A Bakin Aurenki Complete
BAK’IN AUREN KI…漏Feenat Ja’afar.
1_Sauri take tamkar taci da k’a, kai daga ganinta
ka ga marar gaskiya, a d’ai d’ai layin da zai
sadata da gidanta ta t’saya tamkar munafuka ta
d’an leka, da sauri ta komar da kai tare da dafe
kirjinta mai barazanar fashe mata… “Na
shigesu.. Ja’afar? Ta fad’a tana mai sake
lekawa, sai karaf sukai ido hud’u dashi,tuni
buguwar zuciyar ta ya k’aru, bata ta6a ganin shi
a irin wannan yanayin ba.
“Mey yasa kika fita bayan yace ka’rki fita?…
Bak’in g’yalenta tasa tana t’sane gumin dake
t’sat’safo mata, cikin jihadi ta fito daga inda ta
boye harda d’aure fuskarta tamkar bata ganshi
ba.
Kanta na k’allon gefe tazo d’ai d’ai kofar gidan
zata shige ba tare da ta k’alli yanayin nashi ba..
Turus taja ta t’saya, ganin yadda ya d’aura wani
mukulli kan wanda ta rufe gidan dashi, cikin
k’arfin hali fuskarta na gefe tace “ya haka?
Wanda bai nan ma yafita,hakan yasa ta kara
fad’in “Ya Ja’afar ya haka?.. Tamkar kububuwa
yake cika, ji yake tamkar ya rufeta da duka dan
takaici, Ashe d’uk uban rat’suwar Salma ta mai
kan ta d’aina a fatar baki ya t’saya?..
Mota ya bud’e yana ko’k’arin shiga ta mot’so da
sauri, “Ja’afar magana nake fa… A tunzure ya
juyo da nufin kifa mata mari tai baya da sauri
gabanta na fad’uwa.
Lalle yau ta ta6o ran y’an maza, cikin bacin rai
yai mata k’allon banza, “kin za6i gidan suna
sama da sharad’i na koh? Toh mey kika dawo yi
min gida? Koh kin manta da sharad’in da na baki
na in kin fita toh kin fita “A BAK’IN AURENKI?…
Ido ta zaro tana dubenshi, kawai sai ta dake,
cikin k’arfin hali tace “A BAK’IN AURENA fa kace
Ja’afar? Daga gidan sunan shine har kake
wannan kumfar bak’in?.. Ta karasa tana y’atsine
mishi fuska,kawai sai ya k’ada kai ya shige mota.
Ganin da gaske tafiya zai yasa da sauri t ajiye
t’siwar ta fara kiranshi, ina,tuni ya juya a kalar
motarahi cikin zafin nama, da sauri ta mat’sa
ganin sai ya iya bi ta kanta..
Tana ganin da gaske yake hakan yasa tuni ta
t’sure, hannu ta aza bisa kanta cikin nadamar
fitar da tai sunan da ba’a ma gaiyace ta ba, “na
shiga uku ni Salma.. Na ja ma kaina wani bala’in..
“Yanzu igiyar Aure na biyu ta t’sinke kenan?..
Tuni zufa ta kara zubo mata dan tunawa da
kalaman Babanta, “d’uk randa zaki kara maimaita
haka Salma sai na 6alla kafarki in kin doso
gidana…. Fad’uwar gabanta ta t’sananta,t’saf
Baba zai aikata mata hakan,
ta k’alli gabar,da yamma, ta ma rasa ta ina zata
fara? Gefen dakalin gidan ta d’an dosana, da
d’ukkan hannunta biyu ta dafe kai,tuni kalaman
Ja’afar ya dawo mata, “in kin fita kin fita A
BAK’IN AURENKI….
Ku biyoni Bayan sallah dan jin yadda zata kaya…
By
Feenat
Ja’afar.
9/29/16, 8:46 AM – Queen Safiyyert馃憫: *A BAK’IN AURANKI* *漏 Feenat Ja’afar*. *3*-
Kai ya k’ada mishi, _”aure ba shine mafita ba
Ja’afar,ka g’yara wacce ke hannunka tukun,bana
tunanin wannan shawara ce_. Murmushi yai tare
da k’ada mishi kai _(“I know)_.. _”Amma ka gane
ba dan dad’i zanyi ba,nasan d’uk duniya ba
abinda Salma taki jini irin nace zan kara
aure,dole na d’andana mata mad’acin da ta
d’andana min nima_. Murmushi Garba yai yana
K’allonshi,wai yau Ja’afar ke maganar zai
d’andanawa Salman sa mad’aci?.. Kai ya girgiza,
lalle Salma tai wasa da damarta, dan yasan irin
dimbin son da Ja’afar ke mata, sai dai gashi za a
kaita a baro,dan ta fara sane ma abokinshi..
