

Minista Sadiya ta bayyana haka ne a yayin jawabin da ta gabatar ranar Alhamis a wurin taron jawabin mako-mako da Fadar Shugaban Kasa ta shirya a Abuja Aminiya ta rawaito.
Ta ce, “Muna da shirin yayen N-Power da hadin gwiwar CBN, wanda mutum 300,000 daga cikin 500,000 da suka kammala N-Power suka bayyana aniyarsu ta shiga ciki; Za a koya musu sana’o’in da suke so sannan CBN ya ba su rance su fara sana’o’in.
Ministar ta bayyaan cewa, “Mun yi nisa, har mun fara shirin bayar da horo ga masu bukata, kuma na tabbata zuwa karshen watan Maris CBN zai ba su rancen.”
A cewarta, zuwa yanzu, “Kusan mutum 109,000 da suka ci gajiyar shirin N-Power sun fara sana’o’in kansu, har suna da masu aiki a karkashin su, kuma za mu iya gabatar da shaida da ke tabbatar da hakan.”
[ad_2]