BA CIKI BANE

Da mamaki Nawaf yake kallon Hindu sannan yace
“Kamar ya ban gane ba kimun bayani.”
Ai kuwa nan da nan Hindu ta fad’awa Nawaf abinda ya faru gaba d’aya a gaban su akayi shi.
Nawaf yayi mamaki sosai sannan ran shi ya b’aci dan ba abinda ya ta6a 6ata mishi rai kamar wannan.
Iska mai zafi ya huru a bakin sa nan yace
“Wad’an nan mutanen me suke nufi ne akan mu?
Mu suke son hallakarwa!
Cab! Ya zama dole nayi maganin su na gyara musu zama.”
“No Bro Umma tace kar a kulasu kar ma mununa mun gani insha Allah abinda sukayi mana sai ya koma kansu.”
“Hmmm Sis ki bari kawai Safnah tana samun lafiya wallahi ni bazan bar suba sai nayi maganin su,
Yanzu bari naje restaurant na siyo mana abincin sai mu k’arasa maganar.”
“To Bro sai Ka dawo.”
Haka ya juya ya tafi zuciyar sa sai faman tafasa take mishi.
Rahma tana tsaye a parlour ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman zarya take taje ta dawo haka tayi tayi a parlour’n wayan ta ne ya fara ringing da sauri ta d’auka ta kara a kunne tace
“Hello Momy.”
Saratu ce tace
“Ke kina lafiya dai ko?
Dan naje wajen bokan yace ba abinda zai iya.”
“Eh Momy yanzu dai lafiya qlau.”
“To kina jin wani abu kimin waya dan musan nayi amman tunda har yanzu ma ba abinda ya faru inajin ba komai da zai faru.”
“Momy gaskiya nikam a tsorace nake sosai kuma ga abinci nasu har yanzu basu dawo ba.”
“Kar kidamu da wannan ke dai yanzu kiyi ta kanki.”
“To Momy.” Kad’ai tace ta kashe wayan dan yanzu ita har ta fara tsanar Momyn nata.
Zama Rahma tayi a parlour tayi tagumi tana tunanin me zai faru da ita.
Sai misalin k’arfe d’aya Safnah ta farka Alhamdulillah taji sauki sosai dan bata jin komai sai yunwa tana bud’e bakin ta tace
“Ya Nawaf yunwa nake ji.”
Da sauri ya k’araso wajen ta yace
“To tashi muje ki wanke bakin ki.”
Haka suka mik’e suka nufi toilet sai da suka gama abinda zasu sannan suka fito.
Hindu tana zaune ta zuba musu ido dan ita sha’awa ma suke bata addu’a take a zuciyar ta itama Allah yabata Wanda zai kula da ita haka.
Haka suka dawo suka zauna ya fara sa mata abinci a baki tana ci sai da ta k’oshi sannan yabar bata.
Haka suka yini a asibiti sai bayan isha’i sannan aka sallame su.
Sai da suka tsaya a gidan su Nawaf suka ajiye Hindu suka gaida Umma sannan suka koma.
Nawaf baiyiwa Umma maganar abinda ya faru d’azu ba saboda bayason Safnah taji ta tada hankalin ta.
Sai da suka wuce restaurant suka sake siyo wani abincin sannan suka dawo gida.
Da suka dawo gidan ba kowa a parlour Rahma tana ciki haka suka wuce cikin d’aki.
Sai da sukayi wanka suka shirya tsab sannan suka zauna cin abinci suna ci suna d’an ta6a hira haka sukaci suka tashi.
Hamma Safnah tayi tace
“Ya Nawaf ni zan kwanta dan wallahi barci nake ji sosai.”
“To My Angle kizo na saki barci kinji.”
Haka ya jata jikin sa yana shafan bayan ta nan da nan barci ya d’auke ta.
Rahma yini sukayi suna waya da Momyn ta dan duk minti biyu sai sunyi waya sai bayan magriba ne jikin Rahma ya fara mata k’ayk’ayi abu kamar wasa tana sosawa ya fara mata wasu manyan kuraje.
Tun tana iya d’aga waya har yazama ta kasa jikin ta duk ya kunbura kanta ya zama k’ato leben ta duk sub kunbura.
