NOVELSUncategorized

NIDA AMARYATA 9-10

9-10..
      “Lah mama kune,Bari In sakko,dama abinda yasa nahau sama,saboda bana son su ummi suzo su sameni suce saina sammusu,Dan dama guda Daya ya ragemin sai agwaluma biyu,Bari in sauko na sammuku,ku kwakuli kwallo,tunda ki biyu ne saiku ciri biyu,in Kuma Nan zaku hawo Bari in Nuna muku ta inda nahau saiku hau”…..

  ” Ikon Allah! Cewar Aunty munnira,wannan ce tunkiyar taki?kice ‘yar raino aka kawo miki,to ai wannan sallamar ta bazaiyi wuya ba,dan haka Kara kwantar da hankalinki”.daga kanta tayi sama tare da kallon Nihila tace,” Kinga mun gode da kyautar ki sakko kinji,kada ki fado kinji”.

Da to ta amsa kafin ta Kama kokawar sakkowa,harta samu ta sakko din,sannan ta Mika  musu agwalumar tace “gashi mama ki gutsura”.

“Ah ah nagode Sha abarki” 

“Kinwa kanki, to ke dayar maman gutsuri in Zaki Sha”

Ita dinma Aunty munnira cewa tayi ta gode.”Shikenan tunda kunki sha,nidai Zan fadawa Aunty Hama ban muku rowa ba,Kar ta ce banji abinda ta fadamin ba.

Kallon juna sukayi suka saki murmushi, sannan Aunty munnira tace,”Kinga basai kin fada mata ba,ai mu mun San Baki mana rowa ba”

“To shikenan ku zauna na kawo muku ruwa”

“Ah ah shima barshi kawai zauna kici gaba da hutawa,mu Kinga tafiya ma zamuyi,Ina angon naki? Ko ya fita ne?”

“Ah ah Yana can Yana bacci,ta fada tana rufe fuska da hannu Wai ita kunya”.

“To inya tashi ki gaisheshi”

“Tam zaiji” 

Haka suka juya suka fita,suna fita munnira tace,”lallai Yaya wannan badan yarinta ba da sai ince sai munyi da gaske akanta,Kinga kyau kuwa? Wlh ni nama dauka aljana ce dafarko”.

“Hmmmm wallahi Nima hakan,yanzu dai meye mafita?”

“Ai mafita guda Daya ce kawai mu barta mugani zuwa wani lokaci”.


“To shikenan,Amma fa Naga wadannan da nasu shirin,domin iya kwana Daya kawai sun wafci miliyan Daya Ina zaune”.

“Kinga barsu su yagi rabonsu su Kara gaba,Dan dama kin San duk masu auren nasa bazai wuce Dan hakan bane,ke din dai kin Zama turmin tsakar gida Sha lugude”.

Haka dai sukaci gaba da maganga nunsu,har ta rakata farfajiyar gidan,inda ta ajiye motarta ta Nan ta shiga ta tafi.

***

Shi kuwa Alhaji Yana farkawa yaji ciwon kan yayi Masa sauki Dan haka ya mike yaje yayi wanka,ya dauro alwala ya fito,anan yayi sallah Dan bazai iya fita da wannan kumburarren bakin Nasa ba,wayoyinsa ma kashewa yayi Dan karsu Alhaji Kabir su dameshi,Sam ya rasa inda zaisa kansa,dole ya nemi mafita tun wuri,Dan Nihila matar gwadawa sa’a ce,dole ya nemi yadda zai bullowa lamarin.Waya ya dauka ya Kira Hajiya yace ta kawo Masa Abincin sa Nan sama Dan bazai sakko ba.

***


Kwance take saman gadon Tasha kwalliyarta Mai daukar hankali,Sam takasa bacci,motsi kadan saita kalli agogo,ganin har Sha biyu ta kusa gashi ta Fara Jin bacci,yasa ta mike ta cire kayan jikinta tasa na bacci,cike da takaicin hallayar mijinta,Wanda dawowar dare ta zame Masa tamkar ibada,bisa gadonta ta kwanta cike da tunani,kwanciyar yarinyar ta ta gyara sannan itama ta kwanta,cikin bacci taji dawowar sa yana tashinta,cikin bacci kamar ko yaushe ta tashi tana mishi sannu da zuwa,amsawa yayi tare da tube kayanshi ya shiga wanka,ita kuwa sai kawai ta mike ta nufi kitchen Dan zuba Masa abinci.

Saida ta tabbatar ta zuba komai yanda ya dace,tana niyyar barin falon ya fito sanye da jallabiya,Zama yayi yafara kokarin cin abincin sannan ya umarceta data zo ta kunna Masa kallo.Haka kuwa akayi tana kunna Masa ta juya ta shige daki batare data ce Masa ko kala ba,shima din Bai wani damu da shurun nata ba Dan kallon ne agabansa.

Sam bazata ce ga iya adadin lokacin Daya dauka ba kafin ya shigo,Dan har tayi bacci.Takaici ne ya cikata kamar ko yaushe,ganin tanata tashinshi da asuba Amma Sam yaki ya tashi yayi sallah,haka ta kyaleshi kamar ko yaushe har Saida Rana ta fito sannan yayi wanka yayi sallah,yayi Shirin fita gun aiki.sosai sukayi Hira inda ta rakashi har bakin motarshi, kasancewar yarinyar tasu Bata tashi ba.

Sannu sannu dabi’ar Bashir ta zamewa Sadiya jiki,Dan haka ta daina Masa magana domin ko tayi ma a banza,ko tayi maganar iyaka ya daina na kwana Daya ko biyu,sai Kuma ya koma ruwa,idan har taga yadawo gida dawuri tofa bukatar ta yakeyi,Kuma shi Sam Bai iya wani wasa ba,da zarar yayi iya abinda zaiyi burinsa kawai ya zira kwallo a raga, bukatar sa na biya shikenan.

Hakan yasa Sadiya ta Fara Jin ya sire Mata,domin duk abinda yayi haushi yake bata.

Batada abokin Hira sai wayarta,inta gaji da Danna tayi bacci.

Yauma kamar kullum tana kwance tana charting a WhatsApp,ganin duk ABOKAN hirar tata sun sauka yasata kashe wayar cike da takaici,wani tunani ne ya fado Mata a zuciya,kawai saita jawo wayar tare da bude data dinta,inda ta shiga Facebook account ta bude.

Bada wani jimawa ba ta dinga samun friend request,take ko ta dinga accept,inda cikin lokaci kankani ta shiga hira da wasu daga cikin ABOKAN nata,Wanda mafi akasarin su maza ne.haka kawai sai taji dadin Facebook din ma fiye da WhatsApp din.

Yau Kam da wuri  Bashir ya dawo, Sam Bata  wani damu ba,Dan tasan ma’anar dawowar shi da wuri,itako duk abinda ya kamata tayi Masa ta jawo wayarta taci gaba da charting….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button