BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

“Momy kinsan dai Nawaf ya hanani shiga d’akin ta ko?
Kuma jiya munyi fad’a yanzu idan yaji wallahi na shiga uku.”

“Ke dakata kina nufin kina jin tsoron Nawaf?
To ni kuma umarni ne na baki kiyi maza kije d’akin ta ki gani.”

“To Momy.”
Tana fad’an haka ta kashe wayan.

Toilet ta shiga tayi alwala ta fito ta had’a sallahn azahar da na al’asar duk da magriba ta kawo kai sannan ta wuce zuwa d’akin Safnah.

Tana zuwa ta sameta zaune a gaban mirror tana tsara kwalliya ba ko sallama ta fad’a d’akin da mamaki take kallon ta sannan tace
“Ke kina nufin ba abinda ya sameki har wani kwalliya kikeyi?
Cab! Ai wallahi baki isa ba.”

Mik’ewa tsaye safnah tayi sannan tace
“Ban gane me kike nufi ba?” Ta tambaye ta.

“OK baki gane me nake nufi ba ko?
To yanzu zaki gani.” Ta k’arasa maganar tana k’arasowa wajen Safnah.

Ita dai Safnah binta kawai take da ido da kuma mamakin abinda Rahma take nufi Safnah bata ankara ba taji mari a fuskan ta.

Da sauri Safnah ta rik’e kuncin ta tace
“Rahma ni kika mara?”
“Eh na mare ki ko zaki ra……..” Bata k’arasa ba taji sauk’an mari har biyu.

Sannan Safnah tace
“Ke kin isa ki shigo har d’akina kice zaki d’aga hannu ki mare ni!
To wallahi kinyi kad’an kuma kiyi gaggawan barmun d’aki tunkan na miki wanda yafi haka.” Ta k’arasa maganar ta mai nuna ta da d’an yatsa.

Rahma ido da baki ta bud’e tana kallon Safnah dan tsoro ma ta fara bata abinda bata tab’a gani b……katseta Safnah tayi da cewa
“Ki fita mun a d’aki nace”
Ta fad’a da k’arfi.

Da sauri Rahma ta juya tabar d’akin dan ita gaba d’aya ta tsorata da Safnah.

Ta komawa d’aki ta kira Saratu a waya ta fad’a mata komai itama kanta tayi mamaki cewa tayi
“To kodai bokan baiyi aikin bane?”

Rahma ce tace
“Nima dai haka nake tunani Momy.”

“To kinga dai yanzu dare yayi gobe da asuba zan tafi wajen Sa dan na gaji amun ma kankat komai yazo k’arshe ko ita da Nawaf d’in ne a kashe mu huta.”

“Yauwa Momy duka a kashe su nima zan fi jin dad’in haka.”

“Karki damu angama.”
Ta kashe wayan.

Safnah ta shirya tsab cikin k’ananan kaya riga da wando Wanda suka kamata suka bayyana suran jikin ta kayan ba karya sun mata kyau.

Sai da akayi sallah magriba Nawaf ya dawo Safnah tana zaune a parlour taji shigowar motar sa ta sauri ta mik’e ta fita da gudu tana cewa
“Sweetheart oyoyo.”

Da sauri shima ya rungume ta yace
“Babyna ya kike ya jikin ki?”
Wani kallo da ta mishi ne ya sake rikitashi sannan tace
“Sweetheart Yau shine ko ka kirani ko.” Ta fad’a cikin shagwa6a.

D’aukan ta yayi sannan yace.
“Sorry Baby wallahi Yau aiki ne yamin yawa kuma nabar wayan a mota.”

Bud’e kofa yayi dai-dai da fitowar Rahma daga d’aki.

Ido ta zuba musu tana kallon su shi kuwa Nawaf ganin haka ne yasa shi had’a bakin sa da na Safnah waje d’aya ya fara kissing nata.

Tun Nawaf yana hankalin Sa har ya fara fita daga hayyacin sa.

Rahma kuwa tana kallon su ganin abin yanason fasa mata zuciya ne yasa ta k’arasawa wajen su da sauri ta ja Safnah ta fad’i k’asa sannan tace da Nawaf
“To dan akuya yanzu me kagani a jikin wannan har kana wani hauk…….”

Katse ta yayi da wawan naushi da ya kai mata baki.

“Daman baki da hankali?
Safnah kika ja ta fad’i k’asa?
To yau sai kin yabawa aya zakin ta” nan ya sake kai mata mari again ya sake cewa
“Nine da kike kira da dan akuya ko?
To Yau zan nuna miki akuyanci na.”
Ya d’aga hannu zai kai mata duka Safnah ta rik’e tace
“Haba sweetheart yaushe wannan zata tayar maka da hankali har kana cacatun maki da ita?
Dan Allah kayi hak’uri ka k’yale ta sabo ni.” Ta gama maganar tana kallon Rahma.

