Uncategorized

A Bakin Aurenki Complete

Ad

_____

 BAK’IN AUREN KI…漏Feenat Ja’afar.

1_Sauri take tamkar taci da k’a, kai daga ganinta

ka ga marar gaskiya, a d’ai d’ai layin da zai

sadata da gidanta ta t’saya tamkar munafuka ta

d’an leka, da sauri ta komar da kai tare da dafe

kirjinta mai barazanar fashe mata… “Na

shigesu.. Ja’afar? Ta fad’a tana mai sake

lekawa, sai karaf sukai ido hud’u dashi,tuni

buguwar zuciyar ta ya k’aru, bata ta6a ganin shi

a irin wannan yanayin ba.

Ad

“Mey yasa kika fita bayan yace ka’rki fita?…

Bak’in g’yalenta tasa tana t’sane gumin dake

t’sat’safo mata, cikin jihadi ta fito daga inda ta

boye harda d’aure fuskarta tamkar bata ganshi

ba.

Kanta na k’allon gefe tazo d’ai d’ai kofar gidan

zata shige ba tare da ta k’alli yanayin nashi ba..

Turus taja ta t’saya, ganin yadda ya d’aura wani

mukulli kan wanda ta rufe gidan dashi, cikin

k’arfin hali fuskarta na gefe tace “ya haka?

Wanda bai nan ma yafita,hakan yasa ta kara

fad’in “Ya Ja’afar ya haka?.. Tamkar kububuwa

yake cika, ji yake tamkar ya rufeta da duka dan

takaici, Ashe d’uk uban rat’suwar Salma ta mai

kan ta d’aina a fatar baki ya t’saya?..

Mota ya bud’e yana ko’k’arin shiga ta mot’so da

sauri, “Ja’afar magana nake fa… A tunzure ya

juyo da nufin kifa mata mari tai baya da sauri

gabanta na fad’uwa.

Lalle yau ta ta6o ran y’an maza, cikin bacin rai

yai mata k’allon banza, “kin za6i gidan suna

sama da sharad’i na koh? Toh mey kika dawo yi

min gida? Koh kin manta da sharad’in da na baki

na in kin fita toh kin fita “A BAK’IN AURENKI?…

Ido ta zaro tana dubenshi, kawai sai ta dake,

cikin k’arfin hali tace “A BAK’IN AURENA fa kace

Ja’afar? Daga gidan sunan shine har kake

wannan kumfar bak’in?.. Ta karasa tana y’atsine

mishi fuska,kawai sai ya k’ada kai ya shige mota.

Ganin da gaske tafiya zai yasa da sauri t ajiye

t’siwar ta fara kiranshi, ina,tuni ya juya a kalar

motarahi cikin zafin nama, da sauri ta mat’sa

ganin sai ya iya bi ta kanta..

Tana ganin da gaske yake hakan yasa tuni ta

t’sure, hannu ta aza bisa kanta cikin nadamar

fitar da tai sunan da ba’a ma gaiyace ta ba, “na

shiga uku ni Salma.. Na ja ma kaina wani bala’in..

“Yanzu igiyar Aure na biyu ta t’sinke kenan?..

Tuni zufa ta kara zubo mata dan tunawa da

kalaman Babanta, “d’uk randa zaki kara maimaita

haka Salma sai na 6alla kafarki in kin doso

gidana…. Fad’uwar gabanta ta t’sananta,t’saf

Baba zai aikata mata hakan,

ta k’alli gabar,da yamma, ta ma rasa ta ina zata

fara? Gefen dakalin gidan ta d’an dosana, da

d’ukkan hannunta biyu ta dafe kai,tuni kalaman

Ja’afar ya dawo mata, “in kin fita kin fita A

BAK’IN AURENKI….

Ku biyoni Bayan sallah dan jin yadda zata kaya…

By

Feenat

Ja’afar.

9/29/16, 8:46 AM – Queen Safiyyert馃憫: *A BAK’IN AURANKI* *漏 Feenat Ja’afar*. *3*-

Kai ya k’ada mishi, _”aure ba shine mafita ba

Ja’afar,ka g’yara wacce ke hannunka tukun,bana

tunanin wannan shawara ce_. Murmushi yai tare

da k’ada mishi kai _(“I know)_.. _”Amma ka gane

ba dan dad’i zanyi ba,nasan d’uk duniya ba

abinda Salma taki jini irin nace zan kara

aure,dole na d’andana mata mad’acin da ta

d’andana min nima_. Murmushi Garba yai yana

K’allonshi,wai yau Ja’afar ke maganar zai

d’andanawa Salman sa mad’aci?.. Kai ya girgiza,

lalle Salma tai wasa da damarta, dan yasan irin

dimbin son da Ja’afar ke mata, sai dai gashi za a

kaita a baro,dan ta fara sane ma abokinshi..

_”Bana tofa tawa ba nikam,nasan da kai da

Salma sai Allah,ni d’ai kai tunani abokina,kar ka

yanke hukunci cikin fushi azo daga baya ai

nadama_… Baki ya ta6e, kan ya ciro mukulli a

aljihunshi ya mika mishi, _”k’ar6i mukullin

motarka,dan aure kam nayi na ma gama,kuma

*Bintu* zan aura kasa ido_.. Ido waje Garba yake

k’allonshi,kan ya k’yalk’yale da dariya, _”lalle ka

d’ebo aiki..za kuma ka dasa ma Salma zargin ka

cikin ranta tunda kasan komai_… T’saki yai kan

yace _”zanso hakan ya kasance, dan zata fi jin

haushi sosai_.. Kai Garban ya k’ada yana kunshe

dariya, _”muje na sauke ka toh na Salma da

Bintu,kai (scene) din nan zai dad’in k’allo

wallahi_.. Ya karasa da dariyar keta. Murmushi

kawai yai suka shiga mota,har suka isa gida

Garba na mishi t’siya..da ya had’o shi da Salma

zai kicin-kicin. ************************ A wajen

Salma kuwa,sai da dare yai tana k’wance

d’akinsu na da sai juyi take,wanda ita kanta ta

rasa dalili,har yanzun haushin Ja’afar na kasan

ranta na ya mata wulakanci, sai dai da ta tuna

rabuwar igiyarta d’aya sai taji fad’uwar gaba. Yau

gata a katifa ba ta ita da Ja’afar d’inta ba?..yau

d’aya ta raba alakar matashin kanta(kafad’ar

Ja’afar) sai pillow… Hannu takai kuncinta,da

mamakinta hawaye take,kawai sai ta ida

karasawa ta fashe da kuka.. Wanda kai da gani

na k’ewar Jafaririn ta ne da t’sant’sar

nadama,amma ina,zuciya taki amsar hakan.. Ga

uban sauro da ya damu k’unnenta da ihu duk da

da Katanga a t’sakaninta dasu(net), ga uban zafi

ba wuta ba (Gen), d’uk t’siya tasan da a gidanta

ne da yanzu tana shan iskar injin da Ja’afar ke

k’unna mata d’uk dare ta k’wanta dan bata bidar

zafi.. Ga mama tace ba mai tada mata inji

Babanta baya gari, kuma bata kud’in mai…..

Shima hakan take ga Ja’afar, kusan a hali d’aya

suke,sai dai shi kawai ya kura ma fankar d’akin

da ke kad’awa a saman d’akin ido. Tabbas har

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button