NOVELSUncategorized

SANADIN K’AWA 1


khaleesat Haiydar
1

Tashi tayi daga xaunen da take kan yar katifar dake dakin xata fita da wayarta a hannu, warce ke xaune gefenta ta yi hanxarin rikota tace “Don Allah meye haka Fatima, wlknci ma xa ki min don na xo gidanku” komawa fatimar tayi ta xauna tace “Toh naga haka kawai kina neman xubar mana da aji ne, kuma ni yanxu gun Ammi xan je tun daxu ta kirani
fah” kawartata ta hade tace “Kai Fatima ba wani xubar da aji, kema kin san don bani da waya ne ynxu, plss kiyi following dinsa ba don komai ba kawai don mu dinga ganin ko da hotuna ne plsss, ba fa magana xa ki dinga masa ba” Fatima ta wara ido tace “Anya kina da hankali kuwa Husnah, I can’t stoop my self that low inyi following dinsa, you knw I have class” Husnah ta karbe wayar tace “Toh me class naji ni xan yi following din nasa ba ke ba ai” Fatima xata kwace wayar tace “Noo, amma ai Fatima Muhd xai gani ba Husnah Usman ba” Tsaki Husnah ta ja tayi logging Instagram, bbu bata lkci ta yi following wanda take ta nacin su yi following, Fatima dake kallonta tace “Dubi Private account ne fa, Allah ya sa yyi accepting din naki ma tukun” Husnah ta fashe da dariya tace “Ka ji ta, ae dai Fatima xai gani ba Husnah ba” Fatima ta bude baki tace “Au haka ne ma koh? to wllh xan yi canceling yanxun nn” Da sauri Husnah ta boye wayar a bayanta tace “A’a kiyi hakuri plss” Fatima ta turo baki tace “Haka kawai yaje ya raina mu” Husnah tace “Ba xancen raini, xuwa anjima nasan xai yi accepting din request din”  Muryar Ammi mahaifiyar Fatima suka ji ta na kwalo mata kira, Fatima ta mike da sauri tace “Kin gani koh…..” fita tayi tsakar gidan Ammi dake tsaye ta gama shanya wankin da tayi tace “Ni xan daura ma yara girki kafin su dawo makaranta kenan” Ta tsuke fuska tace “Ammi wai da fita fa xa mu yi da Husnah tun daxu kuma na gaya maki” Ammi tace “Toh ki fita” daga haka ta koma dakinta, juyawa tayi kamar xata yi kuka ta koma dakinsu, Husnah tace “Wai me?” “Kinji wai in daura ma su Ummi girki, ko wa xai dinga masu idan na bar gidan” Husnah ta kyabe baki tace “Ae sai hakuri nima haka inna ke takura ni a gida wllh, sai naji dama bamu gama secondary ba” Fatima tace “Wllh kuwa ni xaman gidan nn gaba daya ya isheni ma” Husnah ta yi dariya tace “Toh kice Umar ya turo kawai mu sha biki” Fatima ta yatsine fuska tace “Ke ni fa Umar din nn haushi yake ban yanxu, duk naji ma ni na tsane sa” Husnah ta xaro ido tace “Saboda me?” Fatima ta gyara xama tace “Kinga saurayin Sa’adatu kuwa, kinga irin motar da yake xuwa gunta da shi da daddare, hmm baxa ki gane ba, yanxu ba kayanta ba, har takunta ya canxa wllh, i can’t deny envying her, shi yasa ynxu ko magana ma bana mata wllh, ko ta min yi nake kamar ban ji ta ba” Husnah ta yi tagumi tace “Nima wllh ynxu Sa’ad haushi yake ban, ko ya xo bana fita, tun daga farkon layi wnn shegen mashin din nasa da ya rube yake announcing present dinsa, am just bored of him wllh” Dariya sosai Fatima take yi tace “To ba gwara ke yana da mashin din ba, Umar me xuwa min da kafa fa?” Husnah tace “To ba shi yasa nake son mu ma mu faso gari ba, yanxu ace Elbasheer din nan yayi accepting dinmu mu d’an fara masa magana kin ga ai wataran mu ma dawowa kamar Sa’adatu xa mu yi”  Fatima ta yi shiru bata ce komai ba, Husnah tace “Allah kuwa Fatima ki duba ki ga” Fatima ta tabe baki tace “Allah yasa ya ma yi accepting din ma dai” Husnah