JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 59

Kallon screen din wayar Jiddah tayi jin shirun yyi yawa, taga har sannan bai katse ba, ta d’an turo baki tace “Ina jin ka” Yace “Ohk… Ae ban san kina ji ba” mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, ganin Maimoon a xaune parlor ta tafi ta dungurar mata da wayarta ta juya ta koma daki… Umma ce xaune parlor tare da Maimoon, Jiddah kuma na xaune dinning area rike da littafi a hannunta tana dubawa, Umma na kallon

Maimoon tace “Ke a ina ku ka yi magana da shi kika san bashi da lafiya?” Maimoon tace “Ba muna chatting ba Umma, wani lokacin ma har video call muna yi” Umma ta kyabe baki tace “Toh Allah ya basa lafiya” Maimoon tace “Ameen, Umma har fa ya je asibiti yace min” Umma tace “Ikon Allah, kila change of weather ne, barin yanda ya dade bai fita waje ba, Allah ya basa lafiya” Maimoon tace “Dama nima

nace change of weather gashi he still have some months kafin ya dawo” Umma tace “To kuma wannan shirin gulman da ku ka tsiri yi da shi na meye?” Dariya Maimoon tayi har da kwanciya, tace “Toh ba ya ga ya tafi inda baxae dinga ganin mu ba Umma, gashi bashi da kowa a can, kinga yanxu da a kasar nan ne

bashi da lafiya ae da duk mun je duba sa har da abinci… To amma yanxu babu me kula da shi” Umma dai tayi dariya kawai, can tace “Dama yaje da matar tasa ne da sauki, to bai je ba, kuma ranan da Ummi tayi masa magana cewa yyi kawai bai da niyyar xuwa da ita ne but he is allowed to go with his wife”

Maimoon ta rike ha6a tace “Toh ba sonta yake ba Umma, don dai kawai baxai yiwu ya tafi da warce yake son bane amma ni nasan da ya tafi da ita” Umma tace “Wacece ita warce yake son?” Maimoon ta d’an rufe baki tace “Aa wai imagining kawai nake” Umma ta tabe baki tace “Haka yace maki baya son matar

tasa? Da baya sonta ai baxai aureta ba” Maimoon dai bata sake cewa komai ba sai murmushi take, Safiyya ta fito daga daki rike da wayar Maimoon dake ring ta mika mata sannan ta koma dakin, mikewa Maimoon tayi bayan ta saci kallon Umma ta wuce dakin da sauri, tsaye tayi bakin kofa dai dai nn wayar ya katse, tabe baki tayi sai gashi an sake kira ta daga ta kai kunne tare da sallama, cikin faram faram tace

“Lafiya lau wllh Engineer, amma kuma bata dawo ba har yau fa….” ta d’an yi shiru sai kuma ta kyabe baki tace “Toh gaskiya nima ban sani ba dai, amma babu rana kam, kasan nace maka ta bar nan sbda karatu, mu ma sai season season muke ganinta…” Da sauri tace “Toh ae ita ma matar Ya Ahmad din ba wayar

gareta ba ya fada cikin ruwa…” Ta d’an sosa kai tace “Toh ina jin dai nan da sati biyu ne xan je can gidan sbda kaga baxa mu je mu tarar ma yaya Ahmad a gidansa ba, amma dai idan naje din xan bata in sha Allah” Ta kara da cewa “Toh shkkn bye” katse wayar tayi ta juya xata fita Safiyya tace “Wacece bata

nan?” Maimoon ta juyo ta kalleta bata amsata ba ta fita dakin Safiyya ta bi ta da kallo… Tunda Maimoon ta fito Jiddah ke kallonta, Umma da ta bi ta da kallo tace “Waye ya kiraki don munafurci kika shiga daki Maimoon?” Maimoon ta sosa kai tana er dariya tace “Aa Umma kawata ce ta kirani tace akwai gist daxu ina aiki ban samu mun yi waya ba sai yanxu ta sake kira” Wani kallo Umma ta dinga yi mata ta wuce

kitchen da sauri tana dariya… Da daddare Jiddah na kwance amma ba bacci take ba, tana son yin baccin amma ta rasa abinda yasa ta kasa, sannan tana jin abu da ita kanta bata san meye ba ya tsaya mata a rai yana damunta, Maimoon ce ta shigo dakin bayan ta gama kallon da take a parlor, ajiye wayarta tayi gefen gado ta shiga bandaki, Jiddah ta bi ta da kallo, sae da taga ta kulle kofar bandakin sannan ta mike