Murmushi Nawaf yayi sannan yace
“To Baby na kyale ta saboda ke.” Yana gama fad’an haka ya d’auki matar sa suka koma d’aki.

Ita dai Rahma da ido kawai take binsu dan al’amarin yafi karfin ta.

Da gudu ta koma d’aki ta fad’a kan gado tana kuka dan ita har ta manta da cikin da yake jikin ta.

Sai da tayi mai isarta sannan ta d’auki waya ta kira Saratu.

Nan da nan ta fad’a mata duk abinda akayi ce mata tayi
“Kiyi hak’uri komai yazo k’arshe insha Allah daga gobe bazaki sake ganin su a doron k’asa ba.

A haka sukayi sallama sai da safe.

 

Washe gari da asuba Saratu taje wajen boka bayani ya mata akan komai sannan yace mata
” akwai wani aiki Wanda yana da nasara sosai sannan yana da hatsari sosai.”

“To boka fad’a mun hatsarin sa naji dan nasan ba abinda zai gagare mu.”

“Idan wanda kukayiwa abin bai sameshi ba to kanku zai koma ko da kuwa mutuwa ne ko hauka ko wani ciwo daban amman idan kukayi nasara zakuji dad’i .”

Gaban Saratu ne ya fara dukan tara-tara dan ita a rayuwar ta ba abinda ta tsana kamar mutuwa…….

 

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????

???????? *BA CIKI NA BANE!*????????

????????????????????????????????

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ*​​????✍????

​“`DEDICATED TO ALL MY FANS​“`????????❤❤????????????????????????

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Page 81~85*

Gaban Saratu ne ya fara dukan tara-tara dan ita a rayuwar ta ba abinda ta tsana kamar mutuwa amman wata zuciyar take raya mata da ta yarda ta amince ba abinda zai biyo baya sai nasara.

Boka ne yace mata
“Ke fa muke sauraro kinyi shiru.”

Cikin rawan murya Saratu tace
“To boka na amince amman dai zamuyi nasara ko?”

Dariya boka yayi cikin khaukausar murya sannan yace
“Wannan ne ban sani ba,
Yanzu wanne kike so ayi musu?”ya tambaye ta.

” Ina so a kashe Safnah da Nawaf sannan Hajiya Fatima da Hindu a haukatar da su shi kuwa mahaifin Nawaf a karkata hankalin sa ya dawo gare mu sai abinda muka ce mishi.”

Wani dariyan Boka ya sake yi sannan yace
“Wannan duk mai sauki ne idan zakubi dokokin aikin.”

“Ina sauraron ka Boka.”

Wani bak’in k’ullin magani ya mik’a mata yace
“Wannan shine Wanda za’a zubawa su yaran a abinci amman sharad’in sa idan har basuci abinci ba yayi minti goma to fa kanku zai dawo abin.”

Murmushi tayi sannan tace
“Wannan mai sauk’i ne ba mai wuya ba komai zaiyi.”

Wani k’ullin ya sake mik’a mata sannan yace
“Wannan shine na mahaifiyar tasu ki tabbatar kin zuba musu a k’ofar da zasu taka su wuce,
Amman idan kika bari wani ya ganki ke da hankali har abada dan abin kanki zai dawo.”

Cikin Saratu ne ya murd’a kuuuwwww sannan tace cikin rawan murya
“To Boka insha Allah…..” Katseta yayi da cewa
“Ke anan ba’a kira mana Allah domin ba abinda yace muyi ba muke yi.”

“Tuba nake boka! ba Wanda zai ganni bare kuma abin ya dawo kaina.”

“To ki ajiye mana kud’in mu ki tafi.”

Haka ta ciro kud’i masu yawa ta ajiye mishi sannan ta kama hanya ta tafi gidan Nawaf direct.

Da yake yau Saturday ne Nawaf yana gida suna ta faman shan soyayya da Matar sa.

Tana shiga direct d’akin Rahma ta nufa tana kwance tana ta faman shan barci.

A bakin gadon ta zauna sannan ta fara rashin ta.

Tana tashi taga Momy ta da sauri ta firta
“Momy kece kika zo?”
“Eh nice domin wannan babban aiki ne bana son wasa a ciki.”
“Momy kinje wajen bokan ne?”
“Eh yanzu haka ma a wajen shi na tashi” ta k’arasa maganar ta mai ciro magaggunan,
Nuna mata tayi sannan tace
“Kinga wannan manya ne sannan idan bamubi dokokin sa ba kanmu zai koma?”
“What! Momy wallahi banaso na hak’ura idan har zai dawo kai na, ko kin manta yanda muka sha fama da ita ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button