BA CIKI BANE

Daka mata tsawa tayi sannan tace
“Ke baki da hankali ne?
Ko kina tunanin nayi asarar duk kud’in da na kashe?
To tun wuri ki canza tunani.”
Kallon ta tayi sannan tace
“Momy yanzu idan bai samesu ba kanmu zai koma fa kika ce.”
“Eh amman kiyi mana fatan nasara mana yanzu fa idan aiki yayi kyau yanzu mune da jin dad’in duniya fa.”
Murmushi Rahma tayi sannan tace
“Gaskiya ne kuma fa Momy yanzu duka dukiyar shi zai dawo hannun mu.”
“Kwarai kuwa ‘yar gari yanzu rik’e maganin na miki bayani.”
Haka Rahma ta karb’a Saratu tayi mata bayanin komai akan yanda zatayi.
Rahma tayi murna sosai dan yanzu ji take kamar ya gama cika.
Saratu ce tace
“Yanzu ina suke dan nasan yau yana gidan.”
“Suna cikin d’aki kina gashi kamar maye kullum yana manne da ita.”
“Hmmm ai koma menene karshen sa yazo, to ni zan wuce can gidan nasu sai kinji waya na.”
“To Momy nagode sosai naji dad’in samun ki uwa.”
“To zan wuce .”
Haka ta fito parlour ba kowa ta fita ta tafi.
Ta window’n d’akin Nawaf yaga fitan ta mamaki ne ya kamashi tambayan kanshi yake akan yaushe tazo?Amman ina ba amsa.
Safnah ce tace
“Sweetheart tashi muje kitchen mu d’aura breakfast time ya tafi.”
Mik’ewa yayi da sauri yace
“Sorry Baby na barki da yunwa ko?”
“No sweetheart tashi muje kawai.”
Haka suka nufi kitchen suka kama aiki.
Nan da nan suka kammala breakfast nasu dankali da kwai suka soya sai ruwan tea.
A dining suka jira sannan suka koma d’aki danyin wanka.
Suna shiga Rahma ta fito da kullin maganin nan ta bud’e abincin ta zuwa ta koma da sauri tana dariya.
Suna shiga Safnah wani mugun zazzabi ya rufe ta daman tun suna aiki ta fara jinsan.
Kan kace me jikin ta yayi zafi sosai sai kuma ga amai nan ta shiga kwara shi.
Hankalin Nawaf ba k’aramin tashi yayi ba da sauri ya d’auki wayan shi ya k’ira Dr-Sabir yana d’auka yace mishi
“Ga muna nan zuwa Safnah ba lafiya.”
Bai jira yaji mai zaice ba ya katse wayar sa.
Hijabin ta ya d’auko ya saka mata sannan ya d’auke ta zuwa mota.
Da sauri mai gadai ya bud’e mishi gate ya fita da gudu bai tsaya a ko ina ba sai hospital.
Yana zuwa aka tare shi aka fito da ita aka tafi da ita emergency dan ta galabaita.
Saratu kuwa da taje gidan su Nawaf ba kowa a parlour hakan ne yasa cewa
“Yauwa basu tashi a barci ba.”
Nan taje k’ofar d’akin Hajiya Fatima ta barbad’a wannan maganin sannan ta dawo k’ofar d’akin Hindu shima ta barbad’a har zata fita taga abinci a dining ai kuwa da sauri ta k’arasa wajen ta bud’e shima ta zuba masa.
Ashe duk wannan abin a idanun Hindu da Hajiya da Alhaji ne.
Ta gama breakfast ta shirya su a dining ta shiga d’akin ta fitowar da zatayi ne taga Saratu tana barbad’awa su Hajiya Fatima abu a k’ofar d’aki shine Hindu ta kira Umman ta ta fad’a mata suma suka lek’o suna kallon ta.
Kowa mamaki yake akan me Saratu tazoyi musu harda magani? Amman ina ba amsa.
Da sauri ta fita tabar gidan tana murna sosai akan yau burin su zai cika.
Hindu ce ta k’ira mai gadi tace yazo ya share musu wajen ya goge.
Ai kuwa nan da nan yazo ya share ya goge wajen tas sannan suka fito.
Hindu ce tace
“Umma waton wannan Matar tazo ne ta kashe mu har gida! To gaskiya ba zamu barta ba kawai mu fad’a wa ‘yan sanda suzo su kamata dan gaskiya idan aka barta abinda zatayi gaba sai yafi wannan.”
Hajiya Fatima da tayi tagumi a zaune ce tace
“Hmm nima dai gaskiya nayi mamaki amman mu barta ita da Allah duk abinda tayi zai koma kanta insha Allah tun a duniya Allah zai nuna mata.”
