SARAN BOYE 75

No. 75
………….Su Jay dai sun wuce abuja, amma duk da su Addah na a asibiti suna a ƙarƙashin kulawar hukuma ne. Bayan wucewar su Jay shi ma Omar da Yoohan suka wuce da yamma. Ya bar Nu’aymah anan kano saboda Umm bata da lafiya. Har yanzu ta kasa fida daga ruɗanin data shiga. Ga jininta yaƙi sauka yanda ya kamata. Ita kanta hajjo jininta ya hau sosai. Sai dai ita Alhmdllh bai kai na Umm da komai yazo mata a yanda bata zata ba. Bama Umm kaɗai ba hatta da ƴan uwan Umm dana Addar wannan al’amari yay masifar rikita tunaninsu da basu tsoro. Anatama Addah ALLAH wadarai da wannan hali nata. Su Hajarah kam sunyi kuka har sun rasa hawayen zubarwa. Musamman Kubrah da dama ba daɗin zaman gidan mijin take jiba. Fitinar yau daban ta gobe daban.
Yanda gidan dai yay wani iri daga shigowa zaga fahimci akwai matsala. Baba malam salla kawai ke fiddashi. Da an idar yake dawowa gida. Komansa ya tsaya cak. Dan duk da daurewar da yakeyi a bala’in gigice ya ke da al’amarin. Bai taɓa ƙawowa a ransa cikin ƴan uwansa za’a samu mai wannan tunaninba akan dukiya dauɗar duniya. Yayi kuka bana wasaba a ɓoye, har ji yake gaba ɗaya ƙasar ta fita masa a arai.
_★★
Su Yoohan na isa Abuja suka iske sabon tashin hankali. Dan sun iske gidansu zagaye da jami’an tsaro. Da ƙyar ma aka barsu suka shiga saboda sanin Yoohan ɗansa ne. Cikin tashin hankali Yoohan ya ƙarasa falon inda ya tarar da ƙannensa duka da mama debora a hagitse. Suna ganinsa kuwa duk suka taso kansa a guje suna rusar kuka. Su duka rungumeshi sukayi har mama debora da Gebrail dake gudunsa a da.
Kallonsu kawai Yoohan keyi cike da tsoro, maganama ya kasa yi. Sai da Umar yay dauriyar cewa, “Granny wai mike faruwa hakane? Ku sanar mana Please. Gida zagaye da ƴan sanda. Gaku kuma cikin tashin hankali. Ina su papa suke ne?”.
Cikin matsanancin kuka joy tace, “Sun gudu Brother Richard”.
“Sun gudu kamarya? Ban ganeba nikam Joy?”.
Sakin Yoohan duk sukayi, mama debora ta kama hannunsa ta zaunar a kusa da ita. Shima Umar ɗin ya zauna. Sauran yaranma duk zama sukayi bisa umarnin mama debora. Tana sharar hawaye ta fara musu bayani.
“John munata kiran wayarka tun jiya ai amma mun kasa samunka. daren shekaran jiya kusan ƙarfe goma na dare wani mutum ya shigo gidan nan a kiɗime jikinsa jina-jina saboda harbi da akai masa. Lokacin duk munyi barci, kururuwarsa ta sakamu tashi batare da mun shirya ba duk muka fita compound. Tun a yanda mahaifinku ya ambaci sunansa a kiɗime na fahimci ya sanshi. Dan gaba ɗaya ya ruɗe shi da Chioma da guards ɗinsu. Shine ya sakamu komawa ciki akan dole batare da munji mike tafe da wannan mutumi dake a cikin jini ba. Muna falo tsaitsaye mun kasa komawa ciki mu kwanta sai ga shi sun shigo. Duk ɗakunansu suka shiga batare da sunce mana komaiba. Sai kuma suka sake fitowa a rikice. Mahaifinku ya rungumeni yana faɗin, karna damu na masu addu’a kawai, ga ATM card ɗinsa nan duk abinda muke buƙata Gebrail zai dinga ciro mana kuɗi. Daga haka suka fice zuwa garden. Ban taɓa sanin akwai wata hanyar fita gidannan ta garden ba sai a ranar. Dan sai bayan wucewarsu da kusan mintuna talatin ƴan sanda suka shigo anguwarnan sunata harbe-harbe. wasu suka shigo nan gidan suna nemansu harda guards ɗinkun nan. Sai lokacin mukasan guduwa sukayi harsu Solomon. Amma an kama guards uku a cikinsu. Su kuma ba’asan inda sukeba har yanzun”.
