Uncategorized

HEEDAYAH 9

 

Hajiya Rahinah na xaune parlonta watching a movie, almost absentminded, lkci lkci take kallon Heedayah da ke xaune kasan lallausan carpet dake 
tsakar parlon, Short bread ne hannunta tana ci a hankali, irin kallon da take ma kofar kitchen sai kace tana ganin kofar ne da idanuwanta, Hajiya 
Rahinah ta sauke ajiyar xuciya for the countless time ta girgixa kai, ba karamin tausayin Heedayah take ba har ranta, text ne ya shigo wayarta ta 
dauka sanin baxai wuce Barrister ba, dai dai nan kuma aka yi knocking kofar parlon, Farida dake xaune dining tana shan cornflakes ta mike ta nufi 
kofar, bude kofar tayi wani matashi dake tsaye bakin kofar yana kallonta yace “Baki je islamiyya ba?” Ta langwabar da kai tace “Mami tace I should 
stay behind xata fita ynxu” Xai yi magana ganin Mahaifiyarsa xaune parlon ya shiga ciki da sallama, Farida ta rufe kofar ta koma dining, xaunawa 
yyi kujeran dake kusa da na mum din tasa yace “Ina yini Mami” tana danna wayarta tace “Lfya lau, jiya baka xo ba Why?” Ya shafa kansa a hankali 
yace “Mami Uncle ne ya bani aiki, amma kin manta ne nace maki baxan dawo ba” Tace “Ohk, ka kai ma Salma sakonta kuwa” yace “Eh daga can nake, har 
xan kawo maki Fadil wai xai biyo ni na fasa, kar ya xo yyi ta mana kuka” Tace “Gobe ma Monday akwai aiki ai” Yana kallon Farida yace “Mami wai ke 
kika ce kar ta tafi islamiyya?” Da sauri Junaid ya dauke kafarsa xai mike jin abu na ta6a sa, bai kai ga cewa komai ba ya ga Heedayah rakube jikin 
kujeran da yake xaune, Kuri tayi ma kafarsa da ido, ya mike ya dinga kallonta, Mami tayi dariya tace “Kai dai ka fiye tsoro kamar mace” Yace “Mami 
wacece wnn kuma?” Mami tace “Bakuwa nayi daxu” hade fuska yyi ya canxa kujera ya xauna, Mami ta mike tana kallon Farida tace “Ki dawo nan parlor ki 
xauna, yanxu xan fita, you make sure baki bar ta ita kadai ba, I will be back soon, kasuwa xan je” Farida ta mike ta dawo parlon, Mami ta nufi 
Heedayah ta duka tana kallonta ta shafa kanta tace “Kina son wani abu dear?” Gyada kai tayi tace “Xan sha ruwa” Mami tace “Farida ki kawo mata 
ruwa” Farida ta tafi fridge dauko ruwa, Mami ta kalli Junaid tace  “Sai na dawo, I am not staying long” ya mike yace “Ni ma ai wucewa xan yi Mami” 
tace “Aa ka jira ni, I said I am not staying long” daga haka ta nufi kofa, da kallo ya bi ta har ta fita, sannan ya koma ya xauna yana kallon 
Farida yace “Who is she? I mean the girl” Farida ta bude hannu tace “Mami came back with her earlier this afternoon” Ya buda ido sosai yace “From 
where?” Farida tace “I don’t know” girgixa kai yyi ya kara satan kallon Heedayah, direction dinsa take kallo, ya d’an hade rai calmly yace “Kin san 
ni ne kike kallona?” Laluben kasa ta shiga yi tana neman murfin bottle water cikin sanyin muryarta tace “Ni ba kallon ka nake ba” yace “Hoto kike 
daukata da idon ki idan ba kallona kike ba kenan” Ta d’an turo baki bata ce masa komai ba tana ci gaba da lalube lalubenta, Farida ta koma kusa da 
shi da sauri ta kai bakinta kunnensa cikin rada tace “Yaya she is blind fa!!!” irin yanda ya yo waje da ido yana kara kallon Heedayah yasa Farida 
tayi dariya bata shirya ba, ta dinga dariya har da kyakyatawa da saukowa saman kujera, Shi kam kallon Heedayah kawai yake da mamaki ya ma kasa cewa 
komai, bai ankara ba sai ganin hawaye na sauka fararen idanuwanta yyi, Bai san lkcn da ya mike ba, Farida ma ta hadiye dariyar da take tana 
kallonta, ya nufeta ya duka kusa da ita yace “Me yasa kike kuka??” Shessheka ta fara yi tace “Xan tafi gun Abba” Farida ta dawo kusa da ita da 
sauri tace “Yanxu fa Mami xata dawo” Junaid ya kai mata rankwashi a kai yace “She thought u are laughing at her… What’s making u laugh that loud 
at the first place” Farida tace “Kiyi hakuri, ba dake nayi dariya ba wllh” Ita dai Heedayah sai juya biscuit din hannunta take hawaye na xuba 
idonta, Junaid yace “Kin ji ta baki hakuri, kiyi hakuri kin ji” Shiru tayi masu, ya dafa goshinta yana goge mata hawayen da hannunsa yace “Kin 
hakura?” gyada masa kai kawai tayi, nan kuma ta daina hawayen, mikewa yyi ya koma kujera ya xauna so relieved ganin ta daina kukan, shi dai fa har 