tace “In sha Allah xai yi, idan kinga yyi don Allah ki daure ki d’an ajiye jan ajin nn ki masa sallama” dariya kawai fatima tayi, sai kusan karfe biyu suka fito dakin, ta tarar har Ammi ta kunna coal ta daura sanwan, Tace “Lah Ammi wllh ban ce baxan yi ba” ko kallonta Ammi bata yi, Husnah tayi kasa da murya tace “Toh ba sai kin raka ni ba kar laifin yyi yawa sai mun hadu….” daga haka ta nufi soro tana kallon Ammi tace “Ammi sai gobe xan wuce” ba tare da Ammi ta kalleta ba tace “Toh ki gaida mutan gidan” Husnah tace “Xa su ji” daga haka ta fita, Fatima ta karasa tace “Ammi kiyi hakuri ni ban ce fa baxan yi ba” Ammi tace “Wannan kuma ya rage naki Amira, in dai irin kawayen da xa ki dinga ajiyewa kenan wllh kina tare da wahala, kuma ki bace min da ganin kada raina ya sake baci” Fatima bata ce komai ba ta koma daki tana turo baki. Jin ring din wayarta a karo na kusan uku Ammi dake xaune tabarma suna cin abinci da yaranta biyu tace “Wai Amira ba kiran wayar ki ake yi ba” Fatima dake xaune kan nata tabarmar daga bakin kofar dakinsu da kwanon abincin ta a gaba tace “Ehh Ammi ni baxan iya fita ba ne” Ammi tace “Wa ke kiran ki?” Ta hade rai duk da ba ganinta


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Ammi take ba saboda duhun tsakar gidan tace “Umar ne” Ammi tace “Shine baxa ki fita ba?” Tace “Ni na gaji Ammi duk kaina ma ciwo yake min shi yasa baxan ma daga ba” Ammi tace “Toh yyi kyau” bata sake ce mata komai ba, Fatima ta gama cin abinda xata ci a abincin ta mike ta shige daki, ta gyara gun kwanciyarta ta kwanta duk ta kagu Ammi ta shiga ciki ta aiki kanwarta ta siyo mata kati don tun daxu da rana sub dinta ya kare, wani littafin hausa ta dauka tana karantawa har kaninta suka shigo dakin, mikewa tayi ta bude jakar kayanta ta fiddo dubu dayan da Umar ya bata da ya xo shekaranjiya tace “Ummi kati xa ki xubo min na dubu daya” Ummi tace “Na dubu daya fa kika ce” Fatima tace “Ba Sajjad idan baxa ki ba malama” fita Ummi tayi dakin ba tare da tace komai ba ba a jima ba ta dawo mata da katin, Tana gama loading dinsa ta yi sub ta bude data, bbu bata lkci WhatsApp messages dinta suka soma shigowa sannan Instagram, bata yi concentrating kan na WhatsApp din ba ta bude IG kawai, tsuru tayi ta na kallon sakon dake nuna mata Elbasheer yyi accepting follow request dinta sai dai bai yi following dinta back ba, ta hade rai sosai, fita tayi a gun nan idonta ya sauka kan hotonsa da yyi uploading 3 days back with more then 6k likes, tsaye yake jikin mota ya Rungume hannayensa ga wani makeken gida dake gefensa kamar a turai, flowers masu kyau ne xagaye gidan ga motoci kusan biyar tana hangowa, he is an epitome of true handsomeness, don yyi kyau har ya gaji a milk geznar dake jikinsa yana kyalli, dogo ne shi ba na wasa ba, don irinsu ake kira da gentlemen, yana da haske amma ba sosai can ba, ga dogon hancinsa da manyan idanuwansa da ya kara fito da ainahin kyawunsa,  ta kalli bakinsa me xagaye da millionaires belt ga sajensa dake kwance, lkci daya jikinta yyi sanyi, kawai Husnah so take su yaudari kansu, me wannan handsome din d’an masu kudi xai yi da su ‘ya yan talakawa, ta sauke ajiyar xuciya a hankali ta shiga duba duk hotunansa, kasa ci gaba da kallonsu tayi don gani take xata iya suman kwance, irin wnn kyan da Allah yyi masa haka, cike da courage ta shiga DM dinsa ta tura masa da sallama complete without short cut, yatsine