NOVELSUncategorized

A GIDANA 9

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Tara
Harta bude kofa zata fita tadan juyo, kallansa tai tace ” yanzu zaka wuce?”


 Yanzu kam ya juyo yadan kalleta kadan yace “eh zan wuce danbatta ne.”

 Danbatta?
 Ta fada cikin mamaki, juya kansa yai yace “eh.”

 Fitowa tai batace komai ba, tana neman bude kofa taga an bude da sauri, Nusaiba? Ta fada tana kallanta.

 Sam batama kula da ita ba ta wuce gun Khalid da gudu? Yana rataya jakarsa a baya taje kusa dashi tace “Ina wuni?”

 Khalid ya kalleta murmushi yai sannan yace “ya gida?”

 Tace lfy kalau, ga wannan.
 Ta mika mai coke mai sanyi tace ga wannan kasha rana.

 Kallanta yai sannan ya amsa, Zainab ta saki baki tana kallan ikon Allah sai jitai an rikota, juyawa tai ta kalli Adam wanda ya sa dariya yace “kwaro da alama kayi kasuwa.”

 Nusaiba ta rufe ido da sauri, ta juya ciki da gudu, har tafa dan bige Adam dake jikin kofar kadan.

 Adam ya kara sa dariya, Zainab ce taja hannunsa suka shiga ciki.
Khalid ya juya ya fita.

 Tasha ya wuce kawai ya hau mota ya tafi danbatta.

 Bayan magrib ya isa, dukansu na zaune a waje suna cin tuwo sukaji sallama, da gudu su Amir suka tashi suka nufeshi suna cewa Yaya yaya

 Khalid ya rungumesu sannan ya shigo ciki, Umma da Abba sunyi zuru suna kallanshi.
Asiya kam mikewa tai ta dauko plate ta ajiye, Khalid ya kalleta yace “yauwa kanwata nagode.”

 Umma ya gaida sannan ya gaida Abba ya tambayi jikinsa.

 Abba ya kalleshi yace “meke faruwa?”

 Khalid yace “kawai ina tashi naji gida nake so.”

 Asiya tasa dariya tace “sai kace dan boarding yaya.”

 Yace “dama inasan kaiki boarding da alama na kusa.”

 Dariya tai tace “boarding ina Ss2?”

Abba yace “ban gane ba? Yanzu kana tashi kawai ka taho?”

 Yace “eh Abba naga hakan yafi sauki, nawa ma tafiyr take daga kano zuwa danbatta?”

 Umma tace “to yanzu ci abinci kai sallah ka huta.”
Ta kalli Abba tace “tunda yaga hakan yafi sauki sai ka barshi, sanda yaga bazai iya ba sai yaje can din.”

 Khalid yace “yauwa Umma.”

 Abba yai shiru bai kara cewa komai ba, Khalid ne ya zuge jakarsa ya ciro coke din nan yace “ga coke Abba.”

 Abba ya amsa yana cewa “to nagode.”

 Nan suka ci abinci, suna gamawa ya mike ya shiga daki.


*********

 Fitarsa Sallar isha’i ya hangota a inda ya barta, meke damun yarinyar nan? Wai ba mutanene a unguwar da ba wanda zai taimaka mata?

 Wucewa yazoyi tare da dauke kansa kamar bai ganta ba, ji yai ance “bawan Allah.”

 Gabansa ne ya fadi, ya juyo ya kalleta, tasowa tai daga inda take ta matso kusa dashi tace “ka taimakeni ka bani gun kwana dan Allah, jiya ruwan da akai tsakar dare a kaina ya kare, gashi ko ruwa ban samu nasha ba bare abinci.”

 Adam yai shiru yana kallanta, idanunta ya kalla duk ya jeme alamar wuya, yace “biyoni.”
 Nan tabi bayanshi da saurinta.

 Shiru yai a bakin kofa gabansa na duka uku uku, cewa yai tsaya anan sannan ya shiga ciki, mai gadi ya kalla yace “Bala duba min ban dakinku ko kunbar fanfo a kunne, naji karar ruwa.”

 Cikin mamaki Bala yace “fanfo?”

 Adam yace “eh duba.”

 Nan Bala yai hanyar bandaki, da sauri ya mata alama data shigo, ta shigo da sauri.

 Adam ya nuna mata wani daki a can gefe, ta nufeshi da sauri.

