BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

[12/3, 9:02 AM] .: BABBAN YARO
MALLAKAR BINTA UMAR
71
Daurewa kawai yayi ya karasa kusa dasu cikin yanayin tafiyar sa ta jarumin namiji, baby Aysha ya dauke daga jikinta kawai ya fuce daga dakin. Kallo granny tabi shi dashi itanan ta kira shi ne tayi musu fada shi da Asma’u gashi ya futa, cigaba da rarrashin Asma’u tayi kusan mintuna ashirin tukkuna ta futa daga dakin, parlor ta same shi ya tasa baby a gaba yana kallo. Tace”Kai da zaka rarrashe ta kuma sai ka dauko ‘yar ka ka futo Asma’u tana bukatar Dan rarrashi.” Da Jan ido ya kalleta yace.” Granny nima Neman Wanda zai rarrashe ni nake domin bata fini jin ciwo ba.” Tace”Ai kai namiji ne kana da jarumta ita kuwa macace don Allah ka rike yarinyar nan amana k’ato kar ka hofintar da ita zakaji dadin zama da ita domin jikina na bani akwai alkairi a auran Ku da ita.”
Shuru yayi kawai ta cigaba da cewa a yanzu tana cikin damuwa saboda haka duk wani bori da zata yi maka kayi hakuri kar ka biye mata domin an shiga hakkin ta ne.... Ranshi a Dan bace yace." Granny wato ni ba a shiga nawa hakkin ba kenan? Hararasa tayi zata yi magana ya katse da sauri yace." Nifa bani nace ina son ta ba domin ni yanzu babu maganar aure a tsarina, gaskiya amma dai tunda kun kulla Allah ya sanya alkairi, amma kiyi mata fada sosai duk wasu halayen ta da nasa ni a da to ta sauke su domun bazan zauna da ita dasu ba."
Granny tace.” Insha Allahu zaka ji dadin zama da ita kuma zan ja mata kunne da kyau kai dai ka zama namjin duniya a gidan ka.” Shiru yayi mata ita kuma ta cigaba da yi masa fada har sanda Jahid ya shigo, ya same su. Kusa da Amjad din ya zauna yana fadin “Ya zamu yi ne gasu Khalid can sun shirya walima kamar yanda aka saba sai ka kimtsa bayan sallahr magariba zamu fita.” Gyada kansa kurrum yayi Jahid din yaji babu dad’i yace.” My friend nasan nayi maka katsalandan cikin rayuwar ka amma ina me baka hakuri don Allah idan hakan bai maka dad’i ba, hak’ika banaso in rasa Asma’u saboda kyawawan haleyen ta tunda Allah ya kaddara cewa ba matata bace shine nayi maka sha’awar auran ta ko don baby nasan gaba zaka ji dadin wannan abun insha Allah kayi hakuri ka sasssutawa zuciyar ka idan ka saki ranka na tabbata itama Asma’u zata saki nata Ku zauna lafiya.
