HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 8

 *HALIN GIRMA*            8

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

***

Sake kiranta yayi a karo na biyu, ta daga tana goge ruwan da yake hannun ta, tana ciki tana wankewa Gaji toilet shi yasa bataji kiran farko ba, sai da ta fito wanda yayi daidai da sake kiran.

“Assalamu alaikum.” Tayi sallama cikin muryar da ta saka Moh sallama duk bacin ran Khalil da ya kwasa yanzu.

“Wa alaikisalam, kina lafiya?”

“Lafiya lou wallahi, ya aiki?”

“Alhamdulillah, ina waje nazo ganin Abba.”

“Owk tam gani nan.”

Tace sannan ta ajiye wayar, ta fito tana tunanin yadda zata sanar wa Abban, a harabar gidan ta hangi motar sa, alamun ya dawo kenan, karasawa tayi wajen su tun kan ta isa Moh yake sake admiring kyawun ta, koman ta very simple hatta da tafiyar ta kamar ba zata taka k’asa ba, a matukar nutse take komai hakan yake sake dulmiyashi a kogin soyayyar ta.

   Taba shi Musaddik yayi, ya dan yi firgigit sannan ya saki murmushi

“Allah zaka bada maza, kamar ba soja ba?” Yayi whispering maganar yadda Moh din ne kawai zaiji, banza yayi masa ya rigata karasowa wajen suka hadu a hanya. Kamshin turaren sa me dadi ya rigashi karasawa

“Sannu da zuwa.” Tace tana shakar kamshin da ta kasa tantance shi

“Yawwa Dear, kina lafiya?”

“Alhamdulillah, lafiya lou.”

“Masha ALLAH, gani nazo neman izini wajen Abban mu, ina fatan ban makara ba.”

Girgiza masa kai tayi

” Masha ALLAH, yanzu ya za’a yi, shige mana gaba zakiyi muje ko?”

Da sauri ta kalle shi, idanun ta suka haska cikin nasa sai a lokacin taga ya rage kasumbar fuskar sa sosai kamar ya aske, fuskar sa ta fito sosai idanun sa da suka fi kama da a lumshe suke sun fito sosai, saurin dauke kanta tayi tana jin wani irin faduwar gaba

” Tunda ba zaka yi introducing dina ba, bari nayi da kaina.” Musaddik da ya karaso wajen ya harare shi yana murmushi

” Sannu malama Fatima, sunana Musaddik kuma ni ogan sa ne a komai, ina fatan zaki karbi aboki na hannu bibbiyu dan da gaske yake ba da wasa ba.”

” Sannu da zuwa,  Ina wuni?” Ta gaishe shi tana sauke kanta kasa har yanzu bata daina jin faduwar gaban ba

” Lafiya lou, ya komai da komai?”

” Alhamdulillah.” Tace

” Bari na duba Marwan sai yazo ya yi wa Abban magana.”

” Owk.” 

Ta juya zuwa part din su tana addu’ar kar su hadu da khalil, a falo ta tarar da su dukka Zeenat na danna wayarta, Maama na zaune Marwan yayi filo da kafarta yana kallon Disney World, shigowar ta ya saka suka maido hankalin su kanta

” Sannu da gida Mama.” 

Kin amsawa tayi, ta gimtse fuskar ta ta muskuta tana cigaba da kallon TV.

” Mama dama Muhammad ne yazo wajen Abban.”

Da sauri Zeenat ta mike, ta hau kyalkyala dariya kamar wata sabuwar tababbiya, kawai sai Maman ma ta hau tayata, suka sakata a gaba da dariya abinda ya bata mata rai har taji kuka na neman xuwar mata

” Su Malam ne anzo za’a Abba kenan, ya kyauta miki ai ya taimaka da yazo, dan Khalil yafi karfin ki, shi din dai shine daidai da me bakin hali irin naki, me kike so nayi yanzu.”

Daidaita muryar ta tayi, tace

“Dama so nake Marwan yayi musu iso wajen …” Da sauri ta katse numfashin ta

“Tashi maza maza Marwan, je kace wa Abban gidan su Aliyu yana da baki, yi masa kar ya gaji da jira yace ya fasa.” 

Sai ta sake tuntsurewa da dariya Zeenat na tayata. Hawayen da take ta rikewa ne suka shiga sakkowa a fuskar ta, 

“Kadan kenan kika gani in dai junan mutum bakin ciki toh wallahi shine a ciki.” Zeenat tace tana jan tsaki. Juyawa tayi zata fita Maman ta tsaida ta

“Zo ki wuce ki wanke kanukan da aka bata.”

