BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 5

Page -5️⃣

Sai after sallah isha’i ya fito harabar gidan ya zauna a inda aka jera kujerun zama domin hutawa, kusa da garden, sai kamshin turare yake kamar sabon ango, fuskarsa cike da annuri, sai dai babu walwala ko kadan a tare da shi.
A hankali ya hade yawun bakinsa ya daga kansa sama yana kallon taurarin dake samaniya, kamin ya juyo yana kallon Amal dake sanye da kayan bachi tana nufo inda yake.

“Ya Talba”

Ya dan sakar mata murmushi kadan.

“Lil Sis ya kike?”

Ta zauna a kusa dake kusa da tashi tana amsawa.

“Lafiya kalau”

Sai kuma ta yi shuru tana kallonsa.

“Kina bukatar wani abu ne?”

Ta girgiza kai ta soma wasa da yatsun hannunta.

“Talk to me Lil Sis fada min damuwarki”

Ya fada yana kallon yanayinta dake nuna akwai damuwa a tare da ita.

“Yaya ka sake yin fada da Ya Leila ne?”

Fada suka yi? Ya zai fada mata? Abun da suka yi fada ne ko aa, shi be ma tabbatar ba, all what he know is ta kira shi wani shi kuma ya fada mata magana, sincerely speaking ma ya manta me yace mata.

“Yeah Maybe”

Ya fada yana dan tabe baki.

“Miya faru?”

“Ta dawo gida tana ta kuka tun dazun, yanzu kuma kuma Daddy ya shigo yai ma Momy fada ita ma kuka take?”

“Why?”

“I don’t know, kawai dai na ji Daddy yana cewa babu wanda ya isa ya wulakanta masa d’a, kuma wai ya zaba maka Leila ne saboda kar kaje neman auren wata a wani gidan ace ba za a baka ba saboda yadda kake behaving, amman a gidansa yana da iko da Leila”

Talba ya cika ma bakinsa iska ya busar.

“Ina Momy?”

“Tana dakinta…”

Amal ta karasa tana kallon Kabir daya doso inda suke zaune ta kofar gaba, kana ganinsa ka san a fusace yake.

“Look Talba, ba zaka Leila kuka saboda bakin halinka and now ka saka Momy kuka ba okay? I won’t tolerate this, dole ne sai ka auri Leila ne? Idan ba ka canja hali ba ba zaka taba aure ba a rayuwarka”

Daga inda yake zaune ya dago yana yi ma Kabir wani banzan kallo.

“Ka sani ba a amin tsawa ba a nuna ni da yatsa”

“To sannu ubana, sannu Sarkin Arewa, girman kai zai kashe Mtssssssssss”

Kabir ya karasa yana jan wani dogon tsaki. Amal ta yi saurin kama hannun Talba.

“Ya taso mu bar mishi gurin gaba daya”

Uffan Talba be sake cewa ba ya bi Amal dake rike da hannunsa, har sai da suka shigo cikin falon sannan ya saki hannunta.

“Je dakinki zan yi magana da Daddy”

“To amman karka ce masa ni na maka gulmar”

Yayi murmushi ya juya zuwa bangaren Daddy. Daman can duk wata gulmar gidan gurin Amal ake jinta. Cikin natsuwa da kamala ya shiga bangaren Daddy, yai sallama Daddy ya amsa masa tare da kai hannu ya dauki remote ya kashe plasma dake kunne. Talba ya zauna kasa kusa da kafafuwan Daddy.

“Daddy yau na kawo maka karar kanka”

Daddy yayi murmushi.

“Na taba Momy ko?”

“Eh Daddy ka san bana son hawayen Momy”

“To ai laifinta ne, taya Leila zata yi laifi na yi mata fada kuma tace zata shigar mata”

“Amman Daddy Momy tana kare Leila ne kamar yadda kake min, kuma tun da har Momy ta shigar mata na yarda ni ne ba ni da gaskiya, domin Momy kullum tana side dina ne”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“I will try my best na ga na zama Romantic, zan zama yadda Leila take so indai hakan zai faranta ran kowa, yanzu abu daya nake so Daddy ka je ka bawa Momy hakuri?”

Daddy ya nuna shi da yatsa.

“Hey i talk to your mom na mata fada, kuma ita ya kamata ta ba ni hakuri saboda rai na ya bace”

“Amman Daddy ai kai kayi mata laifi”

“Really? Kasan da wannan amman idan kai ma Leila laifi sai ka sa bata hakuri”

Talba yayi murmushi.

“Daddy wacan yana da banbanci da wannan, ita Leila ai yarinya ce, wannan kuma ba zaka iya da yayanta ba, yaranta ba za su yarda kai mata haka ba”

“Leila ma wata rana uwar wasu ce, kuma yaranta ba za su dauki abun da kake mata ba, kamar yadda a yanzu kake jin rashin dadi, and tell me, you take your Mom side”

Talba ya sake yin murmushi.

