__ LOKACIN da wadannan ALJANU na HASKE keta saran jikin su YARIMA LUBAINU,JINI na tsartuwa da feshi,shi kuma BOKA DARBUSA nata fama rusa dariyar mugunta da farin ciki,sai gaba dayansu su ukun suka zube kasa saboda jira sakamakon jinin dake zuba a jikinsu.Har mugayen fadawan na Boka Darbusa sun yunkura zasu karasa kashesu suyi musu KISAN GILLAH sai ga wani babban HADIMI na boka Darbusa ya shigo cikin fadar a firgice kuma a guje har yana tuntube,kuma yana mai kwallawa boka Darbusa kira.Al’amarin daya janyo hanakakin Boka Darbusa kenan da mugayen fadawan nasa suka juya izuwa kan hadimin suka kura masa idanu.Da isowar Hadimin sai ya zube kasa a gaban boka Darbusa yana haki kamar ransa zai fita,sai da numfashinsa ya dan dawo daidai sannnan ya iya budar baki yace,ya shugabana ga wani takadirin MAHAYI can ya durfafo wannan gida naka bisa wani BAKIN DOKI kuma sanye da FARAREN TUFAFI,ya rufe jikinsa da fuskarsa gaba daya,kuma yana rataye da wata zabgegiyar TAKOBI a bayansa.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Boka Darbusa,saboda a iya zamansa a cikin wannan DAJI babu wani mahaluki walau MUTUM ko ALJAN daya taba durfafo hanyar wannan gida nasa da tsawon kwanaki uku kafin isowarsa ba tare da ya sani ba,koma yasan ko wane ne,da kuma dalilin zuwansa,sai a wannan karon.Cikin alamun tsananin fushi da kaduwa boka Darbusa ya dubi wadannan fadawan nasa wato Aljanu na haske yace ku biyo ni a baya muje mu hallaka wannan shaidanin bil’adama daya tunkaromu,domin koma wane shi nasan cewa MAKIYINmu ne.Koda gama fadin hakan sai Boka Darbusa ya zare takobinsa take wadansu bakaken DAWAKAN TSAFI na haske suka baiyana a gabansa.Kawai sai shida mugayen fadawan nasa suka haye dawakan.Cikin gaggawa wannan babban hadimin ya dubi Boka Darbusa yace,ya shugabana yanzu ya zamuyi da wadannan ABOKAN GABA namu su uku?Koda jin wannan tambaya sai Boka Darbusa ya dubi su Jarumi Lubainu wadanda ke kwance cikin jini,kuma rai a hannun Allah,ya bushe da dariyar mugunta yace,ai wannan gawa ce kawai taki rami,nan da dan kankanin lokaci duk zasu zama gawa tunda babu wanda zai kawo musu dauki a cikin halin da suke ciki sakamakon wannan jini dake zuba a jikinsu babu wanda zai tsira da rayuwarsa a cikinsu.Koda gama fadin hakan sai Boka Darbusa da wadannan mugayen aljanu nasa sa dawakan da suke kai duk suka bace bat!daga cikin fadar. Bacewarsu keda wuya sai wanann babban hadimi na boka Darbusa ya dubi su SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA ya bushe da dariyar mugunta yace,yanzu ku in banda wauta irin taku wane tsautsayi ne zaisa kuyi gangancin zuwa nan gidan domin ku dauki ALLON SIHIRIN shugabana? Tabbas biyu babu zakuui yanzu babu biyan bukata kuma babu rayuwarku.Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi hadimin cikin karfin haki tace ina farin cikin zan mutu a matsayun jarumar data sami nasarar shigowa har nan cikin fadar shugabanka,kuma nayi yaki da dakarunsa,amma ina da wata alfarma guda daya da nake son kayi min ita bayan mutuwata.Ka taimaka ka matso kusa na rada maka wannan alfarma saboda bana son kowa yaji.Koda sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai hadimin ya sake bushewa da dariyar mugunta a karo na biyu sannan ya matso kusa da sarauniya Akisatul Sauwara ya tsugunna a daidai fuskarta domin tayi masa rada a kunnensa.Sarauniya Akisatul Sauwara ta yunkura kamar zata gaya masa magana a kunnesa sai ta shammaceshi cikin bakin zafin nama ta zaro sharbebiyar wuka a kugunsa ta cala masa ita a KAHON ZUCIYA!!!Nan take hadimin ya kurma uban ihu a lokacin da jini yai feshi ta cikin kirjinsa ya sulale kasa matacce.Koda ganin abinda ya faru sai ragowar dakarun dake cikin fadar suka rugo da gudu izuwa kan sarauniya Akisatul Sauwara,kawai sai gani akayi ta mike zumbur!ta yagi rigar jikinta ta daure babban raunin dake kan cinyarta sanna ta daka tsalle can gefe daya izuwa inda takobinta take ta sureta ta sake daka tsalle sama ta dira a tsakiyar dakarun ta hausu da SARA DA SUKA.Nan da nan kuwa ta rinka ragargazarsu tana zubar dasu kasa matattu. Koda Sarki Darmanu da Yarima Lubainu sukaga irin jarimtakar da Sarauniya Akisatul Sauwara takeyi sai suma suka yunkura cikin tsananin juriya suka kama daure raunikan jikinsu suka mike tsaye suka kaiwa sarauniya Akisatul Sauwara Dauki aka sake ruguntsumewa da sabon masifaffen yaki. A¤A¤¤H¤A¤D¤A¤H¤A¤D¤A A CAN WAJEN gidan boka Darbusa kuwa lokacin da wannan BAQON JARUMI ya durfafo kofar gidan sai yaja linzamin dokinsa ya tsaye cak,sakamakon ganin Boka Darbusa da mukarrabansa.Nan da aka tsaya ana kallon kallo tsakanin Boka Darbusa da Bakon jarumin. Daga can sai Boka Darbusa ya budi baki yace yakai bakon jarumi wane ne kai,kuma menene ya kawoka wannan daji harka durfafo wannan gida nawa? Koda jin wannan tambaya sai Bakon Jarumin yayi shiru baice komai ba,kawai sai ya sauko daga kan dokinsa ya zare takobinsa daga cikin kufe.Koda ganin haka sai Dakarun Boka Darbusa ma suka zare nasu Takubban saboda a zatonsu yakarsu zaiyi. Kawai sai sukaga ya kama zane akan kasa da tsinin takobinsa ya rubuta KALMAR SHAHADA,gami da bayanin cewa yazo ne ya yada ADDININ MUSULUNCI a wannan nahiya.Koda ganin hakan sai Boka Darbusa ya fusata ainun ya dakawa bakon jarumin tsawaya yace kai kurmane da bazaka budi baki kayi magana ba,kuma mummunar fuska gareka da harda kake boyeta? Koda jin wannan tambaya sai bakon jarumin ya tafa hannunsa sau uku,faruwar hakan keda wuya sai ga wani dan guntun mutum ya fito daga cikin daji da gudun tsiya tamkar tashi sama yakeyi. Karfin gudun nasa ya cika abin al’ajabi.Da zu wan wannan dan wada gaban bakon jarumin sai ya risina yayi gaisuwa yace me kake da bukata? Take bakon jarumin yayi masa magana cikin yaren kurame,wato da hannu yayi masa magana.Nan take dan wadan ya fahimta sannan yajuya ga Boka Darbusa yace,ni Sunana DAZYAN kum na kasance bawa ga wannan bakon jarumi dake gabanku! Ku sani cewa maigidana ba kurma bane,kuma yana boye muryarsa da fuskarsa ne saboda wani sirri da ba lallai bane ba ku sanshi,amma dai kamar yadda yayi muki bayani mu baki ne daga wata nahiya daban,kuma munzo ne domin mu gabatar muku da addininmu wanda ake kira da ADDININ MUSULUNCI! kuma shine ADDININ GASKIYA.Addinin daku ke kansa na BAUTAR GUMAKA gami da ALJANU da TSAFI duk shirka ne kuma bata ne mabayyani!! Koda dan wada yazo nan a zancensa sai Boka Darbusa ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa ya dubeshi cikin alamun tsananin fushi yace tabbas kai da maigidan naka kun cika wawaye,kuma marasa hankali da tunani harda kuke tunanin cewa zaku zo mana da SABON ADDINI kuma mu karbeshi alhalin mun saba da addininmi tun IYAYE da KAKANNI!!! Tabbas kun kawo kanku GIDAN MUTUWA,kuma bama ku ba hatta ire irenku ma