_”Bana tofa tawa ba nikam,nasan da kai da
Salma sai Allah,ni d’ai kai tunani abokina,kar ka
yanke hukunci cikin fushi azo daga baya ai
nadama_… Baki ya ta6e, kan ya ciro mukulli a
aljihunshi ya mika mishi, _”k’ar6i mukullin
motarka,dan aure kam nayi na ma gama,kuma
*Bintu* zan aura kasa ido_.. Ido waje Garba yake
k’allonshi,kan ya k’yalk’yale da dariya, _”lalle ka
d’ebo aiki..za kuma ka dasa ma Salma zargin ka
cikin ranta tunda kasan komai_… T’saki yai kan
yace _”zanso hakan ya kasance, dan zata fi jin
haushi sosai_.. Kai Garban ya k’ada yana kunshe
dariya, _”muje na sauke ka toh na Salma da
Bintu,kai (scene) din nan zai dad’in k’allo
wallahi_.. Ya karasa da dariyar keta. Murmushi
kawai yai suka shiga mota,har suka isa gida
Garba na mishi t’siya..da ya had’o shi da Salma
zai kicin-kicin. ************************ A wajen
Salma kuwa,sai da dare yai tana k’wance
d’akinsu na da sai juyi take,wanda ita kanta ta
rasa dalili,har yanzun haushin Ja’afar na kasan
ranta na ya mata wulakanci, sai dai da ta tuna
rabuwar igiyarta d’aya sai taji fad’uwar gaba. Yau
gata a katifa ba ta ita da Ja’afar d’inta ba?..yau
d’aya ta raba alakar matashin kanta(kafad’ar
Ja’afar) sai pillow… Hannu takai kuncinta,da
mamakinta hawaye take,kawai sai ta ida
karasawa ta fashe da kuka.. Wanda kai da gani
na k’ewar Jafaririn ta ne da t’sant’sar
nadama,amma ina,zuciya taki amsar hakan.. Ga
uban sauro da ya damu k’unnenta da ihu duk da
da Katanga a t’sakaninta dasu(net), ga uban zafi
ba wuta ba (Gen), d’uk t’siya tasan da a gidanta
ne da yanzu tana shan iskar injin da Ja’afar ke
k’unna mata d’uk dare ta k’wanta dan bata bidar
zafi.. Ga mama tace ba mai tada mata inji
Babanta baya gari, kuma bata kud’in mai…..
Shima hakan take ga Ja’afar, kusan a hali d’aya
suke,sai dai shi kawai ya kura ma fankar d’akin
da ke kad’awa a saman d’akin ido. Tabbas har
yanzun baida sama da Salma koh a kasan
zuciyarshi.. Yana sonta, so marar misali,duba ga
yadda suka gina soyayyar tasu kamin aure.. Da
za’a ce mishi a da Salma zata sauya hali gaba
d’aya musamman akanshi da zai mu sa… Juyi
yai ya jawo filo,d’uk t’siya tanan yai k’ewar
Salma.. Dan karamin t’saki yai kamin ya tashi yai
waje dan kashe inji. *By* *Feenat Ja’afar*
9/29/16, 8:48 AM – Queen Safiyyert馃憫: *A BAK’IN AURANKI* *漏 Feenat Ja’afar*. 4-
Salma Umar Y’a ce ta biyu gun Mama(Haj Rabi’a)
da Baba(Malam Umar),y’an asalin Yobe
ne,kasuwanci ya kawo kakansu Kano da rabon su
Salma. Su biyu kawai ne a gun kakan su Malam
Bukar Mai buhu,baban su Salma ne karami, sai
yayanshi Baba Aji, yaranshi a kallah za suyi
(16),yayin da Baban Salma ke da uku,Aisha
(Aunty A’i)dan tafi Salma sosai,Salma,sai Ummi.
Kasuwanci ne gadon su Baba,dan koh bayan
rasuwar kakan su Salma sun cigaba da juya
abinda ya rage musu. Suna taimakon juna
sosai,hakan yasa kansu yake a had’e, duk da
rufin asiri ne kawai na Allah. Sannan d’ai-d’ai
iyawa sun bama yaran su karatu da tarbiya,suna
da t’sanani musamman Baban su Salma. Sai dai
fa ita Maman su gani take kakarsu ta yanke
saka,tunda Allah ya hore mata yara mata uku
setin samira ta zuba jari,shi yasa d’ukkan wani
abu akan A’i yake karewa dan ita tasa a lokacin.
Ba lefi,ak’wai dan k’yau irin na ainashin mutan
kanuri,sai kuma Maman dake asalin Shuwa,ba
farare bane,za dai mu iya kiransu da _”black
beauties”_sirrin su kuwa,diri ne da yalwar gashin
ka da _”beauty point”_ _(dimples)_.. Wanda
tamkar kowa diga mata ake. Hakan yasa kasuwar
Aunty A’i ta daga da sauri,tuni k’wa Mama abin
nema sai ya samu,hakan yasa ta kara sa ma
sauran Burin da yafi na Aunty A’in.. Barin Salma
dake doguwa ce cikin su. Ita kam Salma bata san
ma ana yi ba. Kasantuwar shagonsu Baba ya
zama biyu sai ya zamana aiki yai musu yawa,
har bai samun damar dawo wa gida cin abinci sai
d’ai Ummi koh Salma su kai mishi. Ranar kaiwar
Salma ne,tai shirin Islamiya ta doshi shagon su
Baba. Tunda ta ajiye abinci taki gaba taki