 Tana shiga Bala na fitowa yace “nikam banga komai ba.”

 Adam yace to kila ba nan gidan bane ya wuce.
Dakin ya shiga ya kunna fitila.

 Tana tsaye, dayake dakin ba komai sai katifa katuwa dake kasa.

 Adam ya kalleta yace “ki zauna anan zuwa dare zan ce ki shigo ciki.”

 Kallansa tai tace “zan iya zama? Karna ja wani abin ya faru.”
 Yace “karki damu zan kawomiki abinci, anjima zaki shiga ciki, ba dadi ne ban sanar asu ba su ganki.”

Tace “nagode Allah ya saka da alkairi.”
Fitowa yai ya wuce ciki.

 Zainab na zaune a falo, Goggo na kan kujera daga gefe suna kallan sautin arewa wato inda Zainab ke aiki, gefe kuma Nusaiba ce da Nabila.

 Zainab dake zaune tana cin abinci tna dan kallan tv din ta kalli Nusaiba tace “Wato harda daumin coke kiyi gwaninta dashi?”

 Nabila tace “to da Aunty bakisan meta kinkimo zata kaimai ba.”

 Zainab tace me?

 Abinci ta zuba a flask, ta sa coke tasa robar ruwa tasa apple a basket wai zata kaimai yai lunch.

 Zainab batasan sanda tai dariy ba tace “sannu matarsa.”

 Nusaiba tace “Aunty dan Allah ku auramin shi.”

 Goggo tasa dariya tace “yaro yaro ne, wato wannan zamani ba kunya, wai yarinya ke cewa a mata aure.”

 Nusaiba zatai magana Adam ya shigo yana cewa “in kina sanshi tsaf zan aura miki shi.”

 Da sauri tace haba?

 Zainab ta dan harareshi tace “karka tunzurata batasan gatse ba.”

 Tana gama cin abinci ta wuce daki, tana mikewa Goggo tasa cassette, Nabila tace “mu dai Goggo ki bari mu gama kallan shirin da ake.”

 Adam yai saurin mika ma Nabila remote yace “sa abinda kikeso.”

 Goggo ta kalleshi fuska a hade, yace “Goggo magana zamuyi.” Yai maganar cikin rada.

 Mikewa tai ta nufi daki, Nabila na cewa “Goggo fushi kikai?”

 Adam yace “bari naje naji.”

 Nan yai ciki, suna shiga ya zauna kusa da ita yace “Goggo ya zanyi yrinyar tana dakin wajen can.”

 Kallansa tai galala tace “mene?”

 Yace “baki ganta ba wlh duk ta rame.”

 Goggo tace “to meye damuwa ta?”

 “Wai Goggo meyasa kike min haka? Taimakon rai zamuyi, dan Allah ki taimaka ma yarinyar nan.

 Tace “naji amma kwana biyu, inta wuce kuma wlh duk abinda ya biyo baya kar ka sa dani.”

 Yace “ta ina ma zata wuce? Ai tana gamawa zan sallameta.”

 “Ynzu ya zakayi?”

 Yace “idan wadancan rigimanmun sun kwanta zan shigo da ita tai wanka ta kwanta a dakinki, kinga ita da sassafe take fita, to inta dawo sai ince mata tazo.”

 Goggo ta tabe baki tace “wato kwakwalwarka bata tashi yin banban tunani sai kanasan abu.”

 Dariya yai yace “Yanzu zan kawo abinci na ajiye anan dakin karda daddare a gane in aka kamani ina zuba abinci.”

Tace “can kai ka sani, nidai ka tabbatar randa zani bikin nan na yar kawata kai ka kaini a mota.”

 Yace “an gama Hajiya Goggo.”

Fitowa tai ta dawo falo, shikuma ya wuce daki.

 Zainab na ganinshi ta dan matsar da laptop din data kunna tana cewa “gobe kaduna zani.”

 Kaduna? Ya dada tare da zama kusa da ita, tace “eh wlh zamu presentation.”

 Ya kwantar da kansa akan cinyarta tasa hannunta acikin gashinsa tana cewa “ko zaka kaini?”

 Idanu yadan zaro, yace eyee, dariya tadanyi tace “just joking, harna fadawa abokinka.”

Sun danyi hira kafin ya fito falo, yana ganin yaran sun bar falo ya fita ya shigo da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba.

