NOVELSUncategorized

A GIDANA 8

Haske Writers Association馃挕

Shafi na takwas

*********

  Bude kofar tai sannan ta shiga cikin inda ake editing.

 Suna ganinta kowa ya zauna daidai, tare da maida hankali kan aikinsa.


 Fitowa tai ta bude cikin news room suma gyare gyare sukeyi tana gamawa ta fito, da niyyar wucewa dan ta shirya saboda program dinta.

 Tana shiga taga Ramla a zaune tana waya.
 Sam bata kula tana bayanta ba sai da Zainab ta karasa gun, Ramla na juyowa sukai ido hudu da Zainab da sauri ta mike daga gun da sauri tare da cewa “Good Morr..”

 Kallan da Zainab ta mata ne yasa ta yin shiru, sannan tace “ba laifi dan dama irinku kallo daya mutum dai muku ya fahimta.”

 Ramla cikin mamaki tace “ya fahimci me?”

 Zainab ta mata alama da kai akan ta fita, Ramla idanunta suka ciciko, ta bude baki zatai magana聽 Zainab ta kalleta wanda hakan yasata yin shiru, hawaye ne suka zubo mata tasa hannunta share sannan ta fita.

 Tana rufe kofa Zainab ta dan sauke numfashi kadan cikin takaici, sannan ta wuce ciki.

 Ramla kam fitowa tai cikin station din tana dan hawayenta.

 Kusa da wata mota ta tsaya ta share hawayenta sannan ta dau waya, bata dade da dialing ba aka daga, daga can ta fashe da kuka tana cewa “Yallabai…..kawai tasa kuka.

 Daga cikin mota Khalid dake zaune yana waya da Abbansa ya kalli jikin windown.

Sallama sukai ya kashe tare da rufe idanunsa, kuka ta cigaba dayi tana cewa “Nikam matarnan ta tsaneni wlh, yaufa saura kadan ta kirani karuwa…”

 Ta kara sa kuka, haushi ya kama Khalid ya kalli jikin window din gashi ta tsaya jikin kofar ba dama ya fita.

Ta cigaba “ni dai Allah bata sona, wai tsoran Zainab din kake?”

 Can kuma ta kara sa kuka, sannan ta kashe wayar, tana kashewa ta kalli madubin jikin motar dan gyara fuskarta.

 Kallanta taga anayi, idanunta zato da sauri sannan ta sa hannu dan bude motar, Khalid ya bude motar sannan ya kalleta.

 Sai yanzu ta kalli jikin mottt are da take, gabanta ne ya fadi dan tasan motar Zainab, idanunta ne suka fifito ta kalleshi sannan ta danyi yake tace “ashe da mutum a ciki.”

 Khalid ya fito ya rufe motar yana neman tafiya.

 Da sauri tace “kaji me nace?”

 Kallanta yai sannan yace “daga ina?”

 Ta dan motsa baki sannan tace “kaji daga farko har karshe kenan?”

 Juyawa yai bai amsa ba, tai saurin cewa “dan Allah kayi hakuri karka fadawa Assistant director Zainab.”

 Ta ina zan fada mata? Abinda yake tunani kenan, da sauri tace “dan Allah, karka fada mata.”

 Juyowa yai ya kalleta, mota ta nuna mai tace “ba motarta bace?”

 Sai yanzu ya gane, juyawa kawai yai ya wuce, dan wata irin yunwa yakeji, Ramla ta saki ajiyar zuciya tace “shikenan na gama yawo, you are fired.”

**********

聽 Adam ne yai shiru a falo, Goggo nata waya tana ma mai dinki bayani akan dinkinta, Nabila da Nusaiba na gefe suna dane dane a waya, wata nannauyan ajiyar zuciya yai wanda Goggo tana waya tadan kalleshi, mikewa yai ya fita, bai dade sosai ba sai gashi ya dawo.

 Goggo ta kalleshi tace “ina kaje?”

 Kallanta yai yace “Goggo!”
Ta kalleshi ya mata nuni da daki.

Mikewa tai ta fito suka nufi daki, tana shiga tace “menene?”

 Kallanta yai tare da zama yace “Goggo yarinyar can na bukatar taimako” kallansa tai tace “wace yarinya kenan?”

 Labari ya bata na yarinyar sannan yace “Zainab bazata taba bari a taimaketa ba.”

 Goggo tace “ka sani kazo kana fada? Kai ba ka saki jiki komai sai dai a maka ba.”

 Yace “wai Goggo ba a dalilina kikejin dadin nan ba? Meyasa komai nazo miki dashi sai ki dinga fadamin magana?”

