BA CIKI BANE

“Eh Momy yanzu zan tashi na tafi ina tunanin rashin mutun cin da zan musu ne dan ni bazan barsu suji dad’i ba.”
“Haka ne ‘yar albarka ai daman ke duk wani halina kin gaje shi shiyasa nake sonki sosai wallahi ki tattabar kin musu wulak’aci wanda bazasu mance shi ba kuma idan ta kama har duka kiyiwa ‘yar iskar.”
Dariya Rahma Tayi sannan tace
“Yauwa Momy wallahi kinyi a rayuwa wacce bata samu uwa tamkar ki ba bataji dad’i ba.”
Hajiya Saratu ma dariyan jin dad’i tayi sannan tace
“To ‘yar Albarka tashi ki tafi kafin jarabben mahaifin ki nan ya dawo.”
“To Momy dan kuwa yanzu zaizo ya fara mana.”
Haka sukayi sallama ta tafi hankalin ta kwance.
Nawaf kuwa ya d’auki Safnah ya d’aura ta a cinya yana ta lelleyata tamkar k’aramar yarinya Rahma ta bank’o musu k’ofa ko sallama.
Ko ta Kansu bata bi ba ta kama hanyar d’akin ta Nawaf ne yace
“Me daga ina kike?” Ya tambaye ta.
Wani wawan kallo ta watsa mishi sannan tace
“Daga inda ka aike ni nake.”
“Ke! ni kike fad’awa haka?”
“Eh an fad’a ko zakayi wani abu ne?”
“Rahma wai ni kike fad’awa wad’an nan maganganun ko dai wani abu ne ya sameki?”
“Kutumar……..ni kacewa mahaukaciya?
Ai wallahi bazan yarda ba sai na nuna maka hauka na” tana gama fad’an haka ta nufi kitchen.
Bata dad’e da shiga ba ta fito hannun ta d’auke da wuk’a tana cewa
“Wallahi yau sai na nuna maka bani da hankali” ai kuwa wajen su ta fara tunkarowa da wuk’ar.
Nawaf ne yace da Safnah
“Mik’e ki shiga d’aki dan naga wannan Yau ba da hankalin ta tazo gidan nan ba.”
Yana rufe bak’in sa har Rahma ta k’araso wajen su yanka ta kaiwa Safnah Nawaf ya tare a hannun sa ta yanke hannun sa.
Da sauri ya tura Safnah d’aki ya rufe sannan ya juyo wajen Rahma.
Wasu tagwayen mari yakai mata har sau uku sannan yace
“Daman baki hankali ban sani Rahma!
Tun wuri kifita ki barmun gida idan kuma ba haka wallahi sai na lahira yafiki jin dad’i.”
Cikin kuka dan zafin marin da tasha tace
“Wallahi bazan bar gidan ba sai dai kacire gawa na.” tana gama ta juya ta shiga d’akin ta.
Baki bud’e Nawaf yake kallon Rahma dan shi har tsoro ta fara bashi.
Haka ya koma d’aki zuciyar sa yana mishi zafi tamkar zai fashe.
Washe gari Rahma bata fito ba har sai da Nawaf ya fita zuwa office sannan ta fito.
Koda ta fito bata sami Safnah har ta gama zaman ta bata fito haka ta hak’ura ta koma d’akin ta ta kwanta barci.
Hajiya Saratu taje wajen bokan ta tayi mishi bayanin komai da abinda suke so ayi musu ai kuwa nan da nan ya kama aiki akan Safnah.
Wani bak’in hayaki ya tura mata ita kuma tana kwance taji wani irin abu yana zagaye ta addu’a ta kamayi duk wanda yazo mata a hankali ta fara jin dauk’in abin har tazo ta daina ji.
Bokan ne yace da Saratu
“Gaskiya wannan aikin zaiyi yuwa dan wannan yarinyar ta dage da addu’a sai dai ayi mata wani abu daban kafin mu samu nasarar kashe ta.”
“To boka hakan ma yayi kuma naji dad’in hakan ina jira naga an canza mata halitta.”
Wani irin dariya yayi sannan yace
“An gama.”
Haka ya cigaba da wasu tsafe-tsafen sa ya dad’e yanayi sannan yace
“Komai yayi dai-dai an gama ki tashi kije gida.”
Haka Hajiya ta mik’e ta fita tana wani wawan asher.
Safnah barci take amman tana jin jikin ta yana mata wani iri but bata damu ba dan tasan bata jin dad’in jikin jin abin ya dame ta ne yasa ta bud’e idon ta tana bud’ewa taga jikin ta gaba d’aya………..
*Wayyo Allah menene kuma a jikin ki baiwar Allah*????????????♀
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????