“No Daddy kullum ai ina side dinka, amman dai ina son Momy ta daina bacin rai please”

“Shikenan zan kirata ta zo nan na bata hakuri”

“No Daddy ka tafi dakinta mana, zata fi daukar abun da muhimmanci Please”

Daddy ya masa kallon mamaki.

“So that’s mean kasan yadda ake lallaba mace, duk abun da kake yi da gangan kake yi kenan?”

Talba ya mike tsaye yana dariya kamar ba shi ba, Daddy ma murmushi yai mai sauti yana binsa da kallo cike da kauna irin ta Uba da D’a.
Bangaren Momy ya dawo, kai tsaye ya nufo dakin Leila, be tsaya knocking ba ya tura kawai ya shiga, sai ya same ta zauna gaban mirror tana duba fuskarka. Tsaye yai cak kamar an dasa shi, ta ina zai fara? Me zai ce mata? Sorry? Shi da kansa? Yace mata sorry? After ta kira shi wani? Taya ma zai ce mata haka? For the sake of Daddy, wata zuciyar ta raya masa, but duk da haka be jin zai iya ce mata sorry.

“Idan wani abu ya faru a tsakaninmu, ki bar shi a tsakaninmu ba zai wani ya ji ba”

Ya fada sannan ya juya, sai kuma ya juyo.

“And if you need something, lemme know”

Yana fadar hakan ya juya ya fice ba tare da ya rufe mata kofar ba. Tabe baki tai ta mike tsaye ta isa gurin kofar ta rufe ta juyo ta dawo gaban madubin ta zauna. Har ga Allah tana son Talba, kuma ta san yana sonta amman abun da yake mata is yayi yawa, girman kansa da jin kansa yayi yawa, that’s why dazun ta fadawa Daddy cewar bata shirya aurensa a yanzu ba sai nan gaba, Momy kuma ta goya mata baya ganin kullum ita ake kwaruwa, but this time around Momy ta goyi bayanta.
Jin wayarta ta yi kara alamar sako yasa ta mike tsaye ta isa gurin da wayar take ta dauka ta duba sakon.

“Good Night”

Shine rubuce da number Talba, ba shiri ta zauna tana mamaki. Da gaske shi ne ya turo mata sakon ko wani dai? Dan murmushi.

“Duk sai na rama abun da kai min, it’s my turn”

Ta fada tana jin wani irin dadi, juya ido tai.

“Ya kamata ya san ina da tsada”

Ta fada sannan ta kwanta saman gadon.

         ***   ***   ***

Kamar jiya Saturday, yau kuma Sunday, kowa yana zaune a teburin cin abinci ban da Daddy da zai karya bangarensa da kuma Leila da take dakinta.

“Ina Leila?”

Talba ya tambaya yana kallon Amal.

“Tace zai ba zata fito ba”

“Why?”

“Just”

“Hada nata breakfast din na kai mata dakinta”

Ba Momy da Kabir ba, ko Amal har Baaba mai aikinsu sai da ta kalleshi.

“Kamar dai ba kai Talba”

Kabir ya fada, sai Talba yayi murmushi kadan.

“Sounds funny, right?”

“No sounds new”

Momy ta yi murmushi.

“Ban fada muku ba? Wata rana Talba zai canja”

Ya mike tsaye ya shiga hada ma Leila nata abun karyawa.

“I didn’t change, ina yi ne for the sake of you and Daddy”

“So na dan ra’ayin kanka kake ba, kenan baka farinciki da abun da kake, doesn’t make sense”

Kabir ya fada yana tabe baki. Talba dai be sake ce masa komai ba har ya cirewa Leila komai ya dauka ya nufi upstairs. Amal ta mike da sauri ta bi bayansa ta rigashi karasawa gurin kofar ta bude masa saboda hannayensa duka biyu suna dauke da abu ne. Yana shiga Amal ya janyo kofar ta rufe, har gefen gadonta ya aje mata komai sannan ya dago ya kalleta.

“Good Morning”

Ya sake gaisheta duk da kasancewar ya aika mata da sakon gaisuwa da safe kuma bata masa reply ba, which is pain her. Bata amsa masa ba sai kallonsa take.

“Ga breakfast dinki, idan kina bukatar wani abu ki fada min”

Yana fadar hakan ya juya, sai da ya kusa isa kofa sannan ta ce.

“Anjima zaka kai ni shopping”

“Idan kin shirya ki kirani”

Ya fada ba tare da juyo ba, sannan ya fice ya ja mata kofar. Yana saukowa downstairs be koma dinning din ba sai ya nufi kofar fita, yana fitowa ya tsaya bakin kofar falon ya kira Ali. Kamin Ali yai picking Kabir ya fito ya tsaya daidai inda yake tsaye.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button