ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A Hankali ya sayyadi yace ” JINNUL ATFAL sune aljanun dake shiga kananan yara Ma’aruf su irin wadannan aljanun suna da wuyar sha’ani saboda sun riga sun saba da yaran tun suna k’anana!kuma sakakin iyaye ke janyowa yaran aljanu!kaga yawan barin yaro shi kadae yana bawa aljanun kwarin guiwar shafar yaranmu!sannan yawan barin yaro gabancin magrib ya zauna shi kadae ko yana wasa shima yana sa aljanun shigar yaron da sakaki da addu’a ga uwar yaron ko barin yara ba kaya ajikinsu……”

Shiru yayi yana sauraren shi kafin yace ” To Malan yanzu menene Mafita……?

Murmushi yayi a hankali yace “Zan fad’a maka wasu magunguna da zaka sawo yanzu idan ka fita ka had’a mata Inshaa Allah ko da ban ganta ba zata samu sauki …
• GARIN KUSDUL HINDI (SANYA) .
• MAN ZAITUN
• MAN HABBATUSSAUDA,
A hada waje daya sannan a sa shi a wuta yayi zafi sosai sannan a sauke idan ya huce sai a samu kwalba ko wani abu a zuba a Rink’a shafa mata amma in son samu ne a karata……
• AYATUL KURSIYU
• KULYA
•FALAKI DA NASI
• TABBATI YADA
• KULHUWA
• SURATUL FATIHA.
TO IN SHA ALLAHU WANNAN YANA MAGANCE ISKA DA SAURI DA YARDAR ALLAH.……Haka kuma idan zata kwanta a shak’a mata tare da shafe jikinta dashi insha Allahu zata samu sauki zuwa sati daya sae ka dawo ka fad’a man yanayinta……”

Godiya yayi sossae sannan ya fiddo da kudi masu yawa ya aje mashi!amma sam yace ya kwashe abunshi bai masa dan ya biyashi ba……Haka ya dauk’a ya tafi daga nan islamic chemist ya wuce ya sawo abunda malan ya fada mashi sannan ya wuce gidan Madre ya kai mata !Ita da kanta ta hada tare da karanta surorin da yace sannan ta bashi tace idan yaje ya fara mata amfani dashi……

【】

“Allah ya tsinewa mai abunda aka hanashi……!

Da sauri Sumayya ta kalleta tare da wurga mata harara ta gefen ido sannan tayi kitchen tana boye garin maganin da beeba ta kawo mata wae tayi hayakin HQ dashi……

Itama hararan ta jefa mata tana rufe baki da hannu sannan tace “K’ala jikawa zaki yi ko?Yarinya kin mutu ba ruwana……”

Kamar ta fasa ihu ta juyo tana fad’in “Wae dan ubanki meye hadina dake……!

Washe baki tayi tace “Bunkul(Uncle)Shi ya had’amu……!

“Ubankine Bunkul din……”ta fad’a tare da jeho mata cup din dake hannunta……Sallamar Ma’aruf ta katsewa K’arama abunda tayi niyyar fad’a……Tayi gurinshi da gudu ta kankameshi tana washe baki……

Kayan dake jikinta ya kalla sunyi diki diki kamar bai mata wanka ba yau!……

Dariya ta saki da karfi tana kallon Sumayya data tako a hankali ta rungume Ma’aruf tace “Lahhhhh amma ke babbar yar iska ce aradu……”

Kuka Sumayyan ta saki tana fadin “Wallahi Ya Ma’aruf na gaji da wannan mayyar!dan Allah ka mayar da ita garinsu……”

“Aradun Allah ba inda zanje……”K’arama ta fad’a tare da watsa hannu baya kamar yarda ta ga Maitafasa nayi……

Kamo hannnunta yayi yana rungume da Sumayya ya zauna saman kujera ya dubi K’arama yace “Hafsa me kika wa Auntynki……?

Waro ido tayi tana dashire hakuranta tace “Ba abunda na mata kwarankwatsa……”

A Hankali yace “Ban hanaki wannan rantsuwar ba?Shiru tayi tare da rufe bakinta da hannu tana kallonshi……

Lumshe ido yayi yace “Ce tayi hakuri……”

Ba musu tace “Kiyi hakuri……”
Sumayya kam kara kankame hannunshi tayi tana fad’in “Dan Allah ka mayar da ita gurin Madre……”

Cikin sanyin murya yace “Sumayya ke bara ki iya zama da ita ba amma kike so akai ta gurin Madre……?

Turo baki tayi tace “Madre tsohuwa ce nikam amarya ce !Tun zuwan wannan yarinyar ta hanani jin dadin aurena……”

Tabe baki yayi yace “Dan tana fad’ar Gaskia?

