GOJE

GOJE 5 and 6

5&6
Kwanciyarta da kamar mintina goma bacci ya kwasheta sai dai baccin beje ko’ina ba dafin kunamar ya fara yawo a sassan jikinta, a gigice ta tashi zaune gabadaya jikinta ya dauki rawa ga wani irin gumi da yake karyo mata! rikicewa tayi ta rasa inda zata sanya ranta taji dadi.

Gurin ya karaso, yana tambayarta, abunda ke damunta, da kyar ta iya bude baki tayi magana.
Bece komai ba ya bar gurin, halin da take ciki besa ta bishi da kallo ba, har ya dawo kanta yana kasa wannan karan kuka ya samu ta nayi, ta dan bashi tausayi kadan, amma bai nuna a fuska ba.

Ya bude gwangwanin Milo din dake hannunsa, wani abune mai duhu a ciki, da alama magani ne aka kwaba da mai, ya kalleta da fadin.” Zaki iya nuna min gurin da kunamar ta cijeki.”?

Wani irin kallo ta tsawa masa, ta dauke kanta, ranshi ya baci ya daka mata tsawa da fadin” Taimakonki fa zanyi kike min kallon banza kin san wanene a gabanki kuwa.”?

Hannu tasa ta goge fuskarta ta daure zugin dake damunta, cikin rashin tsoro tace.” Sanin wanene kai bai dameni ba, na dai san ka amsa suna biyu wato barawo kuma dan ta’addah.”!

Ya tsira mata idanuwansa masu kaifi! yana mamakin maganarta, ‘barawo kuma d’an ta’addah! tunda yake a duniya babu wanda ya ta’ba kiransa da sunan barawo sai ita, kalmar d’an ta’addah kuwa yana ji tana yawo a gari a kansa.

Ya girgiza kansa cikin yanayin maganarsa yace.” Wannan shine karon farko da aka ta’ba kirana da wannan kalmomin a gaban idona, kiyi kokarin kiyaye harshenki kafin ki bar hannuna, GOJE! nake ba’a kawo min wargi duk tsagerancinki ni zan daidaitaki.

Ta kalleshi a wulakance kafin tace.”A hakan? babu tarbiyar! ka fara daidai ta kan…………’Barin makauniya yayi ya fuskarta, a take hancinta ya tsinke da jini, tasa hannu ta dafe, jiki na kyarma! take kallonsa, fuskarsa ta rikide da zallan bacin rai!

“Zaki janyo nai miki mugun rauni a gurin nan, babu ruwana da kowace masarauta kika fito, ki sani ba’a nuna ni da yatsa ban karya ba! sannan ba’a jayayya dani, kuma bana magana biyu, Billahil-lazi hurramanu! duk sanda kika kara fadin wata mummunar magana akaina sai na illataki.”!

Shuru tayi jikinta yayi bala’in mutuwa ganin yanda hancinta ke zubar da uban jini shine abinda yafi zaburar da ita.

Ta kalleshi, yana safa da marwa a gurin, tace.” A kan me ba zan kira ka da wannan suna ba? ka sato ni a gaban iyayena domin su baka kudi. akan me ba zan kiraka da ‘Barawo ba me kake bukata? da ka kawoni daji ka ajiye kana azbtar dani, kamar ni Zinatu wacce ta gaji sarauta gabada da baya ina rayuwa a wannan kazantaccen gurin, tare da kai makaskanci to saurara kaji da kyau! wannan jinin da ya zuba, be zuba a banza ba, wallahi sai kayi daka sanin zubar dashi.”!

Hannu d’aya yasa cikin aljihun jins din dake jikinsa, ya dan sunkuya tare da dogare gwiwarsa, fuskarta ya dago da hannunsa, yana kallonta tana kallonsa, yace.”Daga wace masarauta kika fito naga kina girmama kanki kina mutunta kanki, duk wanda ya gaji saurata baya kambaba kanshi kamar yanda ke kike, ina so ki sani zargin da kike a kaina kar ki gazgata, Allah ya kawoni ne tareda jama’ata domin na taimakeki, kuma zan taimakaki bakin kokarina, amma ni zan koya miki tarbiya.

Magana za tayi ya sanya yatsunsa biyu ya murje fatar bakin………..tsam! ya rike lebunan yana ligwigiwitawa, kukan zucci kawai take, jikinta yayi mugun sanyi, yana sakin bakin ta silale a gurin, yaja tsaki da furta “kalankasa kawai.”!

Zanin dake nannad’e a jikinta ya janye duk tana jin abinda yake amma tsabar yanda jikinta yayi tubus, ta kasa hanashi sarrafata.

Bai damu da kallon wasu sassan na jikinta ba, domin gabad’aya babu wani feelings a tare dashi, tunda yake sai yace babu ranar da wata mace ta ta’ba tayar masa da hankali duk zubi da kirar dake gareta, Asalima yakan jima bai shiga yanayi na bukata ba, shiyasa auran baya gabanshi, wanda uwar rikonshi wato kakarsa Uwale keyi masa surutu akan hakan.