xaune ta jawo wayar a hankali don bai shiga lock ba, call logs ta fara shiga ta d’an yi scrolling sae kuma ta fita da sauri ta shiga application din WhatsApp, second to the last chat din da ta ga an sa Yaya A… Ta shiga tana sake kallon kofar bandakin, dai dai nan taji an bude kofar saboda rudewa kawai ta kashe wayar tana kan What’sapp din ta mayar da sauri ta ajiye ta kwanta ta rufe ido, Maimoon ta fito ta dau

wayarta ta bude lock din, mamaki ne ya cikata tana kallon wayar ganin chat dinta da Abuturrab ne gaban screen din bayan ita ba kan WhatsApp take ba, ta kalli Jiddah da ta ki bude ido, kofa kawai ta nufa ta tafi parlor ta xauna kan kujera sannan ta fara kyalkyale dariya har da kyakyatawa, Safiyya tace “Meye haka??” Dariya kawai Maimoon take, Safiyya tayi tsaki ta mike ta wuce daki, Sae da Maimoon tayi

dariyar me isarta sannan ta tashi ta koma dakin, Jiddah dai ta rufe har kanta ko da Maimoon ta koma dakin. Da safe Jiddah taki amincewa su hada ido da Maimoon, Maimoon dai sai harkan gabanta take, karfe goma Umma da Safiyya suka fita xuwa kasuwa, Bayan fitarsu Maimoon ta shigo daki ta dinga jan

Jiddah da hira don sun gama aikinsu tun safe, tun Jiddah na kin tanka mata har dai ta sake, labarin wata kawarta da tayi aure mijin ke gallaza mata Maimoon ke yi mata, Jiddah tace “uHum! To ko dai ita ma akwai abinda take masa ne kawai fada maku ne baxa tayi ba” Maimoon ta takarkare tace “Aa wllh, babu wani abu da take masa, d’an iska ne kawai ta aura, ke kinga soyayya kamar xa su cinye kansu kafin ayi

auren?? Wllh soyayya kamar indiyawa har suna intimidating dinmu, to yau dai ga shi sun koma enemies din juna, abun da mamaki” Jiddah tace “Ke dai kawai kiyi shiru tunda ba a gidan nasu kike ba balle kiyi siding dinta, ba dole sai ta fada maku gaskiya ba” Maimoon tace “Ji wani magana da kike, to ke duk xamanki gidan yaya Aliyu kullum ne yake kula da kin ci abinci ko baki ci ba? Ba wahala ya dinga baki ba

duk kika rame kika kanjale har kika gwammace bai dauko ki daga gidanku ba” Kallonta kawai Jiddah ke yi, sai kuma ta dauke kai tace “Aa ni bai ta6a bani wahala ko ya bar ni da yunwa ba, in ji waye yace maku haka…” Maimoon tace “Aa fa xancen gaskiya muke yi a nan Jiddah kar ki wani rufa masa asiri, kuma

kinsan a yanda take bamu labarin mijin nan nata wllh kamar halinsu daya da Yaya Aliyu, ai ke kin xauna gidansa kinsan wanene shi” Jiddah dake kallonta tace “Wani irin hali ne irin nasa?” Maimoon ta gyara xama tace “Kin ga Zainab bata da wani freedom tun da ta shiga gidan nan, sannan kullum a hantare take wajensa, gashi babu wani kulawa, ga masifa ga fada, ga yunwa, ga shi yayi ta depriving dinta of so many

things, to mention but a few…” Katse ta Jiddah tayi tace “Aa ni dai ban tuna sanda ya hantareni ba, sannan ni yana kula da ni… freedom kuma dama xaka auri mace ne ka saketa tayi ta yawo a gari? Sannan ni dai ban ta6a xama da yunwa a gidansa ba, and he never deprived me of anything all through

my stay in his house, in dai Aliyun da na sani kike magana a kai to ba halinsu daya da mijin kawarki ba” Maimoon ta rike ha6a tace “Ohh har kin manta duk abinda kika yi facing lokacin kina gidansa kenan Jiddah?” Jiddah tace “Ban yi facing komai ba, ni dai nasan ko baya nan nace ga abinda xan ci yana kawo

min, ba fa wai sae yana within kaduna ba, A’a ko daga kano ne yana kawo min, sannan xan iya kirga sau nawa nayi girki a gidan sa, kullum sai yayi min take away din abinci ko xan ci ko baxan ci ba” Maimoon tace “Tabb da gaske haka yake da caring? Ni wllh irin mijin da nake so kenan” Sau daya Jiddah ta kalleta

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button