 Dakin Goggo yai da ita, sannan ya fita, Goggo na zaune a falo tana kallansa har suka wuce ciki, itadai sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan lamari, mikewa tai ta dau abincin da aka zuba tai daki.

 Tana zaune a kasa, jikinta duk yai datti, Goggo ta kalleta sannan ta nuna mata toilet da kayan da ta fito dashi, ta juya ta fita.

 Adam ya kalleta yace “kiyi wanka kici abinci ki kwanta mayi magana gobe.”

 Kai ta daga mai alamar to, sannan tace “nagode nagode….”

 Hawaye suka zubo mata.

Adam ya juya ya fita….

***********

 Tunda tai sallar asuba bata koma ba ta tsaya gyara slide din da zasuyi presenting.
 Karfe bakwai ta mike tai mikar gajiya sannan tai wanka ta shirya, Adam na kwance nata sharar baci.

 Kayanta ta kwasa ta fito, yana tsaye a waje sanda ta fito, murmushin da batasan dashi bane ya fito, tabbas tanasan mutum taga yasan aikinshi, lalai kasarmu tana cikin wani hali ace masu kwazo da san aiki sune wadanda basuda aikinyi.


Tana shiga yaja suka tafi, ba abinda wani yace a cikinsu har suka isa cikin station din, yana parking tace “yanzu zan fito.”

 Ba matsala

 Abinda yace kenan ya fita.

Ciki ta shiga, tana shiga ta daure fuska sosai, sunyi meeting dinsu sun gama, nan wadanda zaku rakata suka shiga tasu motar sukai gaba akan sai sun hadu acan, dan sun san bata yawo da mutane a motarta.

Zainab na fitowa taji karar text a wayarta, kallan wayar tai ta bude, Wlh Zainab sai naga karshenki, yadda kika koran daga aiki shekara biyu kenan na rasa wani aikin, ni zan zama ajalinki wlh

 Tana gama karantawa tai tsaki tare da wucewa ta shiga office dinta, printing dinsu tai sannan ta kara duduba komai ta fito waje.

 Mota ta shiga suka dau hanya.

 Tun da suka fara tafiya mota ke binsu a baya, Khalid ya kula da hakan sau dai da alama ita bata sani ba tana ta dube dube a tablet.

 Daurewa yai yace “tare muke da wadancan?”

 Juyawa tai ta kalli bayansu, sannan tace “a’a wadanda muke tare sun wucemu da kusan 20min.”

 Shiru yai yana kara kallan motar ta glass, kallansa tai tace “menene?”

 “Bin mu suke.”
Bin mu? Ta maimaita cikin tsoro, text din dazu ne ya fado mata.

 Kallanta yai ta glass yace “kinsan su waye?”

 Bakinta na rawa tace “a’a”

 Tunowa da mai kukan jiya yai, kai ya girgiza da sauri yana cewa may be hanyarce daya.

Jitai yace “bari muyi kamar zamu siya abu muga.”

 Tace to

Kusa da masu sai da kwan zabi suka tsaya nakan hanya, Khalid ya juya baya, gani yai motar ta tsaya a bayansu kadan, yanzu kam yasan tabbas binsu akeyi, kurawa motar ido yai, maza ne a cikinta kusan guda biyar.

 Kallanta yai itama kallansa take, yace “kin ma wasu laifi ne?”
Shiru tai hakan yasa yace “please ki fadamin insan ya zamuyi, ga meeting kina dashi ga wadanan, in muka tsaya biye musu zaki rasa abinda zaki je yi.”

 Wayarta ta ciro ta bude text din ta nuna mai, karantawa yai sannan yace “kinsan number?”

 Tace “a’a amma daga alamun text din cikin mutanen dana kora ne.”

 Baisan sanda yai wani murmushi ba.

 Fuska ta hade tace “meye?”

 Yace ” seat belt.”

 Sawa tai tana kallansa haryanzu so take taji murmushin rainin hankalincan na meye.”

 Ganin bashida niyyar magana yasa tace “tsoro kake?”

 Batare da ya juyo ba yace “me nayi da zan tsorata? Mai laifi ai shine da tsoro.”

 Yana kaiwa nan ya fizgi mota da gudu………

 (Ai nikam jinai motata ta makale, ashe gudu sukai suka barni a baya……)

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button