Education

Abinda Ya Kamata Kayi Lokacin Dakaga Anciri Kudi Account Dinka

Abinda yake faruwa yanzu ga mutanen da ake cirar musu kudi a bank account nasu da sunan ana zarar kudin bashin Nirsal da suka karba

Akwana biyu din Nan an Sami bullowar wani Abu Wanda sai dai kawai kaga an zara maka kudi a cikin account din ka

Idan Kayi tambayar ya akayi kudin ka ya fita sai kaji mutane suna CE maka nirsal ne suke cirar kudin su directly

To gaskiya duk Wanda yaga an cira masa kudi to ya Fara tuntubar bankin Nirsal mafi kusa da shi domin tabbatar da sune suka dauki kudin ko Basu bane kaji menene zasu CE maka

Sannan duk abinda suka fada maka sai ka ziyarci bank din ka kayi musu rohoto cewa an cire maka kudin ka
Suma zasu duba maka inda aka Kai wannan kudin naka

Saboda na’urar cirar kudin tana cirar kudi ne har a account din Wanda Basu ci kudin Nirsal ba

Sannan Kuma nirsal Basu bayar da Sanarwar zasu Fara cirar kudi account na mutane ba kawai sai gani akayi ana zarar kudin a account din mutane

To duk Wanda yaga matsala a account nasa kada ya tsaya daga abinda mutanen gari suke fada masa Abu mafi sauki shine kajeka bank suyi bincike Akan account din naka su Kuma zasu fada maka inda asalin kudin ka ya tafi

Allah ya sa mudace

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button