sai sunyi nadamar zuwa wannan nahiya tamu,kuma yanzun nan zansa a yi muku kisan wulakanci irin wanda ko a tarihi ba’a taba yin kamarsa ba a ko ina a cikin wannan duniya.Koda gama fadin hakan sai Boka Darbusa ya dubi wadannan Aljanun haske dake kewaye dashi yayi musu wata inkiya.Nan take su duka suka sakarwa dawakansu linzami suka zaburesu da gudu izuwa kan Dazyan da maigidansa bakon jarumi.Koda Dazyan ya hangosu sun yiyo kansu sai ya daka tsalle sama ya dane kan wani bishiya mai tsawon gaske yana mai motsa bakinsa alamar cewa yana karanta wata addu’a ne ta neman tsari.Shi kuwa maigidan nasa bakon Jarumi sai ya daka tsalle sama ya haye kan dokin nasa tamkar daukarsa kayi aka ajiyeshi akan dokin sannan ya daga takobinsa sama yana mai kwallah KABBARA ya tunkari aljanun.Ai kuwa tun kafin ma su hadu aljanun hasken da dawakan nasu suka firgice suka razana ainun saboda tasirin wannan kabbara da bakon jarumin yayi.Ai kuwa suna haduwa aka ruguntsume da AZABABBEN YAKI mai tsananin tayar da hankali,sai gashi bakon jarumin yana tsarge wadannan aljanun haske da dawakan nasu suna zubewa kasa matattu sun kamawa da wuta su kone kurmus,saidai kaga iska na diban tokarsu.Koda Boka Darbusa yaga yadda Bakon Jarumin yake yi masa mummunar barna sai ya fusata ainun kuma yasha JININ JIKINsa ya tabbatar da cewar lallai wannan bakon jarumi ba kanwar lasa bane,tsafi bazaiyi tasiri akan sa ba.Amma da yake Boka Darbusa ya yarda da kansa akan jarumtakarsa da KARFIN DANTSE Sai kawai shima ya zare takobinsa kuma ya sauko daga kan tsafaffen dokin nasa take dokin ya bace bat! shi kuma sai ya falfala da gudu izuwa kan bakon jarumin.Koda ya rage baifi saura taku goma ba tsakaninsu sai Boka Darbusa ya daka tsalle sama tamkar an cillashi daga cikin Baka ya kaiwa bakon jarumin mummunan sara a wuya da nufin ya cisge masa kai.Cikin tsananin bakin zafin nama Bakon Jarumin ya daga tasa takobin ya kare saran,amma saboda karfin saran saida ya kusan tuje rawanin bakon jarumin.koda ganin haka sai bakon jarumin ya fusata ainun kawai sai shima ya daka tsalle ta baya akan dokin yayi wata irin alkafira ta ban al’ajabi.Hatta wannan dan wada nasa wato Dazyan daya buya a can sama bishiya bai san sa’adda yayi masa tafi ba saboda ganin irin wannan gagarumar BAJINTA da yayi. Bakon jarumin ba sama shima ya maida martanin saran da Boka Darbusa ya kawo masa adazu.Sai gashi shi nasa saran ma yafi na Boka Darbusa nauyi da karfi,don har saida Boka Darbusa ya durkushe kasa bisa gwiwarsa guda kuma sai da kaifin takobin ta farka rigar Boka Darbusa.Al’amarin dayasa Boka Darbusa yayi wuf ya mike tsaye kenan yana mai gyara tsayuwa yana mamki saboda tunda yake GUMURZU da MANYAN MAZAJE bai taba haduwa da mai karfin damtse da iya yaki kamar wannan bakon jarumi ba.Saidai wani abu ya jefashi cikin wasi wasi ba komai bane ya jefashi cikin wasi wasin va face duk sa’adda ya dubi wannan bako jarumin sai yaga surar jikinsa tana kama data MATA,amma kuma idan yayi la’akari da irin zafin namansa da kuma KARFIN DAMTSENsa sai yaga cewa babu yadda za’ayi ya kasance ‘YA MACE.Nan take Boka Darbusa ya aiyana a cikin ransa cewa duk yadda zaiyi sai yaga fuskar wannan bakon jarumi ko da kuwa bazai sami nasarar hallakashi ba.Bayan anyi kallon kallo na tsawon yan dakiku tsakanin Boka Darbusa da Bakon Jarumin sai suka rugo da gudu a lokaci guda izuwa kan juna,suna haduwa kuwa suka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwatance ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama,juriya da jarumtaka. Saidai suka shafe kusan rabin sa’a suna wannan BAKIN ARTABU ba tare da dayansu ya sami nasara ba. Koda bakon jarumin yaga Boka Darbusa na neman bata masa lokaci sai ya sauya salon fada ya hada da kai naushi da bugu ta ko ina kuma yana tsalle tsalle da kwance kwance.Ai kuwa nan da nan ya rikirkita Boka Darbusa har ya sami nasarar gabza masa mugayen naushi guda uku a fuska.take Hancin Boka Darbusa da bakinsa suka kama yoyon jini,kuma idanunsa suka kumbura sukayi suntum!Haka suka ci gaba da kwabsa wannan masifaffen yaki mai tsananin muni da tayar da hankali a tsakaninsu,tun Boka Darbusa yana iya kare naushi da bugun da bakon jarumin yake kawo masa har ya gaza balle ya samu damar mayar da martani. Ana cikin hakane bakon jarumin ya shammaci Boka Darbusa ya daka tsalle masa ya doki fuskarsa da kafa.Saboda karfin dukan saida Boka Darbusa yayi katantanwa sau uku a tsaye kuma take hakorinsa guda na sama ya yi fitar burgu daga cikin bakinsa tare da Wani GUDAN JINI,saboda tsanani zafi da zogin dayaji saida yaga taurarin wuya a cikin idanunsa a lokacin daya kife kasa,kuma yaji kansa ya kara girma yana neman rinjayar gangar jikinsa. Koda Boka Darbusa ya tabbatar da cewar wannan bakon jarumi ya fishi karfin damtse nesa ba kusa ba,kuma yafi shi iya yaki,sai ya mike tsaye zumbur,cikin matukar karfin hali da numa ‘ki fadi,kamar cigaba zaiyi da yaki,amma sai ya juya da baya ya falfala da gudu izuwa cikin daji kamar dunduniyar kafarsa zata tabo keyarsa saboda karfin gudun.Koda ganin abinda ya faru sai dan wada Dazyan ya sauko daga kan doguwar bishiyar da yake kai ya ruga izuwa gaban bakon jarumin ya shiga yi masa kirari yana cewa,Ga ‘ki gudu maganin sa gudu!!Ga mai dogaro da Allah,dodon kafirai.Koda jin wannan kirari sai bakon jarumin ya dagawa Dazyan hannu yana mai yi masa nuni da yai shiru,kawai sai ya nufi cikin gidan Boka Darbusa da sauri,shima Dazyan sai ya bishi da sauri. Nima ganin Boka Darbusa ya gudu,sannan Bakon Jarumin ya nufi gidan Boka Darbusa yasa nima nabi bayansa. Zan dakata anan dafatan yayi. pls Like nd comments idan naga yamin Anjima sainayimuku post din 3b 7 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na Uku (3) Part B A CAN FADAR Boka Darbusa kuwa bayan an shafe kusan rabin sa’a ana gumurzun yaki tsakanin su Yarima Lubainu da dakarun dake cikin fadar,su Lubainu nata samun nasara suna ta ragargazar dakarun saida suka karar dasu gaba daya.A lokacin ne suka gaji likis don haka sai suka zube kasa suna haki da numfarfashi kamar ransu zai fita.Faruwar hakan keda wuya sai suka ji takun sawaye da yawa daga can wasu bangarori na gidan da yawa ana rugowa izuwa inda suke.Al’amarin dayai matukar firgitasu kenan suke mimmike tsaye a tsorace,kafin suyi wani yunkuri sai ga wadansu samudawan dakarun mutane masu kirar MUTANEN FARKO,rike da mugayen makamai suna ta tuttudowa cikin fadar ta gabas da yamma,kudu da arewa,su da yawa ba adadi.Nan da nan suka yiwa su Yarima Lubainu KAWANYA.Koda ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta yarda takobinta,ta dubi sarki Darmanu da Yarima Lubainu cikin alamun karayar zuciya tace,ai shike nan kuma tamu ta kare,domin babu yadda zamu iya kare kanmu daga sharrin wadannan dakaru a wannan yanayi da muke ciki.Babu wani karfin dantse ko na Sihiri dazai cecemu.A yanzu duk burinmu ya rushe,kuma karshen rayuwarmu yazo,saidai mu rungumi kaddara.Idan muka ce zamu yaki wadannan dakaru ma zamu bata karfinmu ne a banza ba tare da mun samu koda nasarar sisi a kansu ba.