Wata irin masifaffiyar zufa ce ke ketoma Yoohan ta ko ina, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un yaketa faman maimaitawa. Shi kansa Umar zancen yay masifar rikita tunaninsa. Batare da Yoohan yace komaiba ya kama hannun Umar suka haye sama. Duk binsu sukai da kallon mamakin mizaiyi?. Bai saki hannun Umar ba sai da suka shiga sashensa can cikin ɗakin motsa jikinsa. Inda tanan yana iya hango duka ƴan sandan dake a compound ɗin gidan da anguwar ma.
Cikin matsanancin fushi ya yarfar da hannun Umar sannan ya tsatstsare sa da jajayen idanunsa. Muryarsa da tsananin kaushi da fushi yace, “Umar mi kuke ɓoye min kai da Matata akan iyayena?. kar kaimin ƙarya, dan ba ita nake buƙataba a yanzu na roƙe ka”.
Yanda ya ƙare maganar muryarsa na rawa kamar zaiyi kuka da haɗe hannayensa waje guda kuma sai zuciyar Umar ta ƙara raunana. Hannayen ya riƙe duka a cikin nasa ya sauke. “Yoohan anzo gaɓar da basai ka roƙeniba zan sanar maka. Sai dai inason ka fahimceni Please. Nima bani da wani zaɓin daya wuce hakan”.
Komai Yoohan bai ceba, saima cire rigarsa da yayi ya hau wani machine ɗin motsa jiki ya fara da sauri-sauri. Huci Omar ya sauke tare da fara bama Yoohan labari. Tun daga abinda ya fara ji akan kashe Nu’aymah da papa ya bama Dr Mateo kwangila har zuwa ɓoyayyun harƙalloli daya fahimci papa nayi a ɓoye. Kamar safarar miyagun ƙwayoyi da cocaine. Safarar makamai, satar yara yana tarasu a wani gida acan ƙauyensu……..
Ihunsu Mama debora daya cika gidanne ya saka Yoohan dan Umar fita da gudu zuwa ƙasa.
Cike da firgici da tsoro Yoohan da Umar ke kallon Little bee da tawagar jami’an hukumarsu. Ta haɗe fuska matuƙa, babuma alamar tasansu. A fusace Yoohan yace, “Lafiya kuwa?”.
Uffan Little bee batace masa ba. Sai ma i’d card ɗinta kawai ta nuna masa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Muna buƙatar shiga ɗakin Mr Goshpower domin yin bincike”.
Magana Yoohan zai sakeyi Umar ya girgiza masa kai alamar karya ce komai. Hannayensa duka biyu ya tura cikin aljihun wandansa ya koma jikin bango ya jingina saboda jiwa dake neman yaddashi a ƙasa.
Da Gebrail sukai amfani ta hanyar ɗora masa bindiga akai. Tuni fitsari ya jiƙe gaban wandonsa kuwa. Babuko kwana-kwana wajen kaisu har sashen papa. Tun a falo suka fara bincikensu. Yoohan baiyi niyar binsu ba, amma sai Omar ya kama hannunsa suka shiga. Basu sami komai a falon ba sai cctv dake a ɓoye. dan haka suka wuce cikin bedroom. Akan idon su Yoohan akaima ɗakin dalla-dalla. Ta hanyar tsabar ƙwarewar aiki su little suka gano ɓoyayyar drawer ɗin nan ta sirri dake a jikin bango. Sai dai kuma garƙame take da security, gashi kuma basu sani ba. An gwada password kala-kala baiyiba. Daga ƙarshe suka yanke shawarar yin amfani da na’urar fasa ƙarfe ko wane irine. Ta wannan hanyar aka fasa wajen. Sosai Yoohan ya firgita da ganin kalolin bindigu, da harsasai kala-kala. Sai tarin hodar ibilis da ƙwayoyin shaye-shaye masu matuƙar haɗari.
Kasa daurewa Yoohan yayi, sai da ya furzar da wani zazzafan hucin da sai da kowa ya juyo ya kallesa. An ƙara bibbincika ɗakin sosai kafin su kwashe duka kayan da suka samu ɗin sannan suka sakko ƙasa inda su mama debora keta faman kuka. Ganin makaman kuma ya sake rikitasu fiye da farko.
Koda suka fito sai suka shiga bincike gaba ɗaya lungu da saƙo na gidan, su dai su Yoohan suna binsu ne kawai da idanu. Sai da suka tabbatar da basu sake samun komaiba sannan suka tattara waɗanda suka samu ɗin zuwa mota. Sun buƙaci tafiya da wasu a cikinsu zuwa asalin ƙauyen su Yoohan ɗin, zakuma su cigaba da riƙesu har sai papa da madam Chioma sun bayayana kansu.
