan. Irin son nan kuma mai kama zuciya da baya saki cikin sauki, duk da ita har yanzu

bata da tabbacin shiɗin yana son nata. Tun tana dauriya har saida hawaye suka dinga ziraro mata, saukintama akwai ba’a gaban Asabe bane. Kagara tayi ta koma

gida dan bata son tayar musu da hankali, gefe kuma tana kwaɗayin yin maganar da Mommy ko taji sanyi a ranta dai.
     Basu bar gidan ba sai bayan sallar la’asar. Driver ɗinta ta samu yana jiranta, dan hala tai sallama da su Basma da sukai mata rakkiya ta wuce. Kafin su

karasa government house ma tasha kuka sosai a mota, suna zuwa ta danne ranta dai ta amshi tarbar da Mama Ladi da Mama tambaya sukai mata harma da sauran

ma’aikatan sashenta da suka riski dawowar tata.
     Duk liyafar da aka shirya musu ta abinci ita da Ramadhan ɗin da dinner bataji ta birgeta ba. Gashi shi baima shigo gidan ba har kusan tara na dare.

Tana falo tsaye shayi take haɗawa koshi ta ɗan sha ta kwanata sai gashi. Tafiya yake a kasalance babbar rigarsa saƙale a hannu yana ƙoƙarin kunce agogonsa

tunkan ya ida hawowa. Sai da taɗan rumtse ido ta karanto addu’a da fatan ALLAH ya bata ikon shanye halin da take ciki kafin ta juyo garesa.
      Sannu da zuwa tai masa da nufarsa kai tsaye domin amsar kayan hanunsa. Babu musu ya mika mata komai sai dai bai amsa sanun datai masan ba. Sai ma yar

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button