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai jikin Yarima Lubainu dana Sarki Darmanu yayi sanyi,take shima Sarki Darmanu ya yarda takobin hannunsa,shima Yarima Lubainu har ya yunkura zai yarda takobinsa sai ya fasa yace kai! Aida dai na mutu RAGO gwara na mutu JARUMI,tsakanin mutum da sa’a da rabo,mutuwa ce don haka dole ne na jarraba sa’ata.Yana gama fadin hakan sai ya daga takobinsa sama ya riketa da hannu biyu.Koda ganin haka sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar mugunta yace,kai yaro hakika ganganci ne ya kawoku nan gidan domin babu abinda zaku samu face AJALINku.Koda gama fadin hakan sai shugaban dakarun ya daga hannunsa sama ya bayar da inkiyar a afkawa su Yarima Lubainu.Kafin daya daga cikin dakarun nasa yayi wani yunkuri sai aka jiyo KABBARA ta cika fadar gaba dya.Take kowa ya waiga baya izuwa inda sautin kabbarar ya fito,kawai sai aka hango BAQON JARUMI rike da takobinsa ya falfalo da azababben gudu,tazarar dake tsakaninsa da wadannan dubban samudawan dakaru yakai taku ashirin amma daua daka tsalle guda daya sai gashi ya fado a tsakiyarsu ya hausu da sara da suka.Nanfa ya tarwatsasu shi kadai ya zame musu GUGUWAR ANNOBA.Da zarar sun yunkuro da nufin su yanyameshi sai kaga ya tarwatsasu yana filfilawa a kasansu da samansu tamkar katantanawa ake murza wa,kuma duk inda yakai sara guda sai dai kaga Mazaje sama da arba’in sun zube kasa Matattu.Koda su Sarauniya Akisatul Sauwara sukaga wannan gagarumar jarumtaka ta ban al’ajabi wacce tafi gaban hankalinsu da tunaninsu sai suka cika da tsananin mamaki suka zazzaro idanu suka zubawa sarautar Allah idanu kawai.Nanfa YAKI ya kara TSAMARI ya zamana cewa dakarun sun fusata ainun suna dada afkawa bakon jarumin ta ko ina da dukkan karfinsu suna kai masa sara da suka,duk da cewa ragargazarsu bakon jarumin yake,JINI na feshi da fantsama kuma sassan jikinsu na yawo a sama yana zubowa kasa suna ihu da kururuwa suna zubewa kasa.Saida aka shafe sa’a biyu da rabi ana wannan mummunan azababben yaki daya daga cikin dakarun bai sami nasarar koda kwarzanar jikin bakon jarumin ba,kuma basu ga ya gajiya ba.Cigaba yake da ragargazarsu kawai amma saboda tsananin yawansu sai kaga kamar karuwa sukeyi.Duk wannan abu dake faruwa dan wada Dazyan ya shige karkashin wani tebur ya buya yana morewa idanunsa kallo,kuma yana karanta addu’ar neman tsari don kada tsautsayi ya haushi domin shi a rayuwarsa ko rike takobi bai taba yi ba bare ya iya yaki ko ya kare kansa.Haka dai aka cigaba da wannan mugun azababben yaki har aka sake shafe wata sa’ar gudu,a sannan ne fa samudawan dakarun suka gane cewa SHAYI RUWA NE!Domin tuni bakon jarumin ya gama kashe kaso biyu cikin kaso ukinsu.Wadanda basu mutu ba kuwa sun zama nakasassu,wasu sun rasa kafafu,wasu hannaye,aki wasu ma sai kaga an zabtare rabin kafadarsu,tsabar taurin rai ne yasa basu mutu ba.Koda ragowar samudawan dakarun suka tabbatar da cewar lallai bazasu iya kashe wannan takadirin jarumi ba,kuma indai aka cigaba da wannan yaki sai ya karar dasu gaba dayansu sai suka ciki wandunansu da iska suka bar ragowar nakasassun a wajen.Nan take fadar tayi tsit,tamkar babu wani mahaluki mai numfashi a cikinta,kuma sai aka fara kallon kallo tsakanin bakon jarumin dasu Yarima Lubainu.Shi kuwa dan wada Dazyan ya fito daga inda yake boye ya tsaya a bayan bakon jarumin yana murmushi gami da karkade kurar jikinsa sakamakon kurar data baibaye masa jiki saboda a lokacin da bakon jarumin yake yaki da wadannan samudawan dakaru,sun ragargaje duk wani abu mai amfani dake cikin fadar an tashi ‘kura mai yawa.Bayna anyi kallon kallo tsakanin bakon Jarumin dasu Sarauniya Akisatul Sauwara sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta tako kafafunta ta matso kusa da bakon Jarumin ta dubeshi tace wanene kai kuma menene dalilin dayasa ka ceci rayuwarmu?Koda jin wannan tambaya sai bakon jarumin ya dubi Dazyan shi kuma sai ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara ya risina a gareta cikin alamun girmamawa yace,yaku wadannan jarumai guda uku,kuyi sani cewa shugabana baya magana ba don ya kasance kurma ba,kuma ya rufe fuskarsa ba don bashi da kyau ba,saboda wani babban sirri ne yasa yake aikata hakan da fatan bazaku damu ba.Kuyi sani cewa mu baki ne daga wata nahiya dabam,kuma munzo nan nahiyar ne domin mu gabatar muku da Addinmu wanda ake kira ADDININ MUSLUNCI!ADDININ MUSULUNCI shine ADDININ GASKIYA,don haka duk wani addini da kukeyi walau na BAUTAR GUMAKA ko RANA ko WATA ko ALJANU duk bata ne mabayyani!!!Tsafi shima shirka ne babba saboda haka muna kira agareku daku tuba ku bar wadannan addinai naku ku karbi namu.Ba komai ne yasa shugabana ya ceci rayuwarku ba face saboda ya fahimci cewa wannan Boka da kuke yaki dashi AZZALUMI ne kuma mushriki.Shin yanzu zaku karbi wannan Addini namu ne ko kuwa zaku bijire masa?Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu da Sarki Darmanu suka dubi junansu sukayi shiru aka rasa wanda zaice kala.Daga can sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi gyaran murya sannan ta dubi dan wada Dazyan tace,yakai wannan gutun mutum…”Koda jin haka sai Dazyan ya turbune fuskarsa kuma ya tari numfashin Sarauniya Akisatul Sauwara yace ke yarinya kada kici min fuska ko kiyi min rashin kunya.Ki sani cewa na haifi kamarki don haka bai kamata ki kirani da dan guntu ba!!!Koda jin haka sai Sarauniya Akisatuk Sauwara ta risina cikin biyayya tace,k gafarceni amma bansan sunan da yakamata na kiraka dashi bane.Dan wada Dazyan yace sunana na yanka shine DAZYAN! Amma ana kirana da ABUL YAZRIN.Sarauniya Akisatul Sauwara tace,daga yau nayi alkawarin zan rinka kiranka da Abul Yazrin don girmamawa.Ka gayawa mai gidanka cewa muna bukatar cikakkiyar hujja wacce zata sa mu gamsu da cewa lallai wannan addini dakukazo dashi shine ADDININ GASKIYA.Baya ga haka kuma muna bukatar muyi nazari da shawara domin mu sanar dakai abinda muke ganin zaisa mu sami nutsuwa da yarda akan wannan sabon addini naku.Koda jin wannna batu sai Bakon Jarumin ya dubi Dazyan yayi masa zance da hannu.Dazyan ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana yace yaki bayananku,kuma ya aminta da duk uzurin dakukazo dashi amma kuma yana son yasa abu guda biyu a tare daku.Abu na farko da yake son sani shine shin me ya kawo ku nan gidan har yaki ya barke tsakaninku da wannan Boka?Abu na biyu kuma shine yana son yasan iya tsawon lokacin dazaku yanke shawara da kuma abinda kuke son yayi