sannan ya kasa yrda bata gani don gashi sai kallonsu take tana kifta fararen idanuwan, Farida ta rufe bottle water din ta mike ta koma kan kujera 
ita ma, Junaid ya dau wayarsa ya shiga gun msg yyi typing kamar haka, “Da gaske bata gani? Don’t joke with me” mika ma Farida wayar yyi, Farida na 
karantawa ta kallesa tayi masa alamar rantsuwa cewar Heedayah bata gani, kara kallon Heedayah yyi da shock, can ya mike ya wuce sama yana kara 
waigo ta. Farida ta canxa tasha ta maida hankalinta kan movie din da ake yi, bayan kusan awa daya taji muryar Junaid ya sakko kasa yace “Why don’t 
you tell her to lie down Farida?” Farida ta juya da sauri tana kallon Heedayah da ta kwantar da kanta saman kujera tana bacci daga xaunen da take, 
Farida ta mike tace “Ban sani ba” nufenta tayi ta ta6a ta tace “Ki tashi in raka ki daki” Heedayah ta bude ido da sauri tace “Aa” Farida tace “To 
hau kan kujera” mikewa tayi ta fara laluben kujeran, shi dai Junaid kallonta kawai yake, Farida ta sa ta kwanta kan kujeran sannan ta koma ta 
xauna. Shidda da yan Mintuna Mami ta shigo gidan da ledoji manya manya, Farida dake parlon har sannan ta mike tana mata sannu da xuwa ta amshi 
ledojin, Mami da hankalin ta na kan Heedayah tace “Me yasa kika bari tayi bacci ta yamman nan?” Farida tace “Ina son in tasheta daxu yaya yace in 
bar ta” Mami tace “Ina yayan?” Kafin Farida tace komai sai gashi nan sakkowa, Mami ta nufi Heedayah ta dafa kanta tace “Dear” bude ido tayi da 
sauri, Mami tace “Yamma yayi tashi kar ki yi sake bacci” Heedayah tace “Abbana fa?” Mami tace “Ga kaya nan Abban ki yace a kawo maki…” Heedayah 
ta katse ta tace “A’a ina son in je wajensa” Mami tayi murmushi tace “To yana jiran ki a waje” kallon Junaid Mami tayi tace “Take her outside, xaka 
ga mota a waje, ka kai ta motar” shiru yyi yana kallon mum din tasa, ganin ko kallonsa bata yi ba sai bude ledojin da Farida ta ajiye take, ya 
karaso cikin parlon yace “But Mami I thought she’s blind how will I take her outside” Mami ta hade rai tace “Kama hannunta xaka yi ku tafi, ko in 
kai ta da kai na?” Ya girgixa kai yace “Aa” ya nufi gun Heedayah, Farida sai dariya take kasa kasa, ya kamo hannun ta jin haka ta sakko daga saman 
kujeran, kamar me counting steps dinsa ya nufi kofar fita yana rike da hannunta, Farida ta bi su da kallo tana danne dariyar ta, sai da suka fita 
parlon, Heedayah dake ta bin sa tace “Ha’an da sauri kake tafiya xan je in fadi” kallonta yyi sannan yace “To ba sai ki fadi ba” Bata ce masa komai 
ba har suka fita gate, ya nufi motar da ya gani a bakin gate din, Bude motar aka yi barrister ya fito, ganinsa Junaid ya yi kasa da kai ya gaishesa 
da ladabi, Abba ya amsa da fara’a yace “How are you doing Junaid?” Yace “I’m fine sir” Abba yace “Ashe ka dawo, kuna hutu ne?” Junaid yace “Ehh 
Abba mun yi hutu” Abba yace “To maa Sha Allah, Allah ya taimaka son” Junaid yace “Ameen nagode” Heedayah sai murmushi take jin muryar Abba, ta fara 
lalube lalube xata ta6a sa, Murmushi yyi ya duka kusa da ita ya kamo hannunta yace “How are you my dear?” Ta fada jikinsa a hankai tace “I am fine 
Abba, are you taking me with you now??” ta gefen ido Junaid ya dinga kallonta, nan kuwa he is trying to vividly recall weda he said anything bad 
daxu da turanci da yyi magana da Farida…. Abba yace “No, xaki tsaya tare da Mami kinga ni xan tafi aiki ne” tayi shiru bata ce komai ba, amma 
gaba daya mood dinta har ya canxa, yace “Ga kaya Mami ta siya maki da yawa sai ki ce mata thank you idan kun koma ciki” a hankali tace “Ohk” yayi 
patting kanta yace “Good girl” cikin sanyin murya tace “Abba yaushe xan koma gun Ammina da Abbuna?” Tana magana har hawaye ya kawo idonta, Shiru 
yyi yana kallonta, can yace “Soon daughter, in sha Allah soon xa ki koma wajensu” mikewa yyi yana kallon Junaid yace “Ku koma ciki Junaid” Junaid 
ya kama hannunta yace “Toh Abba Allah ya kiyaye hanya” Abba yace “Ameen” Sai da suka shiga gate sannan Junaid ya kalleta yace “Ina Ammin taki da 
Abban ki???” shiru tayi bata ce komai ba, yace “Baki ji na ne?” A takaice tace masa “Ehh” tsayawa yyi da mamaki yana kallonta, can ya saketa ya 
koma gefe ya tsaya yace “To ai sai ki kai kanki ciki”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button