A Bakin Aurenki Complete

baya,kamar dai da alamun an mata abu daga
gida. Murmushi Baban yai kan yace tazo.. _”mey
aka miki uwata?_ Hawaye ta dan matso halamar
6aci. _”Mama ce ta hana ni kud’in tara_. Kai
Abban ya k’ada yana murmushi kan ya sa hannu
a aljihu ba chanji,gudar naira dari ya fitar kan ya
nuna mata shagon kusa dasu taje tai chanji. Da
sallamarta ta shiga,ta gaida shi,shago ne na
kayan k’yallin mata na sawa, attamfofi da
laces,ga materials kala kala,d’uk zuwanta bata
ta6a shiga shagon ba sai yau. _”Salamatu y’an
mata,ina su Ummi?_ Murmushi tai mishi,dan tana
ganin shi gun su Baba, dattijon na da kirki da
fara’a, banda yaron shagon shi da koh k’allo bai
mata ba, _”suna gida,Baba ne yace aban chanji_.
Kai ya k’ada, kan ya k’allo na zaune a acikin
shagon rike da littafi halamar yana dubawa.
_”amm *Ja’afar*_.. Kai ya dago karon farko,
_”Na’am Abba_,, sai lokacin ya kula da Salma,
_”Ba wa Salma naira ashirin ta tafi kar tai latti_.
Kai ya k’ada kan ya kara k’allo Salman wacce sai
hange take koh za taga wani dan islamiyar su
tana mika hannu. _”k’ar6i man_.. Juyo wa tai
taga yana miko mata kud’i fuska ba fara’a, da
sauri ta k’ar6a tana tafiya tana fad’in _”na gode
Abba_. Da k’allo Ja’afar ya bita,yana ganin Ummi
ce mai rawar kai ashe sauran ma haka suke.
_customers_ ne suka tada shi ya shiga shagon.
Washegari ma sai ga Salma,wannan karan koh
shagon su Baba bata je ba tai shagon su Ja’afar.
Da mutane da kusan d’uk y’an mata ne suna
siyayya, yana ganin Salma ya had’e rai, sam yaki
jinin a 6ata yaro da kud’i, ita kam Salma harda
mishi murmushi tana dago mishi hannu da kamar
abu aciki. T’saki yai,kan ya cigaba da abinda ya
ke,sai da ya sallami kowa kan ya ganta tana
gaida Abban shi da ya fita yana nuna mata cikin
shagon. Da dan gudinta ta shigo,a tunanin shi
kud’i Abban yace ta kara k’ar6a gun shi,dan da
zumudinta ta gaida shi. _”dama Abba ne yace
in_….. Cikin fad’a-fad’a ya katseta, _”bani da
chanji nima yau,jiya an baki kinji dad’i shin_….
Shiru yai sakamakon idonta da yaga ya cika da
k’walla tana k’allonshi. D’uk kuma sai jikinshi yai
sanyi.. A hankali ta ajiye masa gudar naira
ashirin akan benci ta juya tana goge hawaye. Ba
dai kud’in shi ta biya shi ba dan ya mata fad’a?
Da sauri ya d’auka da niyar k’wada mata kira ya
mayar mata sai dai tuni tai nisa sosai. D’uk
kuma sai yaji bai k’yauta ba. Yana nan zaune har
Abba ya dawo, _”kaga Salamatu wai kud’in ka na
jiya ya hau shine ta dawo ma dashi ba”_.. K’allon
Abban yai da sauri, _”Abba kud’i kuma?_
K’allonshi yai kan ya k’ada mishi kai, _”sai da
nace ta tafi wai A’a tana da wani,Salma ak’wai
hankali, ashe batai ma magana ba?_ Shi dai
Ja’afar yai shiru yana jin Abba,sai ya kara jin
wani iri.
[ad_2]