BA CIKI BANE

*Page 1~5*
Tafiya yake cikin had’add’iyar motar sa a hankali yake tafiya tsabar gajiya da yayi yana Allah Allah ya k’arasa gida wajen amaryar sa.
A bakin gate d’in wani babban gida ya tsaya horn yayi da sauri mai gadin ya lek’o ganin motar ogan shi ne ya sashi bud’e gate d’in da sauri shi kuma ya shigo da motar shi.
K’arasawa wajen ogan shi yayi yana mai cewa
“Sannu da zuwa Yallabai an dawo lafiya?”
Murmushi yayi mishi sannan yace
“Lafiya k’alau Baba kuma na same ku lafiya ya aiki?” Shima ya sake tambayan Sa.
“Lafiya k’alau Alhamdulillah.”
“To yayi kyau.” Yana k’arasa fad’an haka ya shige cikin gida.
Sallama yayi yashiga cikin gidan mamaki ne ya kamashi yanda yaga parlour’n gidan duk yayi kaca-kaca tamkar an shekara ba’a share ba.
Ganin bata parlour’n ne yashi shiga cikin d’akin ta a d’akin ma bai ganta ba har zai fita sai yajiyota a toilet tana amai da sauri ya shiga toilet d’in ya tallafota yana mata sannu a haka har tagama amai ya wanke mata jikin ta ya fito da ita.
Jikin ta ya ta6a jin zazzabi ne yasa shi cewa
“Subhallahi!
Rahma me yake damun ki?”
Kasa magana tayi sai faman rawan sanyi take hakan ne yasa shi cire wayar ya kira Dr-Sabir.
Yana d’auka yace da shi yazo shi gida yanzu Rahma ba lafiya yazo ya duba ta.
Shi kuwa yana jin haka ya mik’e ya d’auki kayan aikin sa ya tafi.
Kwantar da ita yayi ya koma parlour ya fara gyarawa nan da nan ya gyara parlour’n ya saka turaren wuta ai kuwa sai k’amshi ya garwaye parlour.
Ya gama ya koma d’aki ya d’auko Rahma zuwa parlour kenan Dr-Sabir yayi sallama ya shigo.
Dubata yayi sannan yace da Nawaf yana son fitsarin ta dan zai mata test.
Ba musu Nawaf ya tashi Rahma zuwa toilet tayi suka bashi.
Da yake shi yana zargin ciki ne da ita magani ya bata wanda zai tsayar da amain da kuma wanda zaisa ta samu k’arfin jikin ta, bayan ya bata kuma yayi musu sallama ya tafi akan idan anjima zasuji saka mako.
Cikin rawan jiki Nawaf ya bawa Rahma magani tasha sannan ya shiga da ita bedroom tayi wanka.
Alhamdulillah tasamu sauki sosai a haka suka samu suka ci abinci sannan Nawaf yayi wanka sannan ya fita zuwa hospital.
Direct office d’in Dr-Sabir ya nufa zaune ya same shi sai faman had’a gumi yake duk da sanyin AC da yake office d’in.
Sallaman Nawaf ne yasa shi murmushi sannan yace
“Wa’alaikus salam Nawaf har Ka iso?”
Shima murmushi yayi mishi sannan yace
“Eh wallahi Sabir nazo. wallahi hankalina duk ya tashi ne.”
“Gaskiya ne dole hankalin Ka ya tashi
amman gaskiya zan fad’a maka abinda yake damun Matar Ka amman sai dai kayi hak’uri.”
Cikin rud’ewa Nawaf yace
“Dan Allah Ka fad’a mun menene yake damun ta?”
“I’m sorry Nawaf Matar ka tana d’auke da ciki.”
Wani irin mik’ewa Nawaf yayi sannan yace
“What!
Dr-Sabir ciki fa kace?”
“Eh amman hak’uri zakayi ciki ne da ita na tsowun wata uku.”
Kasa magana Nawaf yayi ya fita yabar office Dr-Sabir yana k’wallah mishi kira amman ina da gudu ya k’arasa inda yayi parking motar sa yana shiga bai tsaya a ko ina ba sai gida.
Ko sallama baiyi ba ya shiga yana kiran Rahma! Rahma!! Rahma!!! Sai a lokacin ta amsa “na’am My sw”…..
Bata gama amsawa ba ya wanke ta da wani wawan mari wanda sai da yasata rik’e kuncin ta sannan yace
” Rahma da cikin Uban wa kika zo mun gida na?” Ya tambaye ta cikin kaukausar murya.
Wani kallo ta mishi sannan tace
“Kamar ya ban gane ba?”
Cikin tsawa yace mata
“Ke banason rainin hankali ko ina miki wasa yau auren mu satin shi nawa?” Ya tambaye ta cikin tsawa.