muku wanda zaisa ku gamsu cewa addininsa shine ADDININ GASKIYA?Ya ce na gargadeku akan cewa ku tabbatar da cewar duk abinda zaku fada masa ku fadi iyakar gaskiya,in ba haka ba kuwa bazai sake taimakonku ba kuma zaku iya zama ABOKAN GABA a gareshi!!Kuma yace a sanar daku cewa har yanzu fa baku tsira daga sharrin wannan Boka ba,domin ba mutuwa yayi ba guduwa yayi,babu mamaki ma yana nan a labe wani wurin yana fakonku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa sai Hankalin Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu ya dugunzuma ainun,sukayi tsuru tsuru suna kallon junansu suka kasa cewa uffan.Kawai sai Sarauniya Akisatul Sauwara taja su izuwa can gefe daya inda su Bakon Jarumin basu ji abinda zasu tattauna ba.Cikin nutsuwa Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu da Yarima Lubainu tace me kuke ganin ya kamata muce da wannan hatsabibin bakon jarumi?Kowannenmu ya ga irin tsantsar jarumtakarsa ta ban al’ajabi.Tabbas idan muka yi kuskuren yi masa karya ko yaudara zamu iya yin nadama.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya numfasa yace ai dama tun kafin na baro gida na dauki alkawaron cewa bazanyi karya ba,kuma bazanci amana ba,sannan zan zamo mai cika alkawari saboda haka idan kun amince zan wakilceku naje na yiwa wannan bakon Jarumi bayanin komai bisa gaskiyar al’amarin kuma mu nemi taimakonsa bisa hada wannan ALLON SIHIRI tunda a yanzu haka bamu san a inda Boka Darbusa ya boye nasa ALLON SIHRIN ba kuma bamu san irin tsaron da ya bashi ba bare har mu iya daukoshi.To amma fa akwai matsala guda daya,a tsakaninmu mu ukun nan babu wanda yasan abinda kowannenmu ya shirya a zuciyarsa.Babu mamaki bayan an hada ALLON SIHIRI dayanmu ya shammaci sauran ya cutar dasu ya gudu da ALLON SIHIRIN don cika burinsa shi kadai tunda dole dai mutum daya ne daga cikinmu zai iya cika burinsa a lokaci guda,kuma dole sai yana tare da ALLON SIHIRI zai iya kammala sauran aikin cikia burin nasa.Lokacin da Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka dubi juna kowannensu yai shiru aka rasa wanda zaice kala.Daga can sai Sarki Darmanu yace kai yaro ne tayaya zamu hadu da mutum a yau dinnan rana daya jal,kuma mu saki jikinmu dashi har mu gaya masa sirrinmu?Shin baka tsoron cewa zai iya cutar damu ko kuma yayi amfani da sirrin namu sami Damai-Akala?Kawai muyi amfani dashi wajen cika burinmu in yaso mu a tsakaninmu mu sasanta yadda kowa zai amfana.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace tabbas kazo da shawara mafi alheri,shi kuwa Yarima Lubainu sai ransa ya baci ya dubesu su biyun yace,ni kam daga yanzu na fita daga cikinku domin bazan iya baku yarda da amanata ba,tunda har zaku iya yin karya da yaudara,gwara na baiwa wannan bakon jarumin amincina saboda akwai alamun cewa zaifiku iya rike amanata.Koda gama fadin hakan sai Yarima Lubainu ya juya ya bar wajen su Sarki Darmanu ya nufi inda Bakon Jarumin da dan wada Dazyan ke tsaye.Koda ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta ruga izuwa gareshi tasha gabansa tace haba yakai wannan dan Sarki,ka tuna irin halaccin danayi maka lokacin dakazo gareni bisa neman taimakona.Ka tuna yadda na dauko ALLON SIHIRI NA kuma na biyoka a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske don kawai na taimake ka ka sami nasarar samo lafiyar jikinka ka koma ga matarka kuma masoyiyarka YAZARINA?Idan ka tarwatsa mini nawa shirin saboda cikar burinka kaci amanata kuma ka nuna mini cewa kai ba dan Halak bane!Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo daidai nan a zancenta sai Jikin Yarima Lubainu yayi sanyi kuma hankalinsa ya dugunzuma har idanunsa suka dan ciko da kwallah,amma daya sake tuno da nasihar da aka bashi kafin ya baro gida ta rike gaskiya,amana da alkawari sai ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,kiyi hakuri akan fadin gaskiay saidai kice naci amanarki.Yana gama fadin hakan ya tunkari bakon jarumin gadan gadan yana shirin ya isa daf dashi sai dan wada Dazyan yai sauri ya shiga tsakiyarsu ya dubeshi a fusace yace,doka ta farko ba a kusantar maigidana don yin magana dashi.Na gaya muku cewa ba kurma bane ba,don haka ko daga nesa zaka iya fadin duk abinda kakeson fada masa.Koda jin haka sai Yarima Lubainu yayi murmushi yace hakikanin gaskiya ni neman magani ne ya fito dani daga kasarmu.Nan take Yarima Lubainu ya kwashe labarinsa kaf ya zayyane bai boye komai ba harda batun soyayyarsa da YAZARINA wacce ta haddasa gaba a tsakaninsa da abokinsa YARIMA MANGUL har sukayi gasar neman aurenta ta hanyar yakar juna ya cirewa Yarima Mangul hannun daya shi kuma yayi masa asiri ya kashe masa Mazakuta.Yarima Lubainu ya cigaba da bayani akan fitowar da yayi don neman ALLON SIHIRI ya karantashi don ya gano inda KOGIN BAHAR IMFAL yake yaje cikinsa ya tsinko dan itaciyar da zata warkar da wannan cuta tasa domin ya koma gida a matsayin Namiji lafiyayye yaci gaba da ZAMAN AURE da masoyiyarsa YazarinaLokacin da Yarima Lubainu yazo nan a labarinsa sai bakon Jarumin da Dazyan suka ji sun kamu da tsananin tausayinsa.Bakon Jarumin yayi shiru yana tunani da nazari izuwa tsawon dan dakiku kadan sannan ya dubi Dazyan yayi masa zancen kurame.A Sannan ne Sarki Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara suka taho garesu da sauri domin suji abinda bakon jarumin zaice.Dazyan yayi gyaran murya sannan yace,yakai wannan dan sarki kayi sani cewa shugabana yace inda zaka yi imani da UBANGIJIN MUSULUNCI ka karbi addininmu zaka iya samu lafiyarka a rana guda a cikin dakika guda daya ma jal ka yankewa kanwa duk wahalar dake gabanka.To amma ya fuskanci cewa zuciyarka da ta wadannan Abokan Gaba tana da rauni akan yin imani da ubangijin musulunci saboda kun yarda da Addinin iyayenku da kakanninku,kuma kuna gani kamar addinin naku shine addinin gaskiya,saboda kuga zahiri kuma ku gamsu cewar addinin musulunci shine na gaskiya mafin inganci da daraja akan naku,shugabana ya amince zai ci gaba dayin wannan tafiya tare daku amma duk inda akaje zai barku ku jarraba kafin sihirinku da na damtsenku wajen ganin cewa kun kawar da kowacce irin masifa da aka riska sai bayan kun kasa sannan shi ya kawar da masifar da taimakon ubangijin musulunci,amma fa sai idan kun dauki alkawarin cewar bayan anzo karshen tafiyar zakuyi imani da addinin musulunci,idan kuma baku yarda ba da wannan sharadi ba,to zai cigaba da binku kawai a cikin wannan tafiya ya zaman dan kallo ba tare daya taimaka muku da komai ba.Koda Dazyan yazo nan a jawabinsa sai hankali Sarki Darmanu dana Sarauniya Akisatul Sauwara ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe suka rasa abinda yake musu dadi a duniya,shi kuwa Yarima Lubainu sai farin ciki ya lullubeshi ya dubi bakon jarumin cikin murmushi