BA CIKI BANE

Ba k’aramin haushi maganar yabawa Rahma ba hakan ne yasata tace
“Eh shiyasa akazo maka da shege aka ce naka ne ka yarda da shi,
amman ga Wanda yake naka halak malak amman kaki amincewa da shi.” Ta gama maganar tana nuna cikin ta.
Kallon ta yayi daga sama har k’asa sannan yace
“Waton kina son tonawa kanki asiri kenan?
To bari kiji kar ki sake kiramun d’ana da shege wanda yake shegen na jikin ki daman ya amsa sunan sa amman kika sake kuskura kika kiramun da d’ana shege a ranan zaki gane baki da wayo.” Ta k’arasa maganar yana nunata da yatsa.
“Haka kace ba to wallahi Nawaf kai da wannan ‘yar iskar sai na nuna muku Ku ba komai bane wallahi.” Tana fad’an haka tafice tabar parlour’n.
Safnah dai tana zaune tana jinsu ita gaba d’aya ma rikita ta sukayi da cewa ba cikin Nawaf bane to na waye? Ta tambayi kanta.
Sai kusan k’arfe goma sannan suka koma d’aki suka kwanta.
Washe gari Safnah ta samu sauki sosai dan taji k’arfin jikin ta haka ta shiga kitchen tayi musu girki.
Hajiya Saratu kuwa tun 6:00Am ta tafi wajen boka karb’an maganin da zai zubarwa Safnah ciki.
Ko da tayi mishi bayani wani kullin magani ya bata yace
“A zuba mata a abinci ko a juice idan taci ko tashi shikenan cikin zai zube kuma ita da ciki har abada.”
Wani dad’i ne ya lullu6e Saratu yace
“To boka godiya muke.” Ta ciro kud’i ta bashi sannan ta tafi.
Tana komawa gida ta bawa Hanifa ta kaiwa Rahma kuma ta kaiwa ta dawo kar ta zauna.
Ba musu ta kar6a ta kama hanya tazo gidan Rahma.
Ko da Habifa taje da Safnah ta fara had’uwa tsayawa tayi suka gaisa cikin mutun ci sannan ta wuce wajen Rahma.
Tana shiga ta sameta kwance Rahma tana ganin Hanifa ta tashi ta zauna tana mai jin dad’i.
Bayan sun gaisa ne ta bata kullin maganin tace
“Gashi inji Momy.”
Amsa tayi sannan tace
“Yauwa k’anwata nagode sosai da kika kawo mun wannan abin.”
Kallon ta Hanifa tayi tace
“Aunty dan Allah me zakiyi da wannan abin?”
Wani kallo ta watsa mata sannan tace
“Ina ruwan ki da abinda zanyi da shi?
Ke bana son gulma kina kina ko?”
Kallon ta Hanifa tayi tace
“Allah yabaki hak’uri ni tafiya ma zanyi.”
“To Allah ya kiyaye hanya.”
Haka Hanifa ta fita tana tur da halin Momyn su da Auntyn ta dan tasan duk abinda Rahma take da hannun Momy a ciki.
Mik’ewa Rahma tayi ta nufi kitchen d’in Safnah, abincin da Safnah ta zuba a plate zata ci taji wayan ta yana ringing ta tafi d’auka tabar abinci shine Rahma ta samu.
Da sauri ta k’arasa wajen abincin ta zuba wannan maganin da sauri ta bar kitchen d’in.
Tana fita sai ga Safnah tazo ta d’auki plate d’in abinci ta nufi parlour da shi.
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????
???????? *BA CIKI NA BANE!*????????
????????????????????????????????
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????
“`DEDICATED TO ALL MY FANS“`????????❤❤????????????????????????
*ASSALAMU ALAIKUM MASOYA WANNAN LITTAFIN INA MAI MIK’A DUNBUN GODIYA TA GARE KU YANDA KUKA KULA DA NI NA RASHIN JINA DA KUKA YI.*
“`HAK’IK’A NAJI DAD’I KWARAI YANDA NAGA MESSAGE NAKU KAMAR RUWA DA WAD’AN DA SUKA KIRANI SUKAJI WAYA NA A KASHE NA GODE! NA GODE!! NA GODE!!! ALLAH YA BAR ZUMUN CI AMEEN“`????????
*MY K’AWA JANNART NAGODE DA ZUWA DA KIKAYI HAR GIDA DAN DUBAWA LAFIYA 2 DAYS BAKI GANNI ONLINE BA WALLAHI NAJI DAD’I HAR CIKIN RAINA BAZAN GAJI DA GODIYA BA*????????????❤❣❣❣
“`TO MASOYAN BA CIKI NA BANE KU GYARA ZAMA KU FARA KARATU DAN YANZU MUKA FARA CAKWAKIYAR KUDAI KAWAI KU KASAN CE MOMYN MUSADDIQ “`????????????????☺☺
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 71~75*
Rahma tana fita sai ga Safnah tazo ta d’auki plate d’in abincin ta nufi parlour da shi.