Sai a lokacin gaban ta yayi mummunar fad’uwa dan kuwa babu yanzu asirin ta ya tonu katse mata tunani yayi da wani wawan mari sannan yace
“Rahma kin cuceni kin cuci kanki wallahi bazan ta6a yafe miki ba daman da ciki a jikin ki kika aure ni?
Ki tattara naki da naki kibar mun gida na na sake ki saki d’aya.”
Kuka ta fashe da shi sannan tace
“Dan Allah ya Nawaf kayi Hak’uri Ka yafe mun Karka sake ni..”……
Katseta yayi da ” rufe mun baki munafuka Wallahi ki barmun gida na kafin na fito a d’aki idan kuma ba haka ba wallahi na lahira sai yafiki jin dad’i.”
Yana gama fad’an haka ya bar parlour.
Zama tayi a wajen tana kuka sai kuma ta tuna idan kuwa ya fito ya sameta a gidan shi tsaf zai aikata abinda yayi niya.
Haka ta tashi ta shiga bedroom ta shirya kayan ta cikin kankanin lokaci ta fito tana kuka.
Malam Buba mai gadi ne ya ganta sai faman kuka take hakan ne yasa shi k’arasowa wajenta da sauri yana cewa
“Subhallahi!
Madam lafiya kike kuka a wannan lokacin?”
Wani kallo ta watsa mishi sannan tace
“Ubanka aka mun dan shissshigi ina ruwan Ka da ni munafuki kawa.”tayi mishi tsaki ta wuce.
Shikam Malam Buba mamakin Rahma yake sosai dan kuwa ba k’aramin rashin kunya take mishi ba duk da girman shi.
Kayan ta ta zuba mota ta shiga Malam Buba bai k’arasa bud’e gate d’in ba ta k’araso saura kad’an ta bigeshi Allah yasa ya k’auce da sauri.
Gudu take akan titi sosai Allah ne kawai ya kaita gida lafiya.
Horn Tayi mai gadin ya bud’e mata gate ta shiga.
Bata gama yin parking ba ta fito da gudu ta d’aura hannu a kai tana k’allah ihu tana kiran Momyn ta.
Hajiya Saratu wacce itace mahaifiyar Rahma tana zaune a parlour’n ta taji ihun ‘yar Lelen ta ai kuwa da gudu ta fita tana cewa
“Subhallahi!
Rahma lafiya ke da waye?”
Wani ihun ta sake yi sannan tace
“Momy Nawaf ya sake ni!”
Wani irin kallo tayi mata sannan ta ja hannun ta zuwa parlour.
Sai da suka zauna tace
“Haba wallahi Rahma kin bani kunya ni nad’auka ma mutuwa mijin naki yayi dan ya sake ki shine kike yin irin wannan ihun sai kace ba jini na ba wai ma bari na tambaye ki yaushe ya dawo daga tafiyar?
Kuma ya akayi ya gane daga dawowar sa kina da cikin?”
Cikin kuka Rahma tace
“Momy wallahi yau ya dawo ko nima bansan da dawowar sa ba lokacin da ya shigo shine ya sameni ina amai ga zazzabi shine fa ya kira abokin sa Dr-Sabir yazo ya dubani .” sai kuma ta sake fashewa da wani kukan.
“To naji kimun shiru saki nawa ya miki?”
“Saki d’aya ne Momy.”
Wayan ta Hajiya Saratu ta d’auka ta kira Hajiya Fatima mahaifiyar Nawaf tana d’auka ko gaisawa basu yi ba ta fara cewa
“Wannan shine irin abinda d’an ki yayi mana ya sake min ‘ya bayan ya mata ciki tun a waje mun rufa masa asiri anyi auren shine yanzu ya sake ta ko?
To wallahi da mu kuke zancen sai munyi maganin Ku” tana gama fad’an haka ta kashe wayan ta.
Hajiya Fatima kam gaba d’aya ta k’asa d’aukan komai a cikin maganar sai yayi mata ciki a waje anyi aure ya sake ta.
B’angaren Hajiya Saratu kam murmushin mugun ta tayi sannan tace
” ai saki d’aya ba komai bane kiyi shiru gobe zanje wajen bokan mu zai mana aiki akan su sai sunsan da mu suke zancen.”
Sai a lokacin Rahma taji dad’i sannan tace
“Yauwa momy nagode sosai shiyasa nake son ki wallahi.” Ta k’arasa maganar tana runguman ta.
Kwance yake akan bed d’in shi sai faman juyi yake ya rasa mai yake mishi dad’i gaba d’aya baisan inda hankalin shi yake ba.
Wayan shi ne ya fara ringing shine ya dawo da shi daga duniyar tunani.
D’auka yayi ganin number Umma ne yasa shi tashi ya zauna.
“Assalamu alaikum Umma Ina wuni.”
Amsa mishi tayi sannan tace
“Kazo Ka gida yanzu ina son ganin Ka.” Tana k’arasa fad’ar haka ta kashe wayan ta.
“`Kutmelesy wanne chakwakiyar ne zai faru?“`????