Shiru ta masa ta mike ta dauko shinkafa da wake da mai da ta masu ta zuba mashi!Da yake yana son Shinkafa da mai haka ya sauka yaci ya koshi yasha juice ya mike ya shige daki !K’arama kam komawa tayi ta kwanta rigingine saman carpet taci gaba da kallonta har sae da taga ya shige d’aki sannan ta mike ta koma inda ya tashi ta zauna tare da cinye sauran abincin da ya rage……

K’aramin tsaki Sumayya ta saki lokacin da ta fito tace “Shegiya a cici……”

“Bunkul yace wanda yayi shiru shi ke da hankali!Na fiki hankali……”Cewar K’arama tana lashe hannunta……

Tsaki ta saki ta nufi dakinta a can ta iskeshi yana kokarin bude windows din jin dakin na fitar da wani karni karni ……

“Warin me ye haka Sumayya……?
Yatsina fuska tayi tace ” Oh na manta d’azu Ahmad ya kawo man kifi shine da naci na manta ban yar da ledan ba!ka ganshi can under bed……”

A Hankali ya girgiza kai!za yayi magana wayarshi ta hau ringing!ganin new number ne yasa har ta katse bai dauka ba……Wanka ya fad’a!A Ka kuma kiran wayar Sumayya ta kai hannu ta dauka!dafe gabanta tayi ganin number Beeba ke kiranshi……Jikinta na kyarma ta dauka tayi shiru……

Beeba kam langwashe murya tayi tace “Good Afternoon Sir ……!

Ware baki tayi tace “Beebah!Uban wa ya had’aki da number Ya Ma’aruf……?

K’aramin tsaki Beeba taja tana fad’in “Dadina dake Sumayya ke banza ce!Idan ba dalili ba me zanyi da number mijinki?kinga ni kin hutar dani dama yanzu zance ya baki zanyi magana dake !

Cikin d’aga murya tace “To ni me ya sami wayana da baraki kira ba?

Tsaki ta kuma ja tana hararan wayar tace “Kinga karki man ihu akai!Na kira wayanki Not reachable,ki zo ki karbi magani yanzu aka kawo man idan kuma bakya bukata nace ta tafi……”

Kwantar da murya tayi tana fad’in “Hoo My Beeba wallahi kin kayar man da gaba!amm……”Kife wayar tayi tana kallon Ma’aruf da ke tsaye bakin kofa yana kallonta……

A Hankali ya tako ya mika mata hannu “Da wa kike waya?
A Hankali ta mika mashi wayan tana fad’in “Beeba ce……”

“A wayana kuma?。

。Gyada mashi kai tayi a hankali……

“Ke kika kiranta?ya fad’a yana fiddo idanu
“Ita ta kira……”
“Ok……”Wayar ya fara dubawa!A Hankali ya dago yana kallonta tare da nunota da wayar yana lumshe mata da ido……Ganin Number beeba ce ya sata gyada mashi kai ……
“Karta kuma kirana……!ya fad’a kai tsaye
Shiru ta masa tana fad’in “Sae kace ba kai take gyara mawa ba……”Cikin gunguni……
Harara ya sakar mata ya fita dakin ya iske K’arama ta sata TV gaba kamar zata mayar da ita ciki!
“Muje ki dauko kayanki masu dauda……”Ya fada tare da nufar kofar dakinta……

Gabanshi ta sha tana waro ido tace “Ayi me dasu?

Kai tsaye yace “A Wanke maki!

“Tallahi babu mai wanke man kaya……”Ta fad’a tare da yin dakin da gudu ta hau tattara kayan ta tura karkashin gado!Tsaye yayi bakin kofar har ta gama turawa sannan ya karasa shiga ya dauko kayan yana hararanta!Kuka ta saki iya karfinta ta fadi kasa tana birgima!
Girgiza kai yayi ya fita da kayan ya bawa Mai wanki zannan ya dawo har lokacin tana kwance kasa tana birgima……

Kusa da ita ya tsugunna yace ……
“Wae anya kina Sallah ma……?
Kamar an mintsineta ta mike tsaye sannan tayi shige toilet ta fancalo alwalarta ta fito babu ko hijab ta kabbara sallah!Yana tsugunne amma tayi sallah yafi raka’a Sha biyu……
Tsayar da ita yayi yana fad’in “Wae Sallan ba zata k’are bane……”

A Cikin ruku’u tace “Har da ta gobe nake!
Shiru yayi yana kallonta har ta gama sannan tace “Na gama sallah Bunkul!Na cigaba da kukan?
Girgiza kai yayi yana fad’in “Ki bari sae anjima tukun……”
“To…amma Bunkul Waccen matar bata sallah fa…”ta fad’a a hankali tana kallon kofa
Banza ya mata ya mike ya shiga toilet ya hada mata ruwan wanka sannan ya kwala mata kira!bata dauka wanka zai mata ba ta shiga toilet din……
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button