Bata ce komai ba, tayi hanyar kitchen din zuciyar ta na kunci sosai. Wanke wanken take tana kuka sosai, irin wand a ta jima batayi ba, tana da masifar dauriya akan duk abinda za’a yi mata, amma kuma a wannan bangaren ta rasa me yasa ta kasa jurewa, wulakanci bashi da dadi kuma yanaa da ciwo musamman a tasaka gaba ana dariyar shakiyan ci da wulakanci.

   Adadin lokacin da ta saba dauka tana wanke wanken sai data ninka shi saboda damuwar da take ciki. Ta baya ta fice ta koma bangaren Gaji tana jin kamar ta tattara komai ta bar musu gidan. Sau daya a cikin ranaku masu yawa yau ta tuna mahaifiyar ta, shiyasa bahaushe yace wanda ya rasa uwa yayi kuka.

***Da kallo Abba ya bisu har suka zauna suna masu nuna jin nauyi da kunyar sa. Bayan sun gaisa yace

“Gashi kuma ban shaida ku ba.”

“Dama Fatima ce ta sanar mishi da Abban yace yazo ya nemi izini a wajenka, toh shine dama dalilin zuwan namu.” Musaddik yayi maganar yana addu’ar Allah yasa be kwafsa ba.

“Toh toh…” Abban yace yana tunanin yadda al’amarin yake, musamman maganar Khalil da ya riga ya karbe ta 

“Ita Ummin ce tace kuzo ko?” Yayi tambayar yana kallon su

” Ummi?” Suka Hada baki

” Auw Fatima toh, sunan Uwata ne ni ummi nake kiran ta.”

“Masha ALLAH, Eh Itace ta turo mu.”

“Toh shikenan, ina zuwa.”

Tashi yayi ya shiga ciki, ya kira wayan Abban su Fatiman dan yasan be kai ga dawowa gidan ba 

“Yaya barka da warhaka.”

“Barka dai, ya aiki?” 

“Alhamdulillah mun gode Allah.”

“Allah ya bada sa’a, kana ji, dama akan maganar Ummi ne, yaron nan Ibrahim yazo da maganar sa jiya har ma na bashi izinin daidaitawa da ita ganin shi din na gida ne, yau kuma kwatsam sai ga wani yazo shi kuma wai Ummin ce ta turo shi.”

” Ibrahim Kuma?

“Eh shifa.”

“Amma da kaina na tuntubi Hajara da maganar sa, amma ta nuna min sam ba da gaske yake ba, hakan ya saka na ce Ummin ta sanar wa wannan din yazo ya ganka.”

“Ibrahim kam yazo jiya ya same ni, ga wannan kuma shima.”

“Allah ya kyauta.”

“Zamu duba muyi bincike, idan yaso sai a bashi dama shima, wanda suka daidaita shikenan, bamu san me Allah ya boye ba, kar muyi gagagwa.”

“Shikenan Yaya, duk yadda akayi yayi.”

“Madallah.”

Fitowa yayi ya tarar dasu a zaune, ya zauna yana fuskantar su

“Kace sunan ka?”

“Muhammad.”

“Toh Muhammad daga ina?”

“Adamawa-Yola, amma mahaifiya ta yar Kano ce, nima kuma kaso me yawa na rayuwa ta nayi shi ne a Kanon.”

“Toh toh Masha ALLAH, Anyi karatu Muhammad?”

“Eh Abba, nayi karatu.”

” Aiki fa?”

” Soja ne ni.”

” Ah Masha ALLAH, soja ga wuta ga yaki, soja marmari daga nesa. Hakan yayi kyau a cigaba da samar mana da tsaro a k’asar mu, Allah ya yaye mana abubuwan da suke damun mu suka hanamu zaman lafiya a k’asar, Allah kuma ya cigaba da dafa muku.”

” Amin.” Suka amsa cikin jin dadin yadda Abban ya sake dasu

” Shikenan Muhammad, ka bani number wayar ka da address din ka, zan neme ka in sha Allah.”

Hannu Musaddik yasa a aljihun sa zai ciro wallet dinsa ya dauko complimentary card din Moh din yayi sauri fara karantowa Abba number, yace kuma zai masa text message na address din in sha Allah. Godiya sukayi masa suka fito yana jin tsoro na shigar sa, tsoron kar Abban yayi rejecting dinsa, tsoron yadda zai yi komai ya tafi yadda yake so.

  Kiranta ya sake yi ta fito bayan ta wanke fuskar ta sosai dan kar ya gane, duk da haka sai da ya gane kuwa,ya kafe ta da ido yana jin babu dadi.

“Me ya samu idon ki?” Ya tambaye ta dan ba zai iya hakuri ba,

“Ba komai.”

“Ban yarda ba, kalli idon ki, Dan Allah ki fad’a min me ya faru?”

“Abu ne ya fad’a mina idon dazu, amma ya fita ma.”

“Ban yarda ba, ki fad’a min waya bata miki rai? Waye ya saka ki zubar da hawayenki masu tsada?”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button