A take falon ya sake ruɗewa da kukan su mama debora. Ganin yanda suke neman fita hayyacinsu Yoohan ya ce zai bisu kawai shi da Gebrail. Kuka harda kururuwa Gebrail ya fashe da shi. Abun zat-tausayi zad-dariya. Haka su Mama debora naji na gani aka wuce da Gebrail daketa kwasar kuka da Yoohan.
Yoohan bai sake fahimtar al’amarin mahaifin nasu babba bane sai da suka iso airport, anan ma wasu jami’an suka tarar da alama jiran isowarsu sukeyi. Babu wani tsayawa ya akai ya za’ai aka shiga da su jirgi. Gebrail na nane da Yoohan cikin tashin hankali. Koda suka isa canma sun iske wasu jami’an tare da helicopters biyu. Nanma babu ɓata lokaci suka shiga zuwa can ƙauyensu. A canma sun iske garin a ruɗe sosai, dan uban batakashi akeyi tsakanin jami’an tsaro da yaran su papa. Gaba ɗaya ƙauyen a harmutse yake, dole aka bar su Yoohan a helicopter ɗin su little kawai suka firfita suma da nasu bindugun. Sai a yanzu ne fuskar Yoohan ta nuna tsantsar ruɗani. Gaba ɗaya komansa ya sare akan wannan al’amari. Lallai da alama mahaifin nasu ya jima cikin wannan mummunar harkar batare da su sun sani ba. Haba no wander yake ganin mahaukatan kuɗi basa gajiya da shiga accaunt ɗin papa. Sannan sam bayajin fargaba ko ciwon fitar da kuɗi wajen musu hidima ta bajinta.
Kallo dai iya kallo su Yoohan sun yisa. Daga ƙarshe su Little bee suka sami nasarar cafke gaba ɗaya yaran papa da su Uncle Godwin da aka ritsa a garin tun jiya. wasu sun sami raunika, wasu ko ma an kashesu. A cikin su little ma wasu sun sami raunuka.
Daga haka aka fasa ƙaton gidan da su papa ke ajiye yaran da suka sato ciki. ‘Hazbunallah’. Yarane mata da kananu, sai wasu baƙaƙen ƙartan bayi da kallonsu kawai ya ishi mutum amai, wasu da tsohon ciki, wasu cikin ƙananu ne, wasu kuma suna a tsaka tsaki. Sai jariran da aka haifa da har an gama cinikinsu ga masu buƙatarsu.
Tsabar tashin hankali little sai da tayi kuka ita da sauran ƴan uwanta jami’ai mata. A take Dawood yay kiran Jay ya tabbatar masa al’amarinfa babbane gaskiya. Ga ƴan jarida sunyi caa suna neman bayanai. Kamar yanda I.G na ƴan sanda ya kasance a wajen dole Jay ma ya taho ƙauyen da tawagarsa su Hafeez. Hakama gwamnan jihar dole ya shigo ƙauyen, dan kuwa kowa yasan da taimakon su papa ya hau mulki. Dan papa nada matuƙar ƙarfi cikin jahar tasu musamman daya kasance yana riƙe da muƙamin shugaba (Pastor).
Dole aka kawo manya-manyan motocin guda uku aka kwashe kaf mutanen dake gidan zuwa can babban birnin jihar. Su Dawood kuma suka shiga yima gidan filla-filla da bincike ta ko ina. daga haka suka sake kwasar jiki zuwa ainahin family house ɗin su Yoohan ɗin da suke zama idan sunzo garin. Ananma an samu abubuwa da dama, harda ɗakin sirri dake danƙare da Computers da suke gudanar da ayyukansu na yima mutane kutse, da zuba uwar sata a asusun bankuna dana mutane. A takaice dai papa shugabane mai zaman kansa na ƴan Yahoo.
Tuni zuciyar Yoohan ta gama bushewa tayi tauri akan wannan al’amarin. Binsu kawai yake da kallo tamkar mai kallon film a television. Shi ba zuwa ƙauyen yakeba sosai saboda karatun daya tafi ƙasashen ƙetare yayi. Bayan ya kammala kuma aikinsa baya bari sa samun nutsuwar irin waɗan nan ziyarce-ziyarcen. Idan ka gansa a ƙauyen sai lokacin Christmas da hutun ƙarshen shekara. Wannan kam a ko ina yake a duniya dolene sai yazo bisa sharaɗin papa. koda baizo Christmas ba zaizo a kwanakin ƙarshen shekara yayi new year. To mafi yawancin lokaci ma sai dai ya samesu anan. Bai taɓa damuwa da sanin sarrin duka gidanba. Iyakacinsa ɗakinsa da garden. Sai ko compound. Yawo ma a ƙauyen sai idan su Osin na tare da shine yake fitarsa. Amma shi kaɗai baya zuwa ko ina. Yafi buƙatar yay zamansa a gida.