???????? *BA CIKI NA BANE!*????????
????????????????????????????????
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????
“`DEDICATED TO ALL MY FANS“`????????❤❤????????????????????????
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 76~80*
Safnah barci take but tana jin jikin ta yana mata wani irin ciwo amman bata damu ba dan tasan bata jin dad’in jikin ta jin abin ya dameta ne yasa ta bud’e idon ta tana bud’ewa taga wani bak’in abu yana shiga jikin ta addu’a Safnah take sosai dan gaba d’aya ta fita a hayyacin ta shi kuwa wannan abun yana ta yawo a jikin ta ya kasa shiga cikin fatan ta tsabar addu’a da Safnah takeyi haka wannan abin ya koma wajen boka ba’ayi nasara ba.
Sai da Safnah taji sauk’in wannan masifar sannan ta mik’e ta nufi toilet dan yin alwala.
Duk da ta mik’e amman addu’ar takeyi a zuciyar ta dan shine makarin ta.
*TO ‘YAN UWA MUSULMAI MAZA DA MATA KU DUBA KUGA YANDA SAFNAH TA RIK’E ADDU’A WANDA SHINE YA TSARE TA DAGA SHIGA MASIFAR SU RAHMA DA SARATU KU SANI FA BAD’AN WANNAN ADDU’A BA DA YANZU BA ITA A CIKIN DUNIYAR NAN ADDU’A NE YA CECETA DAGA HANNUN AZZALUMAN MUTANE TO ‘YAN UWA MURIK’E ADDU’A DOMIN ITACE MAGANIN DUK WATA MASIFA DA ZATA TUNKARO MU ALLAH YA TSARE MU AMEEN*
Alwala tayi sannan ta fita ta fara sallah Wanda ita kanta bata san yawan adadin abinda tayi ba.
Bayan ta idar ne ta zauna addu’a itace bata tashi akan sallaya ba sai bayan la’asar don d’aura abinci.
Hajiya Saratu tana komawa gidan ta d’auki waya ta k’ira Rahma ta fad’a mata duk abinda sukayi da boka kuma Safnah halittan ta zai canza.
Wawan tsalle Rahma tayi sannan tace
“Kai amman naji dad’i sosai Momy baki ta6a fad’a mun abinda yamun dad’i kamar wannan ba.”
Saratu ma dariya tayi sannan tace
“To fa yanzu ki tashi kije parlour ki zauna kisha kallo dan kuwa yanzu zakiga abin al’ajabi.”
Da sauri Rahma ta mik’e ta fita zuwa parlour sannan tace
“To Momy gani nafita amman ita d’in bata fito ba.”
Dariyan mugun ta Saratu tayi sannan tace
“To gaggawan me kike yi ne ‘yar albarka?
Ai komai dare zata fito kawai tana fitowa ki kirani a waya.”
“To Momy zan kira ai har d’aukan ta a photo zanyi na tura miki.”
Haka dai sukayi ta hiran su sannan sukayi sallama.
Rahma tana zaune tana ta jiran Safnah amman ko motsin ta bata ji ba haka har ta gaji ta kwanta barci.
Ko da Safnah ta fito a kwance ta samu Rahma haka ta wuce kitchen ta d’aura tuwon semo da miyar ku6ewa d’anya.
Ai kuwa nan da nan gidan ya cik’a da k’amshi na abinci.
Da yake abincin ba wani yawa ne da shi ba nan da nan ta gama tazo ta fara gyara gidan.
Ba laifi yanzu taji sauk’in jikin ta sosai batayi tsammanin zatayi wani aiki ba but sai gashi har gyaran gida tayi.
Ko ina sai da ta gyara sannan ta saka turaren wuta ta koma d’aki danyin wanka.
K’amshin turaren ne ya tashi Rahma daga barci mamaki ne ya kamata jin ko ina na gidan yana k’amshi tambayan kanta take tana cewa
“To kodai da halittan nata ya chanza ne Hindu tazo ta gyara gidan???
To kodai Nawaf ne dan ba k’aramin aikin shi bane…” Haka tayi ta surutanta ganin tana 6atawa kanta lokaci yane yasa ta mik’e ta koma d’akin ta.
Tana shiga wayan ta tafara ringing da sauki ta dauka ganin Momyn ta.
“Ke ba nace ki kirani ba amman kika k’i kira na!” Ta mata maganar a tsawace.
“Momy bata fito ba fa har yanzu dan ni barci ma nayi da na tashi kuma naga gidan a gyare har an saka turaren wuta amman kiyi hak’uri zan kiraki zuwa ajima.”
“Ban yarda yanzun kije d’akin ta ki gani idan abin yayi aiki ke bakisan irin kud’in da na kashe akan wannan aikin ba ko?”