Amjad ya dafa kafadunsa cin kyakyawan lafazi yace"Jahid babu abunda zance maka wallahi sai dai fatan gamawa lafiya ka nuns min kulawa a rayuwata babu shakka zan karb'i Asma'u saboda kai zan rike ta amana dalilin ka, insha Allah." Jahid yaji dad'i sosai hannu ya bashi suka yi musabaha kana ya mike yana fadin bari inje in sanya a kara gyara guri yanzu." Amjad din yace." Zan fito Yanzu insha Allah. "
Granny ma mik’e wa tayi ta nufi kicin gurin Iyami dake had’a abunci na tarb’ar amarya nan granny ta sanya mata hannu suna yi suna hira da yadda abun ya faru har suka kammala tsaf Iyami ta fito ta gyara daining lokacin Amjad ya tashi daga gurin yana bedroom d’insa shi da baby Aysha da take was an ta kan bed din sa, wanka ya fito daure da towel ya tsane jikin sa tsaf gaban dressing mirror ya tsaya ya gyara sumar kanshi hade da shafe ta da Maya mayai masu asalin tsada jikinsa ya shafe da turare kana ya shafa mai sama-sama , wardrobe din shi ya bude ya dauko sabbin kaya cikin ledar su, yadin plitex ne blue black dark yana da taushi sosai sngjilet ya sanya fara kal kana ya Dora rigar a kai wacce ta sakko masa har kasa din ki Muhammad Abacha kenan tsaf ya gyara links ya d’aura a gogon shi Dan Asali turare ya fesa a jikinsa. Ya aje inda yake zuciyarsa na tuno masa shararran k’amshin Asma’u Wanda yake kwadayin sake jin shi, amma ya lura kamar yarinyar da rigima ta shigo gidan dole ya kiyaye kar ta raina shi, zai yi kokari gurin ganin bai shiga harkar ta ba, baby ya gani na kokarin saukowa daga bed yayi saurin d’aukar ta yana fadin”Kin fiye kiriniya Momy sai kinje kin fad’i ko.” Dariya take bangala masa tana wasa da kwantaccan sajan sa dake shek’i, haka suka futo parlor shi da baby suna dariya.
Granny ya samu zaune cikin kujera zaune ta k’urawa TV ido yana futowa tace”Yawwa dama kai nake jira ka futo ka shiga gurin Asma’u nayi-nayi ta fito taci abunci taki kaje ka rarrashe ta.” Zama yayi cikin kujera ba tare da ya bawa maganar ta muhimanci ba yace.” Ba sai ki k’yaleta ba cikin ta ne idan taji yunwa zata futo taci.” A”a baza ayi haka ba ka shiga dai ga lallab’ata. ” Cikin mamaki yake kallon Granny yayi ‘yar dariya hade da Sosa kansa yace.” Granny ni baza ki rarrashe ni inci abunci ba sai wata daban ni kike sawa ma in rarrashe ta alhalin nima Neman Wanda zai rarrashe ni nake ni babu inda zanje idan ta gadama ta futo taci kanta tayiwa.” Bata fuska granny tayi tace”Bana son gaddama yarinyar nan amana ce a gurin mu bana son abunda zai kuntata mata da wanne zata ji.” Shiru yayi ganin ranta ya b’aci sai ya zab’a baby a kafad’a suka shiga dakin da Asma’u take.
Ina kwance har yanzu ina sak'awa da kwance wa naji an turo kofar dakin an shigo tun kafin in d'ago kaina naji k'amshin turaran sa rintse idon nayi da sauri Sam! Bana son mu hada ido dashi. Idonshi a kanta har ya k'araso gurin, baby ta dinga zillo wai ya sauke ta, yana aje ta ta fara kokarin hawa bed din da kansa ya d'ora ta jikin Asma'u dake kwance rif da ciki. Hucin numfashin sa naji a dai-dai wuyana, tsigar jikina ta mike k'amshin sa duk ya baibaye ni. Gabana fad'uwa kawai yake. Shima nashi b'angaran hakan yake domin wata irin sha'awar ta ce ta bijiro masa mai zafin gaske. Yanayin kwanciyar da tayi ya ya sanya shi cikin halin k'aka ni kayi...... Gyaran murya yayi had'e da had'e fuskar sa sosai ya ambaci sunan ta sama-sama." Asma'u.'!! Yarrrrrr!! Naji a jikina domin bai tab'a kirana da irin wannan muryar ba.... Shiru nayi. Tsaki yaja hade da fad'in"Nasan kina jina kika min shiru Ok ina so ki shiga hankalin ki ki nutsu sosai ki San da wa kike zaune naji na karb'a an lak'aba min saboda gujewa sharrin ki jama'a suke gudun had'a zuria dake ni don an raina ni sai a wani d'aura min aure dake.... OK naji na karba amma ki kiyaye wallahi domin bana son shirme da gatsali nayi rashin matata mai biyayya kiyi koyi da halin 'yar uwarki Mimi sai mu zauna lafiya dake ina fatan kin gane ko."!!!!?
