GOJE 11 and 12
FREE PEGE
11&12
Tun bayan tafiyarsa farauta, Uwale ta samu ‘kafar yawo, wanda idan yana gari ko nan da can baya bari taje a cewarsa ta tsufa abinda yafi cancanta a gareta ta zauna a gida ta huta, tunda shi yana iyakacin bakin kokarinsa gurin daukar dawaniyarta da duk wani abu da take bukata na yau da gobe.
Ita kuma a nata bangaran haushin abinda yake mata take, ta dingi mita da surutai tana fadin ba zata zauna zuciyarta ta mutu ba sai ta fita ta nemi kudi kodan bada gudumawa idan sabga dangi ta tashi,
Hakan ya sanyashi
yanke hukunci a duk sanda zai fita sai ya sakar mata kare a gidan ya rufe kofar daga waje yayi tafiyarsa.
A ranar yini take d’aki bata fitowa saboda yanda Allah ya zuba mata tsoron kare a rayuwarta, idan ya dawo gidan sai ta fashe da kuka tana fadin.” UMARU saboda bani na haifeka shine kake azabtar dani, ka san sarai bana san kare amma saboda mugunta zaka sa min kare sannan ka rufe kofa ka tafi yawo to babu shakka wata rana zaka dawo ka samu gawata.”
Sai yace.”Uwale idan kina so mu shirya dake ki daina dillanci domin kuwa kina zubar min da mutunci a gari, ni mutum ne mai zuciya da gudun magana bana son jama’a na ganin gazawata a kanki.”
“UMARU Ba zan daina dillaci ba saboda itace sana’ar data ci da kai ta shayar da kai har ka kai munzali, sannan kuma kana maganar zagin jama’a kai yanzu UMARU wane irin zagi ne jama’ar gari ba suyi maka irinshi ba, babu fa wanda yake maka kallon mutumin kwarai mai daraja, kowa yana maka kallon banza tare da kiranka da sunaye masu muni! B’arawo ‘Dan ta’addah! duk saboda wannan harkar daka jefa kanka a cikinta, Mahaifinka da bakin cikin hakan ya mutu dalili irin zagi da habaice-habaicen da mutanan gari ke masa, bana rana dayan biyu bakin cikinka ne ya kasheshi.”
Duk sanda zata fad’i wannan maganar hankalinsa yana tashi mutu’ka, shi fa har yanzu bai ga illar abinda yake aikatawa ba, na farko bai ta’ba tare wani a hanya ya k’waci abunsa ba, na biyu tunda yake ba’a ta’ba kamashi ya haura wani gida yayi sata ba, na uku bai ta’ba yiwa yarinyar wani fyade ba, abu na karshe shine baya muggan! shaye-shayen da zai janyo masa zubewar kima da mutunci, abunda ya sani shine yana busa Sigari sa’i da lokaci sai shan Shisha da ya zame masa masifa, wannan abu biyun sune abunda ya san yanayi bayan haka azimi sallah akan lokaci basa wuceshi, a ganinsa zagin da jama’ar gari ke masa k’in gaskiya ne, babban abin mamaki kuma duk sanda yayi nisan kiwo dashi da jama’arsa ma’ana suka fita farauta, to duk sanda ya dawo gari da yawa masu zagin nasa sune suke zuwa su gurfana a gabansa domin kar’bar maganin sanyin da yake guzurin zuwa dashi.
Ita kanta Uwalen matan da suke zuwa gurinta kar’bar magani suna da yawa, wani sa’in yana kallo zata zabga kudi masu yawan gaske sai sun nemi alfarma a gurinsa sannan take sassauta musu, amma shi anasa b’angaran ‘karamar sadaka yake kar’ba wani sa’in ma kyauta yake bayarwa yace sadaka ayi wa Annabi Salati dubu, Uwale tayi ta jin haushin hakan, idan ya fita sai ta samu buhu mai zurfi ta shiga dakinsa ta kwashe rabin maganin ta boye a karkashin gadonta, idan ta samu sarari ta fita cikin gari ta siyar akan kudi masu yawan gaske.
Wannan dabi’ar ta kakar tashi tana b’ata masa rai, mutuka idan yana so ya tsoratar da ita akan ta daina abinda take sai yace.” Uwale shifa aljani ba’a wasa dashi kuma wannan magungunan da nake zuwa dasu ba a banza nake samu ba, musulman aljanu ne suka lamunce min da hakan domin kin san kowane bawa da hanyar abincinsa to nima bani sukayi domin na taimaki jama’a idan kika wuce gona da iri zan barki dasu.”
