JIDDAHTUL KHAIR 29

Abuturrab ya buda ido sosai yana kallon Abbansa gabansa na faduwa yace “Divorce kuma Abba?? Why will i do so bayan kayi instructing dina kar inyi haka? Ni ban saketa ba Abba ga ta ka tambayeta, idan na saketa ae baxa mu xauna tare ba.. ” Ba Aunty da ta bude baki tana kallonsa ba, har Jiddah kallonsa take da mamaki, Ummi dai wani direction din daban take kallo, Umma kam duk jikinta a sanyaye yake jin batun nan da ya tasheta da sassafe, Abba kansa ya kasa cewa komai, Aunty ta saki salati tace “Yaushe ka fara karya Abuturrab? Yaushe ka dawo makaryaci? Bakina da naka kace min ka saki yarinyar nan tun ranan da ku ka tare shine xaka karyata ni yanxu a nan?” Ya girgixa kai a hankali yace “Ban karyata ki ba Aunty, kawai na gaya maki haka ne saboda hankalinki ya kwanta tunda naga baki son auren, amma ni ban saketa ba, bana son abinda xai sa ki dinga damun kanki shi yasa na fada maki haka” Bude baki tayi tana kallonsa, yayi kasa da murya yace “Abba ga ta nan ku tambayeta ni ban saketa ba, I’m saying nothing but the truth” Jiddah ta sunkuyar da kanta daga kallon da take masa duk jikinta yayi sanyi, Abba kam ya ma rasa abun cewa, Can Ummi na kallon Jiddah tace “Jiddah” dago kai Jiddah tayi ta kalleta, Ummi tace “Ki fada min gaskiya Jiddah, Aliyu mijinki ne a yanxu ko ba mijin ki bane?” Gabanta ya dinga faduwa taji hawaye ya kawo idonta, Abuturrab ya gyara xamansa shi ma gabansa na faduwa sai dai bai kalleta ba, a hankali tace “Mijina ne Ummi” Aunty taji kamar ta rusa ihu a wajen lkci daya idonta yayi jajir, Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciyar relieve, Abba yace “Shkkn, Allah ya rufa asiri, u can leave now Aliyu” Abuturrab ya mike ba tare da ya kallesu ba yayi masu sallama, ita ma ta tashi ta sallamesu sannan ta bi bayansa tana goge hawayen idonta, Umma ta bi su da kallo xuciyarta na kokwanton amsan da Jiddah ta ba yar uwarta, this isn’t joking matter, she needs to investigate deep into this issue… Aunty ma ta bi su da wani kallo sai kawai ta saki kuka kamar warce aka sanar ma sakon mutuwa, ita Abuturrab xai
yaudara, ita xai karyata, ita xai watsa ma kasa a ido, ita xai kunyata gaban kowa?? Ko minti daya Abuturrab bai kara a a gidan nasu ba ya wuce da Jiddah, bai ce mata komai ba ita ma haka har suka iso gida bayan ya siyo masu abinci a hanya, parking yyi a compound dinsa, sai da ya sauka sannan ita ma ta sauka motar, ya mika mata ledan abincinta yana kallonta, kin amsa tayi hakan yasa yyi wucewarsa ciki da ledan ya bar ta tsaye a wajen, xaunawa yyi kan kujera a parlor ya jinginar da kansa da kujeran ya sauke ajiyar xuciya feeling relieved, sai bayan kusan minti sha biyar ta shigo parlon, xata wuce sama yace “Xo nan” Ta ki tsayawa har ta wuce, ya bude baki yana bin ta da kallo. Through out ranan jiddah na daki shi kuma yana downstairs, bai bi ta kanta ba har after isha, bayan ya dawo mosque ya dai ga alamar tayi making tea a kitchen, yana haurawa sama ya tsaya kofar dakinta sai kuma ya bude slowly, xaune ya ganta idonta yyi ja, ya kulle kofar dakin yana kallonta, yace “An maki wani abu ne kike ma mutane kuka tun safe?” Ta ki kallonsa, a d’an tsawace yace “Ba magana nake maki ba?” Ta juya masa baya, rungume hannu yyi yana kallonta, can yace “Kuka kike saboda kina tunanin kinyi musu karya?” Ta juyo tana kallonsa cikin rawan murya tace “Ehh mana, me yasa xa ka masu karya??” Yace “Ohh da na masu sai nace ke ma kiyi masu??” Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu, ya karasa ya tsaya gabanta yana kallonta da kyau yace “Ni ai ban aike ki kiyi masu karya ba… sannan akwai wani abu na musamman da ke sa mutane su yarda cewar mata da mijinta ne ke rayuwa a cikin gida? akwai wani abun da xanyi da xai tabbatar da cewar ni da ke mata da miji ne? Ko bana ciyar da ke yanda miji ke ciyar da matarsa ne? Ban baki sutura ba? ban baki wajen kwana ba? ban baki kariya ba? Ina ce duk wannan shine abinda miji ke ma matarsa? Ko akwai wani abu daban da ban sani ba ki sanar da ni nima in maki don xaman namu yayi kama da na mata da miji a daina xargin mu…” ta dauke kanta tace “Idan mun yaudari mutane ai Allah shi yasan gaskiya, kuma ai kai ma kasan ni ba matarka bace nima kuma nasan kai ba mijina bane” Kallonta kawai yake yace “Toh meye shaidan hakan?” Tace “Ai kai ma kasani, meyasa baxa ka fada masu gaskiya ba, sannan ni ka bani takardan in ajiye wajena tunda baka aikeni inyi karya ba” durkusawa yyi yana kallonta yace “Haba?” Tace “Ehh” yace “Toh ko dai in fara maki abinda masu aure ke yi, kilan hakan xai sa ki fara rage tunanin ai ni ba mijin ki bane, infact mancewa ma xaki yi cewar babu aure
tsakaninmu, takarda kuma da kika ce… Mu je in baki ki ajiye wajen ki” mikewa yayi still yana kallonta, ta k’i tashi, ya hade rai yace “Mu je ki amsa nace” mikewa tayi a hankali, ya nufi kofa ta bi bayansa xuwa bangarensa, suna isa ta tsaya bakin kofar babban parlon, ganin bata shigo ba yace “A bakin kofa xan baki takardan?” Shigowa parlon tayi taga ya nufi bedroom dinsa yana isa ya tsaya bakin kofa ganin bata karaso ba yace “Shigowa xa kiyi ai malama” daga haka ya shiga cikin dakin, a hankali ta bi bayansa tana shiga ya kulle kofar, ta makale jikin bango tana kallonsa, sanyi sosai ne a dakin sbda Ac dake aiki, ya nufi gaban mirrow ya dau diary dinsa ya bude sai ga takarda well folded ya ciro a ciki yana kallonta ya mika mata yace “Gashi” Ta sauke kanta kasa kamar baxata je ba sai kuma ta karasa ta sa hannu xata amshi takardan ya fixgota, kara tayi a tsorace ta fara kokarin kwace kanta, yace “Saboda ina tsoronki xan baki? And.. ina ruwanki da rashin auren dake tsakaninmu, ci kika rasa ko sha??” Gaba daya a tsorace take, kamar xata yi kuka tace “Kayi hakuri don Allah….” Yace “Baxan yi ba” a hankali ta daga kai ta kallesa, saketa yyi ya tafi gaban madubi ya ajiye takardan sannan yace “Idan kin isa ki dauka ki fita” Yana fadin haka ya nufi kofa ya bude ya fita ta bi sa da kallo har ya kulle kofar, a hankali ta isa gaban madubin ta dau takardan ta warware tana dubawa, takardan ne kuwa, in accord to the content of d paper, he is no longer her husband, duba diary din tayi taga ba a ciki ya falli takardan da yayi rubutun ba, wajen mirror din ta dinga dubawa nan taga takardan da ya cira a ciki, ita ma ta cira sannan ta mayar da sauri ta ajiye, linkewa tayi yanda ya linke na rubutun ta ajiye gaban madubin sannnan ta dau wanda rubutu ke jiki tana tunanin inda xata boye, kana ganinta kasan a tsorace take, hularta ta saka hannu ciki taji gashinta is very oily, ta sake ciran wani sabon takardan ta nannade na rubutun a ciki sannan ta tusa a cikin hulan ta koma inda take tsaye ta tsaya, bayan kusan minti goma sai ga shi ya shigo, sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tace “Kayi hakuri baxan sake cewa ka bani ba kuma” Bai ko kalleta ba, ya ajiye sauran bottle water din hannunsa, sannan yace “Aa ki dauka dai, gashi can gaban madubin” Ta girgixa masa kai kawai, gun takardan ya nufa gabanta ya dinga faduwa tana kallonsa ko kiftawa babu, ya dauka, bata jira taga me xai yi ba har ta juya xata fita da gudu taji yace “Gashi ki tafi da shi” Juyowa tayi tana xare ido taga yana mika mata takardan, kallonta kawai yake, yace “Amsa nace” Ta karasa a hankali ta sa hannu xata amsa ya murda kunnenta yace “Tahowa kika yi xa ki amsa kenan” Bata fuska tayi bata dai ce