NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 19

*_NO. 19_*


………..Ƙiri-ƙiri haɗuwa a tsakaninsu tayi wahala tsawon kwana biyu, dan ko motsinsa taji bata fita falon, akwana biyunnan kuma a gida yake kusan yini, shiyyasa daga ita har A’i babu mai sukunin zuwa zaman falon, kowa da nasa dalili, garama A’i takanyi asubancin fitowa ta gyara ko ina
dukdan gudun karsu haɗu, sai dai fa yini take leƙensa ta Window idan yana zaune a falon.
          Wannan takura kantan da tayi saiya haddasa mata yawan tunani da kewar gida mai tsanani, kaɗan-kaɗan saikaga tana share hawaye, ga maman Ahmad shiru bata shigo gidanba.
     Kwana uku suna wannan ƴar wasan ɓoyar, ana huɗune ta fiskanci kamar babu motsinsa a gidan har yamma.
     Bata tambayi Desmond ba, dukda kuwa yana kawo mata abinci da lokacin cinsa yayi.

      A’i ce taɗan fara walwala a gidan data fahimci yayi tafiya, a ha kali saita ringa jawo hankalin Ummu ma, dukda kuwa badan ALLAH take hakanba, dan kawai bin ƙwanƙwanton tane takaima Momcy gulma ta waya.
     Da yamma suna zaune a falon suna kallo saiga Maman Ahmad, sosai taji daɗin ganinta, da cewa tayi fushi.
    Dariya Maman Ahmad tayi tana kwantar da Ahmad dayay barci, “Ayi haƙuri amaryarmu, kinsan jiki da jini, ga makaranta muna Exam”.
        “ALLAH sarki, ashe karatu kikeyi?”.
    “Wlhy kuwa amarya muna ɗan taɓawa, kema ai kamata ma yay ki koma makarantar”.
    Murmushi Ummu tayi kawai, aranta tana tunani wanene zai biya mata kuɗin makaranta itako, to koma takardunta bata karɓoba balle.
     Sun cigaba da firarsu har zuwa yamma, a cikin firarne Ummu kejin wai Amaan ashe yana Yobe state ne shida Attahir, abin ya matuƙar bata mamaki, amma sai bata nunama maman Ahmad bata saniba, dankuwa ta tuna da gargaɗin Gwaggo hinde akan riƙe sirrin miji koda ace ƙuntata maka yakeyi.