Ikon Allah mutumin da aka turo yayi rarrashi shine yake gasa wannan maganganun masu zafi Wanda zasu iya sanya zuciyarta ta buga a take babu shakka Kalmar da malam bahsushe yake fad’i gaskiya ne Namiji tabarmar k’aya ne waiii
Tun kafin ya karasa maganganun sa nake wani irin kuka yayin da nake jin wani irin zafi da zugi a cikin zuciya ta, ji nayi bazan iya kyaleshi ba, domin a ganina idan na barshi ya saba min da wannan cin mutumcin to babu shakka nice zan sha wahala da sauri na mike zaune ina goge hawayen fuskata da gefan lifayar dake jikina. Ido muka hada dashi yaji gaban shi ya fad’i ganin yanda idanunta sukayi wani irin ja!! Dama gasu masu girma..! Kauda kansa yayi da sauri! Yana wani ya mutse fuskarsa….. Murya ta bata futa sosai nace”Ni ake gudun had’a zuri’a dani.”? Daga kafad’a yayi yana kallona. Na cigaba da cewa “Saboda ana gudun mugun halina, shi Jahid din ne yace maka haka.” !? A d’age ya kalleta yace.” Idan shine ya fad’a min ke Baki isa ki na fad’a miki E ko A’a ba.” Cikin takaici da ciwon zuciya nace”Ni nasan Jahid don an fi k’arfin shi ya sanya ya hak’ura dani, amma babu shakka soyayyar da yake min babu algus a cikin ya nafi tunanin wannan maganar daga bakin ka ta fito saboda mugun sharrin ka da b’ata sunan ka, ita kanta mahaifiyar Jahid din da ta hana faruwar auranmu bata yi min wannan mummunan kazafin fa sai kai.! Tom nagode K’warai amma nima ina fada maka cewar “Wallahi irin zaman da kayi da Mimi kai baka isa kayi irin shi dani ba, sharrin ka zai koma kanka! Kuma baka isa ka kashe ni da bakin Cikin ka ba, ko Mimi ma itace ta sa kanta har ta mutu ta sanadiyar ka ni baka isa kayi sanadin mutuwa ta ba, sai Allah.”
Ranshi yayi mugun b’aci jin kausasan lafuzan ta, dama hausawa sun ce baki in yasan abunda fad’a to bai San abunda za a mayar masa ba… Take yanayin fuskar sa ya sauya sai wani huci yake yi yana kallonta tana kallonsa… Gyada kansa yayi yace.” Kinci albarkin baby Aysha dake jikin ki Yanzu amma da baby shakka sai na miki abunda Baki tab’a tsammani ba.” Da sauri nace” Bans so inci albarkacin kowa kayi min abunda kayi NIYYA don Allah.”!!! Bai saurare ta ba ya bude kofar da sauri ya fuce kamar kububuwa. Granny na zaune taga futowar sa yayi waje kamar zai tashi sama da sauri ta shiga dakin Asma’u sai ta tadda ita ta rungume baby tana gursheken kuka har da majina. Hankali a tashe ta karasa dakin tana fad’in ” innalillahi ASME me yayi miki kike Wannan kukan nagan shi shima ya futa da b’acin rai ki daina kuka ki fada min damuwar ki.”! Cikin kuka nace”Granny zaman mu da abban baby bazai yi wu ba.”” Hankali a tashe! Tace”kan wane dalili kika fad’i haka.” Kasa fada mata komai nayi sai kuka domin ji nake kamar in mutu ya ilahi wai same zanji ne.”!!? Kuka ta fashe dashi itama sosai take fad’in “Kiyiwa girman Allah da Annabi kiyi hakuri babu shakka nasan abunda ya faru tsakanin ki dashi ba me dadu bane da nasan zai shigo yayi b’arna da ban turo shi ba, kiyi hakuri ki dubi wannan yar lab’ub’uwar yarinyar dake jikin ki ki zauna da ubanta ba don halinsa ba, nasan yana da fushi amma ba shi da rik’o don Allah dukan abunda kika San zai hasala masa zuciya ki guji yin sa kin ji ko.” Duk cikin kuka take wannan maganar.