Sai ta tsorata ta dinga rokansa kan cewa ya basu hakuri ta daina abinda take, yace shi babu ruwansa taje ta nemi inda suke ta basu hakuri ba maganarsa bace, kuka irin na tsofaffi take sawa ta rikeshi ta hanashi fita tace lallai sai ya basu hakuri sannan zai futa. sai ya fahimci tayi laushi sannan sai yace tayi shuru ya basu hakuri sun hakura amma kada ta sake aikatawa,
Zata amsa da cewa ba zata sake ba, amma cikin ikon Allah idan aka kwana biyu zata manta ta cigaba da sayar da magani da tsada tana boye kudin a cikin adaka a cewarta da kudin zata hada masa lefen auransa.
Kishingide suka sameshi a gurin hutawarsa, ya mike zaune tare dan gyara zama ido ya tsira musu har suka samu guri suka zauna kafin su gaisheshi, ya amsa still idonshi na tsaye a kansu mussaman mutuniyar tashi da yake hango rashin walwala a tare da ita, koda yake tunda al’amarin ya faru gabadaya walwala da farin cikinsu ya gushe duk abinda suke karfin hali ne.
Gyaran murya yayi kafin yace.” Idan kaga wata to za kaga zarah Aysha Safara’u wannan tafiyar taku tana burgeni.”
Babu wacce ta saki fuska a cikinsu, domin kuwa suna ciki dashi sakamakon hade kai da yayi da matarsa suna daukarsu a matsayin marasa tawakkali.
D’aya daga cikin hadimanta ne yaje ya sheda mata cewa yanzu – yanzu ya gansu sun nufi gurin hutawar Maimartaba
Da saurin gaske ta shiga daki ta shiryo ta fito kai tsaye can ta nufa, tana sauri taje ta riski abinda ya kai su bayan itace da girki.
Tunda ta doshi gurin take hangoshi gabadaya hankalinsa yana kan wacce ta tsana a cikin matan nasa fuskarsa akwai alamun sassauci da rarrashi, gabadaya ma kamar ita kadai ce a gurin babu Safah.
Ta isa gurin da sallama wacce bata fito sosai ba.
Ya amsa yana kallonta kafin ya kallesu da fadin.” Kuna ji ‘yar uwarku na muku sallama kunyi shuru.”
Safah ta amsa a ciki Aysha kam ko kallonsa ba tayi ba ballanatana ‘yar koran nasa.
Ta samu guri ta zauna tana ya mutse fuska da fadin.” Ranka shi dade barka da dare.”
Ya amsa “Barka dai Maijidda ya hidima.” Ta amsa “Alhamdullhi.”
Gurin yayi shuru na ‘yan mintina kafin gimbiyar ta kalleshi babu fara’a tace.”Ranka ya dade wannan magana iyakacin nida kai da ‘yar uwata muka tattauna bana son wani yaji abinda ya shafeni da zuriata.”
Ya ‘bata rai da fadin.” Aysha wannan wace irin magana ce? shin ita Maijiddan bare ce a cikinmu.”?
Ta d’aga masa hannu da fadin.” Allah shi gafarta maka tunda na fara maganata kaji sunan Maijidda a bakina.”?
Ransa ya baci mutuka, yace.” Ki sauke hannunki idan ba hakana ranki ya b’aci zaki nuna min abinda zanyi ne? ko kuma zaki hanani iko da abinda na haifa? dake da ita Zinat din da ita Safa da Maijiddan duk ikona ne to ke baki isa ki tsara min yanda zanyi ba.”
Maijidda ta fashe da kuka da fadin.” Ranka ya dade na rasa me yasa har yanzu matarka bata kaunata, meye laifina ? me kuma nayi mata? haihuwa dai Allah ke bayarwa ba wani ba, nima ban cire rai ba.”
Tausayinta ya rufeshi, sassauta murya yayi yace.” Maijidda kada ki sanya damuwa a ranki nida na aureki nafi kowa sanin halinki babu wanda zai kawo min jita-jita a kanki na dauki maganarsa, maganar haihuwa kuma kada ki cire tsammani, zaki haihuwa da izinin Allah, bayan haka kuma baki da shamaki da zuriata zaki iya yanke hukunci akansu ba tare da na daga kai na kalleki ba.”
Gabad’aya suka kalleshi a lokacin da yake wannan maganar, Aysha gaza hakuri tayi tace.” Ba zai yuwu ba ranka ya dade ana duba nagarta da cancanta kafin a yanke hukunci babu wani d’a da zan haifa na amince ya dauki wannan matarka taka a matsayin me kaunarsa duk mutumin da ya fito da kiyayyarsa a sarari a kanka be kamata kayi rayuwa dashi ba.