 Goggo tace “to ya kake so ayi? Kafi kowa sanin Zainab, ko kawarta ka taba gani a gidan nan? Daga ita sai kanenta sai ni? Sai dai in kanwa ce dakai amma inba haka ba wa ka isa kawowa gidan nan?”

Shiru yai kafin ya kalleta da sauri yace “Goggo!”

 Kallansa tai yace “in mukace mata Sadiya ce fa?”

 Cikin mamaki ta kalleshi tace “mene?”

 Yace “in muka dan kawota akan Sadiya ce in tai kwana biyu sai mu sallameta, bayan ta gama cike abin makarantarta.”

 Goggo ta saki baki tana kallansa tace “ne kake cewa?”

 Kallanta yai yace “Goggo bakiganta ba haryanzu fa tana waje, abin tausayi.”

 “Ni wai yaushe ma ka fara tausayi ne? Sannan a ina ka santa balle kasan halinta? In aljana ce fa?”

 Wata dariya ya saki yace “wani irin zance kike.”

 Tace “lalai Adam bakada hankali wasa wasa, kanwarka? To in abu ya tashi Sadiya tazo daga kura fa?”

 Yace “lokacin sai musan me zamuce kuma hali ma irin na Zainab ganewa zatai.”

 Kallansa tai galala kafin tace “ka samu matsala wlh, kuma ni ba ruwana, in da raban garin taimako……”

 “Haba Goggo meyasa kike haka ne? Taimako na kwana daya zuwa biyu sai ya zama haka?”

 Tace “ni wai yaushe ka zama mai taimako ne?sannan taya zaka shigo da ita?”

 Shiru yai kafin can yace “dama yanzu nake tunanin in shigo da ita a boye inyaso intai wanka sai…..”.

 Shiru yai dan kansa ya kulle, Goggo tace “sai me? Sai na bata kayana tasa?”
 Tai maganar cikin gatse, da sauri yace “eh sai ki bata ta saka yanda inta dawo sai nace mata ga Sadiya tazoyin kwana biyu, a yanda take dawowa a gajiye ma ina zata ganeta? Sannan gobe kinga da safe zata sake fita, kinga tana gamawa sai mu sallameta.”

 Kai zaka biya mata kudin makarantar? Tambayar da Goggo ta jefeshi da ita kenan, kallanta yai sanan yace “Goggo wai meyasa kike haka?”

 Tace “to wa zai biya mata? Zainab?”

 Yace “in taji Sadiya ce ai zata taimaka.”

 Goggo ta mike tace “can kai ka sani ba abinda ya dameni, nidai wlh kaja aka ganeka abu ya shafeni ranka ne zai baci.”

 Adam yai shiru yana kallanta.


聽 ************

聽 Zainab na zaune a office tanacin biscuit da juice, badai yana waje ba? Abinda ya fado mata kenan? Mikewa tai bayan ta gama hartayi hanyar waje sai kuma ta koma ta zauna tare da cewa “ai yau dole yaje ya dawo saboda zaman yayi yawa.

 Da wannan ta cigaba da aikinta, wajen sallar la’asar taga kiran Director, tana kallan wayar har sai da ta katse, sake kira akai ta kalli wayar sannan ta daga.

 Zainab!

 Tace “Yallabai ina wuni?”

 Daga can ya amsa yana cewa “ya aiki?”
 Tace “lfy.”

 “Ashe Ramla tayi laifi? Ayi hakuri kinsan yaran nan ne wlh sai a hankali.”

 Tace “saboda haka ka kira?”
Yace “no dama ina san fada miki ne wannan proposal din sunce gobe aje a musu presentation.”

 Tace “that’s nice, zan shirya power point.”

 Yace “yauwa, sai gobe.”

 Nan sukai sallama ta kalli wayar sannan ta girgiza ki.

 Sai karfe shida ta tashi? Ramla naganinta ta boye, Zainab ta wuce tana kiran Adam, duk da dai jikin ta na bata ya dawo.

 Motar ta gani a waje hakan yasa ta nufi gun.

 Ba kowa a ciki, hakan yasa ta dan wawaiga, daga gefe ta hangoshi ya nufo gun, da alama zama yai a gun.

  Bude motar yai, ta bude baya ta shiga.

 Shiga yai yaja suka fara tafiya.

 Shiru suka danyi a motar, tana kallan wayarta, can tace “badai a waje ka zauna ba ko?”

 Baiyi tunanin dashi take ba sai dayaji shiru alamar ba waya take ba sannan yace “cafe naje.”

 Shiru sukai ba wanda ya sake magana har suka kusa isa, daurewa tai tace “gobe daga gun aiki zamu fita zuwa kaduna, in na shiga gun aiki 1hr zanyi a ciki sai mu wuce.”

 Okay kawai yace suka karasa ciki……

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button