Da kanshi ya lalubi inda kunamar! ta harbeta ya shefe gurin da magani, ganin duk yaran nashi sun bar gurin yasa ya bude mata jikin domin qunar tasha iska.

Har ya gama abinda yake a gurin bata daina zubar da hawayen takaici ba, tayi turr! da wannan rayuwar da take ciki, a tunaninta hanya ba zata iya had’awa dashi ba, sai gashi w Kazami- Bagidaje! irin sa yana ganin sirrin jikinta. tana ganin wannan ko hadimanta (masu yi mata bauta) sun fishi kyawun gani sai gashi a banza yana yin yanda yake so a kanta ya tatta’ba jikinta babu tsoro ko shakka a tare dashi hawaye masu zafi ta goge tana jimanta al’amarin.

Taji dadin maganin sosai domin tana tsaka da tunanin hanyar da zata bi domin kubutar da rayuwarta bacci mai nauyi ya dauketa.


Kana ganinta kaga bafulatana, doguwa ce sambal kyakykyawa a fuska, gata fara tas! ta tara duk wasu abubuwa da da namiji ke bukata amma hausawa sukace wai Dan Adam tara yake be cika goma ba, Hamra’u bata da cikkar kirji hakanan kuma babu baya a tsaye take kamar muciya da zani, sai dai akwai tarbiya da kunya irin ta fulani.

A nutse tayi sallama a gidan, Uwale dake uwar daki ta amsa, da fadin.” ‘Yar halak yanzu nake maganarki a zuciyata.

Murmushi tayi ta cire takalminta, ta shiga dakin, Uwale na kurbar kunu ta mika mata kofin da fadin ” Bisimillah.”
Girgiza kai tayi tana murmushi tace.” Ai daga gida nake kuma sai dana karya kafin na fito.

Dariya tayi irin ta tsoffi tace.” Hamra’u kenan wai me yasa duk sanda zan baki abu sai kice daga gida kike ko dai kankyamina kike ne.”?

Da sauri tace.”Aa Wallahi ba haka bane Uwale na koshi.”

Tace.”To ai shikkenan duk ya mutan gidan.”? Tace.”Suna nan lafiya lou alhamdullhi babanmu yace a gaisheki da kyau.”

Tace.”Ina amsawa ai a cikin satin nan nake so nazo gidanku mu gaisa sai kuma UMARU Yayi tafiya gashi zai dauki sati guda bai dawo ba.

A sanyaye tace.”Yanzu fa nake shirin tambayarki ina yake shine zakice yayi tafiya kuma sai yayi sati zai dawo.”

Tace.”Eh haka yace min da zai tafi kin san dai yanayin al’amuranshi, wani sa’in ma har wata guda ya kanyi yana gwagwarmaya a daji”

A raunane tace.” Ni wallahi ba naso yana irin wannan yawace-yawacen tsoro nake kada ‘yan fashi su kasheshi ko kuma namun daji su cinyeshi.”

‘Yar dariya tayi tana sud’e kofin kunun data gama sha tace.”Sai dai kiyi hakuri Hamra’u wannan mijin naki yayi nisa addua kawai zaki dinga yi masa.

Tace.”Kullum inayi masa addua tare da sauran jama’a.” Tace.”yawwa hakan yana da kyau, sannan ki cigaba da hakuri insha Allahu, hankalinsa zai karkato kanki.”

Idonta ya cika da ruwan hawaye, tace.”Uwale sai nake ganin kamar baya sona tausayina kawai nake gani a kwayoyin idonshi.

Tace.” To in banda abinki Hamara’u ai sai da so ake tausayi, da baya sonki ba zai tausaya miki ba.”

Shuru tayi tana nazarin maganar, itafa tunda take dashi babu wata kalmar so daya taba furta mata, asalima yana kiranta da kanwata, amma bai taba cewa Hamra’u ina sonki ba, sai dai yana tsananin bata kulawa komai take bukata idan tayi masa magana kai tsaye yake mata, wannan dalilin yasa iyayenta da ita Uwalen suke ganin kamar sonta yake, ajiyar zuciya ta sauke ta kudire a ranta cewa idan ya dawo zata cire kunya ta tambayeshi matsayinta a zuciyarsa.

Hamra’u ‘yar kanin Uwale ce, tun tana yarinya Allah yasa mata so dakaunar Goje tun be fahinta ba har Allah ya fahintar dashi, be ajiyeta a wani matsayi na daban ba face wanda take dashi a zuciyarsa, gabadaya tunda ya taso baya da ra’ayin soyayya, shiyasa baya fahimtar tarin ‘yan matan dake k’aunarsa, Samari da yawa a karkarar tasu suna kishi dashi, a cewarsu sai kace shi kadai ne namiji ko wacce budurwa bata da magana sai tasa, ransu yana baci mutuka, suna kuma bala’in kishi a kan haka, ita kanta Hamra’un akwai wanda yake mutuwar sonta amma fafur taki amince masa ita dai Umaru takeso wanda bata da tabbas a kansa…………..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button