Alhaji kam tsabar bakin ciki kasa magana yayi.
Wayar Hindu ne ya fara ringing ganin number Nawaf ne yasa dauka da sauri ce mata yayi
“Kizo asibiti ki sameni yanzu.”
A tsorace tace
“Bro lafiya meye ya faru? Waye ba lafiya?”
“Safnah ce kizoki yanzu” yana fad’an haka ya katse wayar.
Hajiya ce tace
“Lafiya meye ya faru?”
“Wai Safnah ce ba lafiya tana asibiti bari naje.”
Haka ta mik’e ta fita da sauri ta kira driver suka tafi.
Saratu tana komawa gida ta kira Rahma a waya tace
“Kin zuba musu ne?”
“Eh Momy na zuba amman har yanzu basu fito sunci ba.”
Mik’ewa Saratu tayi sannan tace
“Tun yaushe kika zuba?”
“Eh Momy zaikai 30 minutes.”
Da karfi Saratu ta firta
“Na shiga uku ke kije kice su fito Ku karya.”
“Saboda me fa Momy ai naga duk lokacib da suka ga dama zasu fito suci.”
“Ke dan ubanki idan har yafi 10 minutes abin zai koma kanki ne fa kije d’akin nasu yanzu nace.”
“Wayyo Allah Momy na shiga uku meyesa baki fad’a mun tun jiyan ba sai yanzu? Wallahi bazan yarda ba idan har ya dawo kai na.”
Tana fad’an haka ta fita zuwa d’akin su.
Koda taje d’akin a bud’e haka ta shiga da sallaman ta amman ba kowa ko ina ta duba bata samu kowa ba da gudu ta fito ganin ba motar Sa ce ya sake tayar mata da hankali.
Wajen mai gadi ta k’arasa ta tambaye ina suka tafi.
Ce mata yayi
“Ai amarya ce ba lafiya Alhaji ya tafi da ita asibiti.”
Hannu ta d’aura a kai tana ta wayyo na shiga uku mai gadi ne yace
“Lafiya Hajiya kike wannan kuka?”
Kallon shi tayi sannan tace
“Ina ruwanka da ni dan shisshigi kawai.” Ta mishi tsaki ta wuce ciki.
Momyn ta ta kira a waya ta fad’a mata halin da ake ciki itama cewa tayi
“Na shiga uku ni saratu wannan wanne irin masifa ne?”
Dashewa Rahma tayi da kuka tana cewa
“Wallahi Momy bana son wani abu ya sameni gaskiya ki koma wajen bokan yayi abu d’aya.”
“Ke ki barni da tashin hankalin da nake ciki ni nafiki damuwa duk da ni nayi nasara ba wanda ya ganni ki godewa Allah.”
Haka dai sukayi tayi a tsakanin su sannan sukayi sallama akan zasu dinga waya a tsakanin su.
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????
???????? *BA CIKI NA BANE!*????????
????????????????????????????????
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????
“`DEDICATED TO ALL MY FANS“`????????❤❤????????????????????????
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 86~90*
Su Hindu suna shiga asibiti suka samu Nawaf a tsaye yana jiran a fito da Safnah.
Suna gaisawa Hindu tace
“Bro me yake damun ta ne?”
Nan da nan ya fad’a mata iya abinda yasani da aikin da sukayi tare.
Addu’ar samun sauki.
Hindu basu dad’e da zuwa ba aka fito da Safnah d’aura da ruwa hannun ta.
D’aki aka wuce da ita sannan suma suka Ni bayan su.
Dr-Sabir ne yace da Nawaf
“Abokina gaskiya wannan Babyn yana wahalar da Momyn shi.”
Kallon Sa Nawaf yayi yace
“Wallahi kuwan abokina amman ina fatan ba wata matsala ko?”
“Babu komai daman rashin cin abinci ne yaja mata wannan da alamu dai baka kula kana bata abinci akan lokaci.”
“No ba haka bane kadai san bana yini a gida amman daddare tare muke ci.”
“To yanzu dai Ka kikaye munyi iya k’ok’arin mu yanzu dai ba wata matsala tana tashi Ka bata abinci.”
“To nagode sosai abokina Allah yabar zumunci.”
Gaba d’ayan su ne suka amsa da
“Ameen thumma ameen.”
Nawaf ne ya kalli Hindu sannan yace
“Sis ki zauna da ita a nan zanje gida na d’auko breakfast d’in da sukayi na kawo kan ta farka.”
Kallon Sa Hindu tayi tace
“Bro Yau bakasan abinda ya faru ba kenan kake son zuwa gida d’aukan abincin da aka gama barbad’e shi.”