LabaraiNetworking

Yadda Zaku Sayi 3GB A Naira N500 1.2.GB A Naira N200 A Layin Glo (Weekend Data)

Assalamu alaikum yan uwa barkan ku da sake kasancewa damu a wannan shafin LastNg kamar yadda muka saba kawo muku rubutu akan abubuwan da ya shafi garabasa matsalolin waya da layukan waya da sauran su.

Yau muna tafe muku da yadda zaku sayi data me sauki a layin Glo wannan datan zasu baku 3GB  ne a naira 500 sai kuma 2.2GB a naira 200.

Wanan datan zaka iya amfani dashi ne a weekend wato asabar da lahadi zai fara aiki shiyasa mukace bara mu muku rubutun yau juma a idan akwai me bukata saiya saya tun yanxu.

Wannan 3GB yana aiki ne ranar asabar da ranar lahadi shi kwana 2 suka bayar da za ayi amfani dashi.

Kaga daga 12 dare na ranar juma a datan zai fara aiki har sai 12 na ranar litinin.

Wannan kuma  1.2GB din shi kwana daya ne yake yi iya lahadi zaku iya amfani dashi da 12 daren ranan lahadi zai fara aiki zuwa 12 daren ranar litinin.

Yadda Zaku Sayi Datan

Da farko ya kasance kanada layin glo kowani layi yana yi abun baya zaban layi ko 3g ko 4g network ne zaiyi.

Idan ka samu layin naka ka sanya cikin wayar ka saika sa masa katin 500 ko 200 duk wanda kake bukatar saya.

Bayan ka saka katin saika danna #777* saika zabi 1 bayan ya bude saika sake zaban 1 saika sake zaban 1 ko 2 idan kana son auto renew bayan nan saika zabi 7 Night And Weekend Plan, 

Kuna danna 7 din zai nuna muku adadin datan idan zaku sayi na 1.2GB saiku zabi number 4.

Zaku ga sun baku kamar haka.

Idan kuma zaku sayi 3GB saiku zabi number 5.

Shima zaku ga sun baku datan saiku cigaba da amfani dashi.

Ku tura zuwa ga abokan ku

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button