Labarai

ALMAJIRAI BA ‘YAN TA’ADDA BANE. _”Inji Sheikh Dahiru Bauchi 

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce: “Ana Almajiranci fiye da shekaru 1,000 da suka wuce a kasar nan, kuma hakan bai sa ya zama matsala a fannin tsaron kasar nan ba, daliban suna koyan karatu ta fannin karanta Al-Qur’ani da kuma haddace shi, kuma hakan ba wai ya mayar da su ‘yan ta’adda ba ne, hasali ma sune suke yiwa kasa addu’ar neman zaman lafiya.”

Ya kara da cewa, “Duk cikin wadannan ‘yan ta’addar da ake kamawa a kasar nan babu Almajiri ko daya, duka ‘yan fashi ne, sai masu garkuwa da mutane da sauran ‘yan ta’adda.”

“Mun sha ganin ‘yan sanda suna bincike akan ‘yan ta’addar da suke kamawa, idan suka tambayesu cewa sunyi karatun Al-Qur’ani ko kuma sunje makarantar Allo, amsar da suke basu ita ce aa.”

“Ina ganin lokaci yayi da ya kamata gwamnati ta banbance tsakanin ‘yan ta’adda da Almajirai, su ba ‘yan ta’adda bane karatun addini kawai suke yi kuma suke haddace Al-Qur’ani mai girma.”

Ya kuma shawarci masu fada aji a kasar nan da su cigaba da addu’ar neman zaman lafiya da kwacinyar hankali, inda ya kara da cewa,

“Babu wata hanyar da zaku hada Almajiri da ‘dan ta’adda, hakan ba daidai bane, kuma ba gaskiya bane.”

“Muna addu’ar Allah ya zaunar da kasar mu lafiya, ya kuma bai wa shugabannin mu damar mulki cikin kwanciyar hankali da amana, kuma muna yiwa shugaban kasa addu’ar samun koshin lafiya domin cigaba da gabatar da mulki yadda ya kamata,”.

Shehu yayi wannan martanin ne shekaru biyu da su wuce lokacin da gwamnatin shugaba Buhari ta ayyana ƙudurin ta na soke Almajiran ci gaba ɗaya a Nigeria da cewar sune ke shiga ƙungiyoyin ta’addanci.

Khalid Yunusa Faruk Ikara.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button