yace tabbas ni na yarda da wannan sharadi naka.Koda jin hakan sai Bakon Jarumin yayi maganar kurame ga Dazyan shi kuma Dazyan sai ya dubi Yarima Lubainu yace mai gidana yana murna dajin bayaninka.Dazyan ya juya ya dubi Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara yace,maigidana yace ki kuma fa menene ra’ayinku? Cikin rawar murya da tuntuben harshe Sarauniya Akisatul Sauwara tace babu matsala muma mun amince da sharadin maigidanka to amma yanzu yaza ayi akan batun ALLON SIHIRIN Boka Darbusa wanda mukazo nema a cikin gidansa? pls Like nd comments 15 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na uku (3) Part C Batun ALLON SIHIRIN Boka Darbusa wanda mukazo nema yanzu a cikin gidansa.Koda jin wannan tambaya sai Bakon Jarumin ya dubi Dazyan ya sake yi masa zancen kurame da hannu.Dazyan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana yace yanzu zamu bazama neman wannan ALLON SIHIRI a cikin wannan gida,amma ku ukun ne zaku fara neman ALLON SIHIRIN da karfinku sihirinku,idan kuka kasa sai mu roki ubangijinmu ya nuna mana inda yake mu daukeshi da izininsa mu baku.Koda gama fadin hakan sai Yarima Lubainu ya dubi su Sarauniya Akisatul Sauwara yace to kunji yanzu dai shawara ta rage ga mai shiga rijiya.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka dubi junansu sukayi murmushi kuma suka budi baki cikin hadin murya suka ce muma mun amince da hakan.Nan take Sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki Darmanu da Yarima Lubainu suka sake kunna kai izuwa cikin gidan Boka Darbusa kowannensu na karanta dalasiman tsafinsa a cikin ransa.Shi kuwa Bakon Jarumi da Bawansa Dazyan sai suka bisu a baya kawai suna kallonsu kuma suna neman tsarin Allah daga dukkan mugun abun dake cikin gidan.Abu dai kamar wasa saida su sarauniya Akisatul Sauwara suka shiga duk wani sako,lungu da dukkan dakunan dake gidan kuma suka caje komai da ko ina a cikin gidan amma har suka gaji likis ko alamar ALLON SIHIRI basu gani ba.Daga karshe ne suka ga wani daki mai katuwar bakar kofar karfe a kulle wanda ya rage basu shiga ba.Ita kanta kofar wannan daki ta isa abar tsoro domin anyi tane da mulmulallen karfe mai kaurin gaske,sannan akwai hoton KWARANGWAL din kan BIL’ADAMA da kafafuwansa a jikinta alamar cewa wannan daki,daki ne me mugun hadari wanda mutum zai iya rasa rayuwarsa a ciki.Koda sukayi arba da kofar wannan daki sai sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da sarki Darmanu suka dubi junansu sukayi cirko cirko suna kallon kofar.Kawai sai Sarki Darmanu ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace ai sai fara jarraba taki sa’ar mu gani.Ba tare da wata gardama ba kuwa sarauniya Akisatul Sauwara ta kama kofar taja da nufin ta budeta amma sai ta kasa kawai sai ta fara karanta wadansu dalasiman tsafi tana tofawa a kofar.Maimakon kofar ta bude sai wata irin iska mai karfin gaske ta fito daga cikin kofar ta doki kirjin Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sama da ita da karfi,bayanta ya gwaru da jikin bango ta fado kasa a galabaice.Koda ganin abinda ya faru sai hankalin Sarki Darmanu ya tashi jikinsa ya kama tsuma ya dubi Yarima Lubainu yace saura kai.Yarima Lubainu ya numfasa yace shin ka mantane kai abinda Sarauniya Akisatul Sauwara ta kasa yi nima bazan iya ba. Koda jin haka sai Sarki Darmanu ua ciza lebe sannan ya dunkule hannayensa biyu yayi nuni dasu izuwa ga kofar yana mai rintse idanu.Faruwar hakan keda wuya sai iska mai karfi ta fito daga cikin hannayensa ta rinka duka kofar dakin tana jijjigata kamar zata burma ciki amma sai hakan ya gagara.Maimakon ma kofar ta bude sai ta maido masa da iskar hannun nasa ta sureshi sama ta rinka katantanwa dashi a sama ya rinka ihu yana neman hallaka.Koda ganin haka sai Bakon Jarumin ya daka tsalle sama ya riko rigar Sarki Darmanu.Take iskar tsafin ta dauke dif sarki Darmanu ya fado kasa tim.Shi kuwa Bakon Jarumin sai ya diga a kasa bisa kafafunsa cikin koshin lafiya.Sarki Darmanu kuwa saida hancinsa da bakinsa suka kama yoyon jini.Bakon Jarumin ya dubi Dazyan yayi masa zance da hannu sannan Dazyan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu yace shugabana yace zai bude muku wannan kofa da izinin ubangijinsa wato ubangijin musulunci.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Yarima Lubainu da Sarki Darmanu tayi musu kallon ko menene ra’ayinsu? Duk su biyun sai suka sunkui da kawunansu kas.Faruwar hakan keda wuya sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Bakon Jarumi tace mun baka dama.Dajin haka sai Bakon Jarumin ya tunkari kofar dakin kai tsaye ba tare da shakkar komai ba,da isarsa bakin kofar sai ya dungureta da dan yatsansa guda daya.Take kofar ta bude a hankali tamkar yaro ne karami wanda baifi shekara hudu ba ya turata ta bude din.Saida kofar ta gama wangamewa gaba dayanta sannan su Yarima Lubainu suka matso kusa da Bakon Jarumin suna leka cikin dakin jikinsu na tsuma saboda tsoro da fargabar ko wata masiface zata taso,amma sai suka ji shiri kamar maye ya ci shirwa.Koda ganin cewa su Yarima Lubainu sun kasa shiga dakin sai Bakon Jarumin ya juyo ya dubi Dazyan yayi masa inkiya.Take Dazyan ya rugo ya bishi a baya,suka kunna kai izuwa cikin dakin su biyu,ba tare da fargabar komai ba.Duk da haka sai su Yarima Lubainu suka kasa shiga dakinDaki ne babba mai girman gaske tamkar wata karamar unguwa.Babu komai a cikin dakin face durowa da tebura a jere a layi,layi kuma sahu sahu reras,iyakar ganin idanun mutum babu iyaka.Akan teburan da durowoyin kwalabe ne birjik.Cike da RUWAN SIHIRI kala kala.A cikin durowoyin kuwa kayan TSATSUBA ne iri iri kamar kahonni,Layu,Guraye,Kawunan Tsuntsaye da sauran sassan jikin dabbobi dana dan Adam dana Aljanu.Shi kansa bakon jarumin daya shigo cikin wannan daki saida ya cika da mamakin irin abubuwan dake cikinsa da yadda akayi aka iya tarasa.Koda Ya ga sun dan jima a ciki amma su Sarauniya Akisatul Sauwara sun kasa biyosu izuwa ciki sai ya dubi Dazyan yayi masa maganar kurame.Take Dazyan ya juya da baya ya ruga waje yace da su Yarima Lubainu maigidana yace ku cire tsoron komai a cikin ranku ku shiga ciki saboda kune kuka san abinda kukazo nema,kuma akwai rubuce rubucen sihiri da yawa a cikin dakin a jikin abubuwa da yawa wadanda ba zamu iya karantasu ba mu fahimta. Koda jin haka sai Sarki Darmanu yayi wuf ya wuce gaba ya shige cikin dakin.Koda Ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu ma suka bi bayansa da sauri.Shima dan wada Dazyan sai ya bisu da sauri sukaje suka riski bakon jarumin a tsaye a cikin tsakiyar daki.Da isarsu Dazyan ya dubesu yace maigidana yace ya baku damar ku dudduba ko za kuga abinda kukazo nema.Koda jin haka sai duk su ukun suka rarrabu suka rinka bude durowoyi suna