*BAYAN SATI BIYU*

         Satin su yaa Amaan biyu a barno suka dawo, lokacin Ummu na falo kwance barci yaɗan figeta, A’i ma uwar gulma tana kicin wajen desmond suna hirar kurame, acewarsa yana koyan hausa, itama tana koyan turanci????.
        Da sallama ciki-ciki ya shigo falon, ƙal yake da tsafta tamkar yanda yake buƙatar ganin kayansa, ga ƙamshin turare mai daɗi yana tashi.
     Batareda ya lura Ummu dake kwanceba ya zauna a falon yana sauke numfashin gajiya tareda kallon agogon fata dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, ya kuma furzo huci tareda kwantar da kansa jikin kujera yana lumshe manyan idanunsa dake cike da gajiya. Kusan minti huɗu yana a haka, sai dariyar su Desmond dayake jiyowa sama-sama, idonsa ya buɗe a hankali sai suka sauka akan Ummu dake kwance tana barci hankalinta kwance.
        Duk yanda yaso janyewa saiya kasa, saima kallonta daya farayi tundaga ƙyaƙyƙyawar fuskarta zuwa matashin ƙirjinta, baki ya taɓe tareda cigaba da binta da kallo daki-daki. Cike da takaici ya sake maida idanun ya rufe, yama za’ai ace wannan ƙwailar yarinyarce matarsa, yaushema ta gama zama mace dahar ake tunanin dacewarsu?, ƴar ƙibarma daya lura tana da itace ta taimaketa, amma da siririyace da baƙaramar ƙwaila za’aiba a wajen, a ƙyawun fuska kam ya yarda tanadashi bakin gwargwadon iko, hakama kalar fatarta babu laifi, ƙirjinne dai babu alamar abun arziƙi, dolenema yasan abunyi game da wannan yarinyar kam, yanason bi ta hanyar da bazai ɓatama Dad raiba ya rabu da ita, Momcy kam dama kullum fatanta da gargaɗinta akansa kenan.
     Yakai mintuna talatin a falon kafin ya miƙe da nufin ƙarasawa ɗaki yaɗan huta.
        Duk basusan da dawowarsa gidanba saida yafito zashi sallar magriba, mamaki duk saida ya kamasu, desmond ya zube ƙasa yana bashi haƙuri akan baisan ya dawo baneba.
    Hannu ya ɗaga masa, murya can a ƙasan maƙoshi yace, “Haɗamin wani abu nayi azumine”.
    Bai jira cewarsaba ya sa kai ya fice abinsa.
    A’i dake bayansu a ranta tace, ba dole kai azumiba kasamu bakin ƴar mutane ka taune ranar.
        A fili kuwa sai jaddada masa barka da dawowa take yaƙi ko kallonta, sai hannu daya ɗaga mata kawai ya ida ficewarsa.
     Ummu naɗanjin motsinsu daga ɗaki, amma taƙi fitowa, ko kaɗan bamata sha’awar haɗuwarsu ita kam.
         Koda ya dawo sallama a falo ya zauna yay buɗa baki, amma baiga gilmawar yarinyar dako sunanta bai riƙeba shikam, hakan bai damesaba, dan aganinsa lafiya ke ɓuya. Sallar isha’i kawai ta tadashi, daya dawoma falon ya cigaba da zama har kusan 10:30pm, kafin ya tattara inasa-inasa yay ciki.

        Washe garima harya fita wajen aiki baiji motsin Ummu ba, saikuma abun yaɗan tsaya masa arai, baya fatan aikata abunda mahaifinsa zaiyi fushi dashi, karya zam yarinyar ko batada lafiyane?. Hardai yadawo gidan kusan 11 na dare abin na a ransa, hakanne yasashi nufar ɗakinta kai tsaye, dan gidan yayi tsitt babu motsin kowa, alamar sunyi barci.
     Tsaye yay yana tunanin idanma yashiga mizaice ya kawoshi?, amatsayinta na ƙaramarsa bata fito ta gaisheshiba dukda yasan taji motsin dawowarsa sai shine ma zai nemeta. Siririn tsaki yaja tareda lumshe idonsa ya buɗe yana shafar girarsa, harya juya zaibar ƙofar saikuma yakuma dawowa yana jan wani tsakin.
    Handle ɗin ƙofar ya murɗa tareda leƙa kansa, tsakkiyar gadon ya hangota kwance cikin doguwar riga ruwan madara, ya ɗan sauke ajiyar zuciya tareda jan ƙofar ya rufe mata bayan ya fito.
     Duk abinda yake Ummu na kallonsa, dan idonta biyu, da farkoma tsoro taji, amma ganin shine saita koma mamakin miya kawosa? Ganin bai maganaba ta maida idonta ta rufe da cigaba da tunaninta na nemawa rayuwarta mafita.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
   
           Baban Bukky na dawowa mamanta ta sanar masa komai.
    Murmushi yayi yana gyara zama cikin harshen yarabanci yake faɗin, “Babu wani babalawo dazakuje wajensa, kubarni dashi, dan akwai harƙalla a tsakaninmu, dama yaron yana neman wargaza mana wani aiki dukda kasancewarmu a samansa, lallai inada tabbacin da biyu ya dakarmin yarinya, sai dai wannan shine kuskure mafi girma daya tafka a rayuwarsa”.
        Dukda bataso ya dakatar dasuba taji daɗin nuna fishinsa akan hakan, takumasan zai ɗauki mataki kamar yanda ya faɗa.
     Bukky ma dake laɓe tana saurarensu ta gamsu takumaji daɗi, sai daifa ita sam ba Amaan kawai takeso ya ɗanɗana kuɗarsaba harda matarsa, dan haka ta yanke shawarar zuwa ita kaɗai wajen babalawo ɗin batareda iyayenta sun saniba.