fuska tayi tayi log out, ta koma WhatsApp, tayi replying chats dinta sannan ta kashe data, tunani ta dinga yi na wannan bawan Allah, duk taji ai fa ita gaba daya duniya ta tsani Umar har ranta, daga haka bacci ya dauketa, da asuba da mafarken Elbasheer ta farka kamar ynda ta kwanta da tunaninsa, ta tada kanninta su yi sallah, ita kuma da bata sallahn wanka tayi ta wanke baki ta kintsa kanta ta dawo ta kwanta daki ta jawo wayarta ta kunna data, bata ga alamar ya ga message din nata ba ta mayar da wayar a sanyaye, har karfe sha biyun rana bata da wani kuxari, ta kasa daina tunanin Elbasheer, kunun da Umma ta dama masu ma daxu da safe kadan ta sha, duk bayan wani lkci xata bude data ko xata ga message dinsa amma shiru ko bude msg din bai yi ba har lkcn, sake tura masa Hi tayi ta kashe data, tana xaune bakin coal pot amma bata san shinkafa da waken da take dafawa har ya fara konewa ba, kawai jin tsawar da Ammi tayi mata tayi, ta dawo duniyar tunanin da ta tafi a firgice, Ammi tace “Uwar me kike tunani kike konar min da abinci kan wuta?” Da sauri ta dau tsumma ta sauke abincin tace “Kiyi hakuri Ammi bacci na fara yi” wani mugun kallo Ammi ke mata, ta mike kan kujerar da take ta shiga d’an ginin dake tsakar gidan a matsayin kitchen ta fiddo karamar tukunya ta fito ta shiga dakin Ammi ta dau jarkan mai ta xuba tukunya ta daura man kan wuta ta yanka albasa, yana soyuwa ta sauke ta xubda gawayin ta xuba ruwa ya mutu ta wuce ciki bayan ta juye shinkafa da waken a cooler ta kai dakin Ammi, sannan ta fito ta wuce daki da sauri jin wayarta na ruri, hararan wayar tayi ganin Umar ne don a ranan ya kirata yyi sau hudu tayi silencing wayar tayi Kwanciyarta lkci daya bacci ya dauketa, Sai kusan la’asar ta tashi shi ma kaninta dake shirin islamiyya ne suka tadata da 6uruntunsa, ta ja tsaki ta dau wayarta ta fita tsakar gida, Ammi dake kulla kayan sana’arta na kubewa da Kuka tace “Ke kin yaye xuwa islamiyyar ma ynxu ko Amira, baki da aiki sai bacci da danne dannen waya sai kuma kawayen dake xuwa maki kin mayar da su uwarki da ubanki, kina xaton ni kike ma koh, ae Umar ni ya cuta da ya siya maki wannan shegiyar wayar dake neman kai ki ga halaka” kamar xata yi kuka tace “Ammi wai ni fa ba ko da yaushe nake rike wayar fa…” Tsawa Ammi tayi mata, ta mike hawaye cike idonta tace “Kuma ni na gaya maki malam suraj ya sa min ido a makarantar ne gwara kawai in dinga haddata a gida” daga haka ta shige daki ta kunna data, ga mamakinta taga Elbasheer yyi uploading hotunan wasu mata biyu masu kama da shi Wanda ga dukkan alama kaninsa ne don a caption din ma cewa yyi Blood, ta duba DM da tayi masa taga har lkcn bai bude ba, ranta yyi mugun baci, tayi saurin yi masa typn kamar haka “Toh sannu babba, irin kai wani din nan da baxaka iya replying din message din mutane ba koh, to ni ka san wacece ni da har xaka shareni bawai ka san abinda xan gaya maka ba, plss keep ur girman kai and ji da kai for your family meeting malam” ta hada da emojin jan fuska ta tura masa ta kashe data ta ajiye wayar ta fara shirin xuwa islamiyyar da Ammi tayi mata magana, bata tafiya da waya don haka daga ita sai jakar makarantar ta ta fita gidan bayan tayi ma Ammi sallama, sai kusan shidda da rabi suka dawo gida, ko uniform bata cire ba ta bude data, gabanta yyi mugun faduwa ganin message din Elbasheer.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button