duba kan tebura.Saida suka shafe sama da sa’a daya da rabi suna neman ALLON SIHIRIN Boka Darbusa amma basu ganshi ba.Al’amarin dayai matukar dugunzuma hankalinsu kenan suka rasa abinda yake musu dadi a duniya.Koda Bakon Jarumi yaga yadda hankalinsu ya tashi sai mamaki ya turnukeshi yace a ransa”Hakika iska na yawo da mai kayam kara! Yanzu fa saboda kwadayin abin duniya ne yasa wadannan mutane idanunsu suka rufe akan neman wannan ALLON SIHIRI?A cikinsu ma babu wanda yafi cancanta a taimakawa sama da Yarima Lubainu,domin shine wanda aka zalunta kuma ake neman salwantar da rayuwarsa”.Koda gama Aiyana hakan a cikin ransa sai bakon Jarumi ya tafa hannayensa sau uku.Koda jin sautin tafin sai Yarima Lubainu,Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara suka tsaya cak ga barin binciken da sukeyi suka dawo inda yake tsaye.Da zuwansa sai dan wada Dazyan ya dubesu yace,maigidana yace tunda dai kun kasa gano inda wannan ALLON SIHIRIN yake to shi zai bincikoshi da yardar ubangijinsa.Cikin alamun karayar zuciya Akisatul Sauwara tace shike nan mun amince ya dauko ALLON SIHIRI.Koda jin haka sai Bakon Jarumin ya nufi inda jerin durowoyin suke.Har yabi layi na farko domin ya fara bincikawa sai ya tsaya cak,ya kirga layi na tara ya shiga yana kirgasu saida yazo kan durowa ta tara sannan ya tsaya cak ya dubeta da kyau.Babu kofa a jikin durowar kuma a rife take ruf.Babu alamar akwai wani abu a jikinta inda za’a iya budewa har aga abinda ke cikinta.Kawai sai ya daga hannunsa ya doki tsakiyar durowar take ta wargaje,ai kuwa sai ga ALLON SIHIRI kaso na uku a cikinta.Koda Yarima Lubainu,Sarki Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara sukayi arba da wannan ALLON SIHIRI sai suka cika da tsananin mamaki.Kawai sai Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara suka yunkura cikin bakin zafina nama duk su biyun a lokaci guda suka kaiwa ALLON SIHIRIN cafka,kowannansu na kokarin yariga dayan dauka,amma sai bakon jarumin yayi caraf ya rigasu dauka ya dubesu cikin murmushi yace,ai dama nasan cewa sai hakan ta faru a tsakaninku.Da zancen kurame yayi wannan bayani kuma Dazyan ne yayi musu jawabin.Bakon jarumin ya cigaba da cewa Kunga wannan ALLON SIHIRI dakuke gani duk wanda ya hada gudu uku a cikinsu bai isa ya iya rikeshi ba a hannunsa daidai da tsawon dakika goma ba,amma idan kuma shakkar hakan ku kawo ragowar bari biyun dake hannunku kuga zahiri.Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka kama muzurai suna duru duru suka kasa miko Allunan Sihirin nasu.Koda ganin haka sai Bakon Jarumi yayi murmushi kawai sai ya ajiye ALLON SIHIRIN Boka Darbusa a tsakiyar dakin ya koma gefe daya zura musu idanu.Nanfa Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka kama Kallon juna kuma suna kallon wannan ALLON SIHIRI.Nan take kowannensu ya zaro nasa Allon Sihirin kuma lokaci guda sai kowannensu ya daka tsalla ya kaiwa Allon Sihirin Boka Darbusa cafka.Ai kuwa sai hannayensu suka cafki Allon Sihiri a lokaci guda.Nan fa suka mike tsaye a tare suka kama naushin juna kowannensu na kokarin ya kwace Allunan biyu ya hade da nasa.Gashi dai kowannensu yana dakuwa domin naushin junansu sukeyi a fuska da ciki amma saboda naci sunki yarda su saki ALLON SIHIRIN.Shi kuwa Yarima Lubainu dama ya koma gefe daya ya zuba musu idanu kawai yana jiran yaga yadda karshen al’amarin zai kasance.Bakon Jarumin da dan wada Dazyan kuwa sai suka kara matsawa can gefe daya suka zauna akan wata doguwar kujera suna morewa idanunsu da kallon fadan da akeyi.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu na cikin kwarmazuwa sai kawai suka ga wata irin GUGUWA ta shigo cikin daki.Nan take ta suri komai na cikin dakin har da Sarki Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu tayi sama dasu ta rinka gwara kansu a jikin bango.Amma bakon Jarumi da dan wada Dazyan kuwa ko kusa dasu wannan guguwa batazo ba kuma suma suka ki suyi wani motsi suka cigaba da zuba idanu kawai.Cikin yan dakiku kadan su Yarima Lubainu suka jigata suka fita daga hayyacinsu.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu basu san Sa’adda suka saki duka Allunan Sihirin uku ba suka fado kasa.Faruwar hakan keda wuya sai Allunan Sihirin suka hade waje guda suka manne da juna tamkar ba’a taba rabasu ba suka zama babban Allo guda daya.Faruwar hakan keda wuya sai wannan guguwa ta rikide ta zama wadansu irin SAMUDAWAN BAKAKEN ALJANU dauke da muggan MAKAMAN YAKI.Nan fa samudawan bakaken aljanun suka ruguntsume da masifaffen azababben yaki a tsakaninsu,ya zamana cewa kowannensu na kokarin ya dauki ALLON SIHIRI ya gudu dashi amma duk wanda hannunsa yaki kan ALLON SIHIRI sai kaga an dankara masa SARA ko SUKA ko kaga an mangareshi ya fadi can gefe daya sumamme,ko kallonsa babu mai yi saidai ma acigaba da tattakeshi a kokarin gwagwarmayar daukar ALLON SIHIRIN.Tunda aka watsar dasu Sarauniya Akisatul Sauwara gefe daya a galabaice suka kasa mikewa tsaye suka cigaba da zama dirshen a kasa suna kallon wadannan Aljanu kawai suna ganin masifaffan yakin da ake yi tsakanin wadannan samudawan bakaken aljanun.Su kansu sun san cewa basu isa su iya tarar wadannan aljanu da yaki ba bare su iya karbar wan Nan ALLON SIHIRI daga hannunsu.Saida aka shafe sama da sa’a biyu da rabi ana yin wannnan azababben yaki ya zamana cewa da yawa daga cikin aljanun sun zama nakasassu wasu ba hannaye,wasu ba kafafu,wasu ma an datse rabin jikinsu,amma saboda taurin rai irin na aljanu basu fasa cigaba da kokarin daukar ALLON SIHIRIN BA.Koda bakon jarumi yaga ana ta bata lokaci amma an rasa wanda zamo GWARZON JARUMIN da zai iya daukar ALLON SIHIRIN sai kawai ya mike tsaye zumbur daga inda yake tsaye yana mai kwalla KABBARA ya falfalo da gudu izuwa inda akeyin wannan gumurzun yako.Da karfin tsiya ya ratsa ta tsakiyar samudawan bakaken aljanun yana bankesu suna zubewa kasa tamkar yana sassabe a gona.Koda yazo tsakiyar aljanun sai ya sake saka tsalle sama izuwa inda Aljanun sukayi tsiri sama wani kan wani domin sukai izuwa kan wani Gansamemen Aljani mafi tsawo,kauri da Kirar SADAUKANTAKA wanda shi ne ya sami nasarar cafe ALLON SIHIRIN ya bude fuka fukansa yai sama da niyyar ya gudu,amma sai wadansu daga cikin aljanun suka ruko kafafun nasa suna janyoshi kasa don ya fado,amma sai suka kasa saboda tsananin karfin damtsensa.A haka sadaukin Aljanin ya cigaba da fuffuka yana kai yakushi SARA DA SUKA da faratan kafafuwansa.Lokacin da bakon jarumin ya daka tsalle a sama tamkar an harboshi daha cikin baka sai da ya iso inda basamuden sadaukin aljanin yake,yana isowa daidai fuskarsa sai ya takarkare ya zabga masa wawan naushi a fuska.Saboda karfin naushin take karan hancin aljanin ya karye ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji.Nan