  ★★★★

      Washe garikam batareda sanin kowaba a gidan ƙawarta Amo tai mata rakkiya wani ƙauye wajen bokanta.
    Dukkan bayani daya dace tai masa akan baƙar muguntar da takeson aima Ummu.
       Ƴan bincike-bincikensa na bokaye yayi kafin ya ɗago ya kalleta, “Madam maganar gaskiya yarinyarfa akwai tsari jikinta tunma tana ƙarama kakanta yayi, dan alamu sun nuna dukkan zuri’ar mahaifiyarta suna tare da wannan tsarin a jikinsu, kowanne asiri bazai kamasuba sai dai ƙaddarar ALLAH da babu mai gogeta a kundin mutum”.
      Cike da damuwa da takaici Bukky tace, “Yanzu kana nufin koma mizan mata bazai yuwuba kenan?”.
     “Gaskiya bazai yuwuba, sai dai ki bani dama zan sake binciken wata hanyar, nanda wani lokaci saiki dawo”.
     Godiya tai masa suka taso suka dawo, Amo nata kuma tunzurata, harda cewa zataje taga matar ta Ajiwa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

     Ɓangaren Momcy ma hankalinta yakasa kwanciya gaba ɗaya, burinta kawai tayaya zata raba auren Ummu da Amaan, amma sam ta rasa, gashi kullum cikin lasar takobin hakan take.
    Duk da Alhaji Mahmud na lure da ita bai taɓa maganaba, baima kuma nuna mata yasan anaiba.

★★★★

      Haka dai rayuwar taci gaba da tafiya yau da daɗi gobe sai haƙuri, a zaman Ummukulsoom da Yaa Amaan babu wani canji, danba harkarta yake shigaba, hasalima baya haɗa sati guda a jere yana gidan, yanayin yawan tafiye-tafiye wanda Ummu batasan ina yake zuwa ba dan ko sallama sai randa ya gadama yake musu, wani lokacin kuwa sai dai taji a bakin desmond ko maman Ahmad.
    A kwana a tashi aurensu yashiga watanni shida dayi, har yanzu kuma A’i uwar gulma nakai rahoto wa Momcy.
      Yayinda itakuma take ƙarajin tsanar zaman Ummu da ɗanta tareda neman hanyar rabasu cikin sauƙi.
    Taso su Ummayya suje legas amma Dad ya hana ƙiri da muzu.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

        Ɓangaren haji Baseer ma dai a wajensa komai yana tafiya yanda yakeso, yasha amarcinsa da Lubna yanda ya kamata, yayinda ita kuma take masa biyya fiyema da zatonsa.
    Hakanne yasakashi kuma jin Suhailat fita a ransa, dan haka yashiga mata salon wulaƙanci kala-kala.
    Tun Suhailat bata fahimci komaiba harta fahimta, saboda yawan tafiye-tafiye da yakeyi, tun tana dannewa hardai ta tambayi Daddynta ko Baseer yanayine a ƙarƙashin company? Daddy ta yace ko kusa ba haka baneba, shi kansa baisan ina Baseer ɗin yake yawan zuwaba, dan a duk sanda zaiyi tafiya cemasa yake yaje ɗilau gaida iyaye sa.
        Sosai hankalin Suhailat yay mugun tashi, tashiga bin ƙwaƙwƙwafin Baseer, daga ƙarshe tagano ashe aure yay basu saniba, harma amarya nada ciki ƙarami.
     Ai a wannan dawowa dayay tsiya ta ɓarke tsakaninsa da Suhailat, wadda takaiga ya shashsheƙa mata mari ga tsohon ciki. 
       Tako dage ta rama marin dayay mata, nanfa suka harƙume dukan juna saboda bashida hankali, tsautsayi ya sakashi doke ɗan cikin nata tako zube a wajen tana kuka.
    Shikuma a fusace yake faɗin, “Ya saketa saki uku, kuma ALLAH ya isa tsakaninsa da ita”.
      A wannan lokacin Suhailat batashi takeba kam, ta azabar datake ciki take, ga jini yafara zuba mata.
     Hankalin ƴan aikinta yatashi matuƙa, kukun gidan yakira Mahaifinta ya sanar masa.
   
