NOVELSUncategorized
MUTUM DA DUNIYARSA 13

*_????HASKE WRITER’S ASSO…._*
*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
…………..Tunda ya shigo idonsa nakan Jiddah k’yam, duk da a kudundune take da hijjab hakan bai hanashi jin wani farin cikiba, haryay tuntu6e da gado kad’an yarage ya fad’i, yadai samu ya dafa gadon.????????
Ledar hannunsa ya ajiye saman dirowan gefen gadon kafin ya zauna a bakin gadon shima yana fad’in “Amarsu ta ango mai dad’in tuwo! Nidai abud’e fuska indai bakine nasayi abuna dubu d’ari kash”.
Jin Jiddah tayi shiru bata amsaba yakai hannu ya janye hijjabin, wani hucin zafine ya bigesa, yayinda sanyin AC kuma ya shigi Jiddah tahau kankame jikinta. ‘Dan canjawa fuskarsa tayi, yace, “K Jiddah tashi”..
Jiddah dake jinsa sama-sama tad’an bud’e idonta kad’an ta kalleshi, saikuma ta maida ta lumshe tare da k’ok’arin jan hijjabinta daya janye……
Tsawa ya daka mata, wadda tasata mik’e babu shiri, dama Jiddah akwai d’an banzan tsoro, dan haka jikinta keta k’yarma tana hawaye da karanto duk addu’ar datazo bakinta.
‘Dan sassauta fushinsa yayi ganin ta rud’e, ya kwantar da murya yana fad’in “Bakida lafiyane?”.
Kai ta d’aga masa alamar eh.
Shiru yay yana kallonta, danshifa gaskiya bazai iya hak’uri ba, yanda yay savise d’innan ace yatashi a banza ai akwai babbar matsala. Gyaran murya yad’anyi yakai hannu zai Kama nata, amma sai