take ya dimauce bai san sa’adda ya saki ALLON SIHIRIN ba.Caraf sai bakon jarumin ya cafe Allon Sihirin da hannu daya alhalin su kansu samudawan aljanun basa iya daga Allon Sihirin da hannu daya saboda tsananin nauyinsa.Koda Aljanun suka ga wannan bil’adama ya karbe ALLON SIHIRIN sai sukayi caa!a kansa suka yanyameshi suna masu kai masa sara da suka ta ko ina domin su hallakashi.Ai kuwa sai ya tarwatsa su a lokacin da ya sake kwalla Kabbara ya zare takobinsa cikin bakin zafin nama ya shiga kare kansa gami da maida martani.Wohoho!wanda Allah ya kare yafi gaban Magauta!Duk da tsananin yawa na wadannan samudawan bakaken aljanu da tsananin karfin damtsensu da mugayen makamansu sai gashi bakon jarumi ya zame musu ALAKAKAI,Sai gashi yayi musu mummunar barnar datafi wacce sukayiwa kansu,domin kuwa duk aljanin da yayiwa duka daya tofa idan ya baje a kasa wanwar da kyar ma yake iya numfashi wasu ma kamar sun zama gawa.Kai!da bala’i yakai bala’i sai gashi aljanun suna cika wandunansu da iska suna ficewa daga cikin dakin da gudu.Kafin a jima duk sun tarwatse sun fice daga cikin dakinsu duka sun bar bakon jarumin shi kadai a tsaye rike da ALLON SIHIRIN a lokacin da dakin yayi tsit tamkar babu wani mutum daya mai rai a cikinsa.Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul Sauwara kuwa saboda tsananin mamaki bisa ganin irin gagarumar jarumtakar da bakon jarumin yayi sai suka kura masa idanu kawao suka kasa budar baki suce wani abu,kai mikewa ma tsaye sai ya gagaresu.Koda ganin haka sai bakon jarumin ya dubi dan wada Dazyan yayi masa wata inkiya,shi kuma sai ya dubi Sarauniyar Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu da Yarima Lubainu yace,Maigidana yace bazai baiwa dayanku wannan Allon Sihiri ba face an zauna an tattauna kuma koda ma ya baiwa dayanku shi bazai sami damar karantashi ba bare har ya cika burinsa saboda masu farautar Allon Sihirin suna da yawa kuma sunfi ku karfin damtse dana Sihiri.Wadannan Bakaken Samudawan Aljanu da sukazo yanzu maigidana ya fatattakesu Yaran Boka Darbusa ne anan gaba kuma akwai sauran Manyan MATSAFAN DUNIYA da MANYAN JARUMAI dazasu fito farautar wannan ALLON SIHIRI.Kuma shi kanshi Boka Darbusa ba hakura zaiyi ba zai cigaba da kokarin karbarsa ne.Yanzu sai kowa yaje ya nemi dakin da zai kwanta a cikin wannna fada domin ya huta tunda dare yayi in yaso gobe da safe mu tattauna akan abinda muke ganin cewar shi ya kamata ayi.Gama fadin hakan keda wuya sai Bakon Jarumin ya juya domin ya fice daga cikin wannan daki,amma sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi wuf,ta mike tsaye kuma tayi gyaran murya tace,yakai wannan JARUMIN JARUMAI kayi sani cewa mu muna cikin tsoro da fargaba don haka bazamu iya sakin jikinmu ba har mu kwanta a cikin wannnan fada ta Boka Darbusa mu iya kwana a cikinta saboda a ko yaushe zai iya kawo mana ZIYARAR BAZATO ya cutar damu.Koda jin wannan jawabi sai Bakon Jarumin yaji kamar ya bushe da dariya amma sai ya dake ya dubi dan wada Dazyan yayi masa zancen kurame.Nan take Dazyan ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace,ashe bakuyi mamakin yadda shugaban ya iya yakar Boka Darbusa ba da dukkan Aljanunsa? Shin bakuyi mamakin yadda ya gano inda Allon Sihirinsa yake ba ya daukoshi kuma har ya hana wasu saceshi?To ku sani cewa zamanku anan cikin wannnan gida tare da shugabana shine kadai abinda zai baku kariya amma da zarar kun fita daga nan to fa komai zai iya faruwa a gareku,kuma abune mayuwaci dayanku ya iya tsira da rayuwarsa bare har ya sami damar cika burinsa.Koda gama fadin hakan sai Bakon Jarumin ya saba ALLON SIHIRI a hammatarsa ya juya ya fice daga cikin wannan daki Dazyan na biye dashi.Koda ganin haka ai Sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da Sarki Darmanu suka bishi da sauri cikin alamun tsoro suna ta waige waige,gani suke kamar ma a koda yaushe Boka Darbusa ko wakilinsa zasu iya kawo musu hari a ko yaushe. kuyi hakuri dangane da jinkirin post yauALLON SIHIRI Littafi na Uku (3) Part D LOKACIN da Bakom Jarumi ya fita daga cikin wannan daki na kayan sihirin Bokab Darbusa sai ya tunkari inda turakarsa ta barci take,kai tsaye sai kace dama can yasan kowanne lungu da sako na gidan.Da isowarsa kofar turakar sai ya tsaya cak sannan ya juyo baya.Take yayi arba dasu sarauniya Akisatul Sauwara suna biye dashi.Cikin matukar mamaki ya dubesu sannan ya dubi Dazyan sukayi magana kamar yadda suka sabaDazyan ya dubi su Sarauniya Akisatul Sauwara yace shugabana yace na gaya muku ba zai taba yiyuwa ba ya kwana da dayanku a cikin daki guda ba,shi kadai zai kwanta a cikin wannan turaka tare da ALLON SIHIRI,don haka ya zama wajibi kowannenku ma yaje ya nemi inda zai sa hakarkarinsa.Kuma yace lallai ku kwantar da hankalinku tamkar tsumma a randa,yayi muku alkawarin cewar babu abinda zai taba lafiyar jikinku koda kuwa kwarzane guda da izinin ubangijinsa.Koda gama fadin hakan sai Bakon Jarumi ya shige cikin turakar ya janyo kofar ya rufeta ruf ya bar Dazyan tsaye sororo a kofar dakin tare dasu Sarauniya Akisatul Sauwara,suma sunyi cirko cirko suna mamakin bakon jarumin.Abinda ya fara fado musu arai shine.”Menene dalilin dayasa bakon Jarumin bazai iya kwana tare dasu ba a cikin daki guda?Kuma menene dalilin dayasa duk a tsawon wannan lokaci bai yarda anga fuskarsa ba? To waishin ma shi Namije ne ko Mace?Lallai akwai bukatar su tantance hakan domin su san hanyar dazasu bi su rabashi da ALLON SIHIRI.Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi dan wada Dazyan tace ashe maigidan naka ma bai yarda da kai ba tunda ya kasa kwana tare dakai a cikin daki guda?Koda jin wannnan batu sai Dazyan ya takarkare ya bushe da dariya lokaci guda kuma yace yake wannan sarauniya kiyi sani cewa ni kaina bansan ko waye maigidana ba,ban san matsayinsa ba ko asalinsa,hasalima haduwata dashi bata wuce ta shekara uku ba,kuma a tsawon wannan lokaci ban taba ganin fuskarsa ba,kuma ban taba jin muryarsa ba bare kuda kuka hadu dashi a yau din nan.Shawarar da zan baku kawai itace,ku yarda da duk abinda kukaji ya fada,kuyi imani dashi,in ba haka ba kuwa karshenku shine NADAMA gami da yin MUMMUNAN KARSHE!Nidai yanzu zanje na nemi inda zan kwanta saboda na gaji likis kuma nima barci nakeji.Amma maigidana yace na shaidawa miki ke Sarauniya Akisatul Sauwara cewa lallai kema ki ware dakinki ke kadai domin a ka’idar addininmu haramun ne kiyi cudanya da mutanen da basu kasance muharramanki ba.Koda gama fadin haka sai dan wada Dazyan ya hango wani karamin daki dake can gefe daya wanda kofarsa ke bude wanwar,kawai sai ya tafi izuwa cikin dakin ya kunna kai ciki.