     Lokacin da mahaifin Suhailat sukazo gidan tadaɗe da fita hayyacinta saboda jini dake zuba. Basubi takan komaiba suka kwashe zuwa asibiti.
         Suhailat tasha wahala sosai kam, aranar kuma ta haihu bakwaini, yaron ko awa ɗaya baiyiba ya rasu.
    Tsinuwa dai kam Baseer ya shata ga dangin Suhailat, saidai koma ƙeyarsa basu ganiba, dan aranar da abun ya faru aranar yabar kaduna zuwa ɗilau,  ya kwashe Inna da baba wai zai kaisu zaria, aiko ya gudo kano dasu tareda canja layin da dangin Suhailat suka sanshi dashi.
     Sudai su baba sunmasa tambayar duniya yaƙi faɗi musu gaskiyar abinda ya faru, sai ƙarya daya zauna ya tsara musu akan wai wasune suke son cutar dashi, idan kuma basu samesaba su zasu nema ai.
      Hankalin baba ya matuƙar tashi, dan bayason tashin hankali shikam, shiyyasa lamarin basiru ke bashi tsoro sosai, yaron bayajin magana ko kusa ko kaɗan, dan sudai shine jarabawarsu.

    Kamarko basiru ya sani ya gudu dasu baba, dan koda mahaifin Suhailat yasa aka nemeshi bashi a kaduna saiya tura ƴan sanda su kama iyayensa, yasan hakan zaisashi zuwa da kansa ai dole, sai dai kuma sunje babu su Inna a ɗilau, kowa yakance baisan ina sukajeba, dan ko talatuwa ƴarsu batasan da tafiyar yasuba, dayakema ba’a ɗilau take aureba, tanacan wani gari a katsina.
     Mahaifin Suhailat yay alwashi nemo Baseer aduk inda yake, amma sai Suhailat ta dakatar dashi ta hanyar cewa ya barsa, dakanta zatai wannan ramuwar, kamar yanda ya yaudareta ta hanyar zanba itama ta hanya mai sauƙi zata ladabtar dashi, duk da tasan itama akwai kuskurenta na bijirema iyayenta, tun farko sun nuna basaso amma ta dage saishi saboda soyayya ta rufe idonta bataji bata gani.
       Sosai take roƙonsu gafara bisa hakan. cikin tausaya mata suka yafe mata, tareda mata gargaɗin ta kiyaye gaba.
    Murmushi kawai tayi mai ciwo, dan ita zuwa yanzu ko ba’a bata shawaraba ita maibama kantace, ba soyayyaba ko mazama basa burgeta zuwa yanzu, dan duk tamusu kuɗin goro akan yaudara.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

           Tun Baseer na tsorace da nemansa da yasan mahaifin Suhailat zai iya yi harya sami nutsuwa ganin shiru, bayan lafawar komai yabar su baba suka koma ɗilau saboda takurawar da sukayi akan sabawa da sukai da can ɗin.
       Shiko saiya cigaba da rayuwarsa da gimbiya Lubna cikin soyayya da amincin datai masa har ranta……..✍????


*_Kuyi manage da wannan, lafiya tamin ƙaranci wlhy, shiyyasa kwana biyunnan ko editing bana muku, amma insha ALLAH komai zai zama normal_*????????????????????????


⛹‍♀⛹‍♀babu editing dai.






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button