Tana zuwa ta zauna ta ajiye abincin amman zuciyar ta sai faman murd’awa yake da alamuAllah bata son k’amshin abincin.
Haka ta d’auki cokali ta d’ebi abinci har ta kai bakin ta amai ya dawo mata da shi.
Ai kuwa nan da nan ta wanke jikin ta da amai dan ko tashi a wajen batayi ba yazo mata.
Jikin ta rawa kawai yake dan ba karfi ko kad’an haka ta mik’e ta fara gyara wajen.
Kafin ta gama sai da ta d’auki lokaci dan zazzabi ne ya rufe ta.
Tana gamawa ta koma d’aki Tayi wanka sannan ta samu ta kwanta.
Rahma kuwa duk abinda ya faru a gaban dan duk tana kallon ta cewa take
“Cab! ai wallahi baki isaba Safnah kinyi kad’an wannan shegen cikin sai mun zubar da shi ‘yar iska.” Tana gama fad’an haka ta d’auki key d’in motar ta da mayafin ta ta fita bata tsaya a ko ina ba sai gidan su.
Ko da taje gidan su Tayi sa’a mahaifin ta baya nan ya fita ai kuwa da sauri ta shege d’akin Momy.
A kwance ta sameta tana barci a bakin gadon ta zauna sannan tace
“Momy ki tashi.”
Ina Momy barci take abinta d’aga hannun ta Rahma Tayi ta lafta mata a duwawu Wanda sai da yasa Saratu mik’ewa da sauri tana cewa
“Wanne d’an iskan ne wannan……”
Rufe bakin ta tayi ganin Rahma sannan tace
” ‘yar Momy lafiya naganki yanzu?”
Kallon Momyn ta Tayi sannan tace
“Ina ko lafiya Momy!
Wannan ‘yar iskar har yanzu bata ci wannan maganin ba fa tana sawa a baki ta fara amai yanzu haka tabar abincin.”
Ajiyar zuci Saratu Tayi sannan tace
“Kar kidamu idan dama tak’i to zamu koma hagu zamu mai gaba d’aya mu kashe ta mu huta gaba d’aya.”
Kallon ta Rahma tayi tace
“Momy kina ganin ba matsala idan muka kashe ta?”
“Karki damu ba wani matsala idan ba ke zaki tuna mana asiri ba.”
“A’a Momy bazan tab’a tona mana asiri ba ai idan na tona asiri ai na kashe kai na ne.”
“To kar kidamu boka zan fara mana aiki gobe komai zaiyi kinji ko.”
Dariya Rahma tayi sannan tace
“Yauwa Momy nagode sosai wallahi kina sona.”
“To idan ban soki ba wa zanso.”
Haka suka zauna suka ci gaba da shirar su da yanda abinsu zai kasan ce.
Safnah tana kwance ta rasa mai yake mata dad’i sai ga Nawaf yana sallama.
Sallama yake amman shiru hakan ne yasa shi shiga d’akin Safnah.
Da sauri ya k’arasa yana cewa
“My Angle har yanzu jikin ne?”
Kallon Sa tayi da jajayen idanun ta sannan tace
“Zazzabi ne yake damu na Ya Nawaf.”
“Subhallahi!
Tashi muje kisha magani kinci abinci ne.”
Jijjiga mishi kai Tayi alamun a’a ce mata yayi
“Meyesa baki ci abinci ba My Angle?”
“Ya Nawaf bazan iya ci ba amai yake sani.”
“To me kike son ci?” Ya tambaye ta.
Shiru tad’an yi sannan tace
“Yalo nake son ci.”
“Ok idan na kawo miki zaki ci?”
“Eh zan ci.”
“To ki kwanta yanzu zan dawo kinji bari na shiga wajen Rahma.”
Yana gama fad’an haka ya mik’e ya fita.
Ko da yaje d’akin Rahma bai same ta haka ya fito parlour ya duba ta but bai same ta ba duk inda yasan zai sameta bata nan haka ya hakura ya fita yana mamakin halin Rahma a zuciyar sa yana cewa
“Wannan wacce iriyar mata ce wacce sam bata san mutuncin kanta ba bare kuma auren ta.”
Haka ya tafi yana tur da halin Rahma har yaje ya siyo da yake wajen da ake siyarwan ba nisa sosai.
Ba laifi taci sannan tasha magani suka zauna a parlour yana mata hira.
Har magriba Rahma tana gidan su zaune kamar wacce batada niyar komawa sai da Saratu tace mata
” ‘yar Momy bazaki taxi bane dare fa yayi.”