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu ya bishi da sauri.Ita kuwa Sarauniya Akisatul Sauwara sai ta tsaya ta kama duru duru ta rasa dakin dazata shiga.Daga can kuma sai ta nufi wani babban daki wanda kofarsa ke rufe.Da isarta sai tasa hannunta ta murda kofar,bisa mamaki sai taga kofar ta bude da kanta.Sarauniya Akisatul Sauwara ta kunna kai izuwa cikin daki.Tana shiga sai kanta ya daure tamau ta kamu da tsananin mamaki,ba don komai ba sai saboda ganin irin kayan kawar dake cikin dakin.A tsakiyar dakin an ajiye wani lumtsumen gado mai girman gaske wanda aka cikashi da kayan taushi na alfarma.Sannan kuma akwai kofar kewaye a cikin dakin.Sarauniya Akisatul Sauwara ta leka cikin kewayen shima taga an kawatashi da bahon wanka na zinare.Kawai sai ta koma falon tayi tsalle ta fada kan wannan luntsumemen gado cikin jin dadin huce gajiya.Amma kuma har a sannan raunikan jikinta basu daina yi mata dan zogi da radadi ba.Nan take Sarauniya Akisatul Sauwara ta fada kogin tunani. ¤P¤H¤Y¤S¤I¤C¤I¤S¤T¤ AL’AMARIN Yarima Lubainu kuwa,bayan yaga kowa ya shige cikin daki an tafi an barshi shi kadai a tsaye sai ya kama yawo a cikin gidan yana neman dakin dazai shiga ya kwanta shi kadai.Ba don komai yake son ya sami inda zai kwanta ba shi kadai sai saboda ya sami damar dazai zauna yayi tunani da nazari ya yankewa kansa shawarar da zata fissheshi.Da yake wannan fada ta Boka Darbusa tana da tsananin girma tamkar gari guda,kuma gashi anyi gine gine da yawa a cikinta na kawa,sai Yarima Lubainu ya rude ya rasa ma bangaren dazai shiga domin da yayi yunkurin shiga wani dakin saiya hango wani wurin wanda ya fishi kyau da kawa.Yana cikin wannan kai kawo ne ya shigo wani bangare dabam na musamman wanda aka killaceshi a wuri mai ban al’ajabi.Shi dai wannan wuri ya kasance tamkar lambu kuma an kewayeshi da katangar zinare,sannan an zuba shuke shuke na ‘ya’yan itatuwa na marmari kala kala ga kuma tsuntsaye masu kyau ababan sha’awa kuma kofar wannna lamby a bude take.Har Yarima Lubainu ya gifta kofar zai wuce gaba sai ya jiyo shesshekar kuka cikin muryar MACE!Al’amarin dayai matukar bashi mamaki kenan,domin a zatonsa bandashi dasu bakon jarumi babu sauran wani mahaluki a cikin wannan gida.Yarima Lubainu ya dawo da baya ya tura babbar kofar kambun ya kunna kai ciki.Yana shia sai ya kame,idanunsa suka zazzaro sakamakon abinda yayi arba dashi.Ba komai ne abinda yayi arba dashi din ba face wata zabgegiyar kyakkyawar Budurwar ALJANA a daddaure cikin wata murtukekiyar sarkar tsafi waccce ta kanannade hannayenta,kafafuwanta da sauran sassan jikinta,kuma sarkar an zagayata ne a jikin wata dirkar tsafi mai tsananin kaurin gaske wacce fiye da rabinta ya nutse a cikin karkashin kasa.Abin daya daurewa Yarima Lubainu kai dangane da wannan Aljana shine ko a bakin masana labarai bai taba jin cewar akwai halitta mai siffarta ba.Rabin jikinta na bil’adama ne,daga kasan cibiyarta zuwa kanta.Daga gwiwar kafafunta zuwa tafin kafafunta kuwa na Aljanu ne.Kash!in badon wannan ratsin siffa ta Aljana ba dake jikinta da Yarima Lubainu zai iya cewa duk duniya babu wata ‘YA MACCE mai kyan wannan budurwa ba.Koda Yarima Lubainu ya hada idanu da wannan budurwa yaga idanunta sunyi sharkaf da hawayemkuma gata a daure cikin sarka,sai nan take yaji ya kamu da tsananin tausayinta.Amma da ya tuna cewa nan fa gidan Boka Darbusa ne babu mamaki ma wani tuggun ne aka shirya musu aka ajiye wannan Aljana domin su fada tarkon wahala,sai kawai ya juya da nufin ya fice daga cikin lambun,kawai sai yaji aljanar ta budi baki cikin murya mai zaki da bai taba jin irinta ba kuma mai tsananin taushin gaske tace,haba yakai Yarima Lubainu,ya ya kai daka kasance mai tausayi da jin kai zaka tafi ka barni a cikin wannan hali?Ka sani cewa shekara uku kenan wannan azzalumin Boka Darbusa na tsare dani anan,ina jiran ranar da zakuzo ku koreshi daga cikin wannan fada ku ceceni.Koda jin wannan batu sai mamaki ya sake turnuke Yarima Lubainu ya dubi Aljanar cikin alamun rashin yarda yace,wace ce ke kuma ya akayi kika sanni har kika san cewa zamu zo wannan fada mu kori Boka Darbusa?Sa’adda aljanar taji wadannan tambayoyi guda biyu ko uku sai hawaye ya zubo mata,tace ni sunana BADI’ATUL SARIRA,Kuma nice ‘ya guda daya jal a wajen mahaifina Sarkin Bokayen Aljanu na duniya kaf,wato ZARHASU IBINI SAMBILA.A cikin wannan duniya kaf in banda Boka Darbusa babu wani mahaluki daya kai mahaifina karfin sihirin tsafi da kuma tarin sirrikansa.Loka cin da mahaifina da Boka Darbusa suka gano cewa karfinsu yazo daya a sirrin tsafi sai suka zamo manyan ABOKAN GABA ya zamana cewa kowannensu na kokarin ya hallaka dayan ya rabashi da dukkan sirrikan tsafinsa.Asalin wannan ALLON SIHIRI da kuka daukoshi a dakin tsafin Boka Darbusa a hannun mahaifina yake,daga baya ne bayan Boka Darbusa ya samu nasarar kashe shi ya daukeshi.Ba komai ne yasa Boka Darbusa yaki kasheni ba ya daureni anan face cewa koya hada ragowar bari biyun na ALLON SIHIRI dana Mahaifina bazai iya cika burinsa ba face nidin nan na karanta masa wadansu dalasiman tsafi dake jikinsa na fassara masa su yadda zai fahimta,saboda yaren a akayi rubutun dashi a jikin Allon Sihirin mahaifina ni kadai ce na iya shi a duk fadin duniya,saboda mahaifina ne ya kirkireshi kuma tun ina yarinya karama ya koya minshi.Ina mai rokonka daka taimakeni ka kwanceni daga cikin wannan sarka yanzu in dai kayi min haka ni kuma nayi maka alkawarin cewa zan iya raba bakon jarumi da wannan ALLON SIHIRI,a cikin dakika daya jal,sannan na daukeka na kaika KOGIN BAHAR IMFAL a cikin abinda baikai rabin sa’a ba mu shiga cikin karkashin kogin na tsinko maka dan itaciyar dazaka sha ka warke daga cutar da YARIMA MANGUL ya sanya maka ka dawo cikakken da namiji ka koma ga matarka,babbar masoyiyarka YAZARINA ku fara sabuwar rayuwar aure cikin farin ciki.Ladan wannan aiki nawa kawai shine ka bar min wannan ALLON SIHIRI.Koda Aljanar tazo nan a jawabinta sai hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ainun ya rasa irin amsar da zai bata.Abinda ya fado masa a rai shine,shin zai iya yarda da wannan Aljanr kuwa? To ai idan ma ya yarda da ita kamar yaci amanar su Sarauniya Akisatul Sauwara ne! WACE IRIN SHAWARA YARIMA LUBAINU ZAI YANKE AKAN WANNAN DAMA DA YA SAMU? MAI ZAI FARU TSAKANIN SU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA DA BAKON JARUMI IDAN GARI YA WAYE? WANE HALI BOKA DARBUSA YAKE CIKI BAYAN YA FALFALA DA GUDU IZUWA CIKIN DAJI BAYAN SUN FAFATA AZABABBEN YAKI SHI DA BAKON JARUMI DON YA TSIRA DA RAYUWARSA? WANENE BAKON JARUMIN DAYA BAYYANA? YAUSHE YARIMA YAKE CIKA BURINSA NA SAMUN LAFIYA DAGA LALURAR DA YAKE CIKI? WAISHIN INA LABARIN YARIMA MANGUL? WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI. Mu hadu a littafi na hudu(ALLON SIHIRI-4)don jin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari. Post navigation [ad_2]