Sosai tsohuwar ta bani tausayi goge fuskata nayi ns rike hannunta dake karkarwa nace”Granny ki daina kuka don Allah insha Allahu zanyi abunda kika ce din zanyi kokarin ganin na kawo zaman lafiya s zamantakwar mu dashi insha Allah nasan ni tawa kaddarar kenan kuma zan karb’e ta hannu biyu.” Tace”Yawwa ko kefa Allah yayi miki albarka.” Ameen nace. Ina jin wani irin kaunar tsohuwar Cikin zuciyata. Tace”Muje kici abunci don duk ga alamu nan sun nuna ba kici abunci ba.” Nace”zan fito yanzu insha Allah .” Mik’ewa tayi tana kokarin d’aukar baby dake wasa kan bed yarinyar ta sa kuka Granny ta fuce tana fad’in “Ja’ira kawai yau ni din kike gudu saboda kin ga uwarki.” Murmushi nayi kawai na mike ina warware liffayar jikina toile na shiga na wanke fuskata kana na dauro alwala na futo k’arfe hudu da rabi na yamma, dadduma na shimfid’a na tada sallah cikin nutsuwa bayan na kammala addu’a ne na mike a nutse na tsaye gaban wani dressing mirror dake cike da kayan shafa, fuskata na kalla naga duk ta kode dama ban yi wata kwalliyar kirki ba aunt Hauwa babu yanda batayi dani ba naki raina babu dad’i na futa daga dakin. Da babu a hannu granny da Iyami da wasu mata uku s zaune a parlor suna magana sama-sama da suka ga na futo sai suka yi shiru, Kai tsaye gurusu na nufa a nutse na gashe da matan kana na mike na isa gurin cin abunci ina mamaki kallon banzan da d’aya daga cikin su take min……. Magana suka cigaba da yi Wanda bana fahimtar me suke fada na dai lura kamar ransu a b’ace yake dukanin su, kad’an na zuba abuncin ina ci kamar magani baby nake bawa àbinci kad’an kad’an ganin tana so taci babu laifi taci kad’an hankalina na mayar kan su granny jin abunda matar nan dake hararata take cewa”Yo!! Da kike wannan maganar idan Hafsatu ya aura kina nufin ita bazata kula masa da baby ba, ai kusancin sa da Hafsatu yafi Wanda ita take da Uwar yarinyar, ni dai wannan al’amari bai min dad’i ba kuma an munafurce ni.”!! Iyami da bata so a tab’a mata granny tace” Haba ke kuwa da girman ki da komai kike magana irin ya yara k’anana shi ga aure nufi ne na Allah kuma babu laifin Uwar dakina anan, tunda ba itace tace Dole sai anyi auran ba Allah dai ya kaddara za’ayi…..! Cikin hayagaga Inna Suwaiba mahaifiyar Hafsa tace”Kinga bana son munafurci da iya samu guri Yaro dai danmu ne mu muke da magana a kansa ba ke kar ki kara sanya mana baki anan, ai INA zaune a gurin nan har Amjadu ya shigo gidan a matsayin na uwarsa yan umarce shi da iya yi min Abu kuma sai yayi, Granny tace”To idan ya shigo sai ki umarce shi kina da iko dashi duk hukuncin da kika yanke a kansa dai-dai ne dank’i… Matan da suka rako inna Suwaiba suka ce K’warai kuwa maganar ki hakkun kamar yanda kike da iko dashi muma haka nake dashi……….