Fatan jikin ta a lokaci d’aya ya chanza ya dawo bak’i k’irin.
Rahma a lokaci d’aya ta koma wani halitta Wanda idan Ka ganta sai Ka tsorata.
Safnah tanayin barci Nawaf ya zare jikin sa a nata ya mik’e ya kama hanyar d’akin Rahma dan Yau sai ya mata mugun duka kuma ya k’orata gidan su a daren nan.
Yana shiga yaga d’akin baki wutan ba’a kunne yake ba haka yaje ya kunna wutan.
Yana juyawa yaga abu a kwance k’ato bak’i k’irin ai ina da gudu Nawaf ya fita yana addu’a yaje ya rude musu d’aki sai faman haki yake.
Tambayan kanshi yake menene wannan a d’akin Rahma?
To ina Rahma take? Ina bai samu amsa ba cewa yayi
“Sai na koma nagani menene yake faruwa a d’akin.”
Haka ya bud’e k’ofar yana addu’a ya sake komawa.
Kamar dai yanda ya barta tana kwance akan carpet.
A hankali yake magana yace
“Dan Allah wanene anan?”
K’ok’arin magana take amman takasa sai dai kanji tana wwuuuuuu wuuuuu.
Sake matsowa Nawaf yayi sannan yace
“Kai waye kuma me yakawo Ka gidan nan.”
Hannu ta d’aga mishi ganin lalle a hannun ta da kuma rigan da yake jikin ta hijab bak’i ne ya tabbatar mishi cewa Rahma ce ai da sauri ya mik’e yana cewa
“Rahma kece kika dawo wannan abin?”
Ai kuwa da gudu ya fita yabar d’akin ya koma parlour yana haki.
Wayar shi ya d’auka ya kira su Umma abin ya basu mamaki nan duka ce mishi suna zuwa.
Basu dad’e da yin waya ba suka zosu.
Jansu yayi zuwa d’akin ta, suma sunji tsoro da mamaki matuk’a dan har basa son ganin ta.
Hajiya Fatima ce tace
“To yanzu sai ka k’ira iyayen ta Ka fad’a musu.”
Haka Nawaf yayi ta k’iran wayan Saratu amman bata dauka ba, sai da ya k’ira wayan mahaifin ta sannan ya samu ya d’auka
Gaisawa sukayi cikin mutun ci da girmama juna sannan Nawaf yace
“Abba daman Rahma ce ba lafiya jikin yayi tsanani na kira wayan Hajiya bata d’auka ba shine na k’ira.”
“Subhallahi!
Me yake damun ta?”
“Abba jikin nata dai sai kunzo kun gani.”
“To nima tunda na dawo banga mahaifiyar tasu ba amman bari na shiga ciki na fad’a mata gamu nan zuwa.”
“To Allah sai kunzo.” Haka suka kashe wayan.
Mik’ewa Alhaji yayi ya nufi d’akin Saratu.
Abin ba k’aramin mamaki ya bawa Abban Rahma ba ganin Saratu tsindir duk ta birkita d’akin ta ko ina ta juya shi sai faman ihu take.
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????
???????? *BA CIKI NA BANE!*????????
????????????????????????????????
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????
“`DEDICATED TO ALL MY FANS“`????????❤❤????????????????????????
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
????????????????????????
*Page 90~100*
“Innalillahi wa inna illahi raju’un!”
Shine kallaman da Alhaji yake fad’a a bakin sa sannan ya ce
“Saratu lafiya kuwa?
Ko dai aljanune suka shafeki….” Yanke managanar yayi ganin ta tunkaro shi da wani k’atun k’arfe Wanda shima kanshi baisan a ina ta samo shi ba.
“Ke Saratu baki da hankali ne?meye yake damun?”
Dariya tayi tace
“Hankali bani hankali kai kai hankali.” Sai kuma ta fara rawa tana cewa bani da hankali” sai faman tsalle take a tsakiyar d’akin.
Ganin abin da gaske ne yasa Alhaji kulle ta a d’aki ya saka key sannan ya d’auki waya ya kira Nawaf.
“Assalamu alaikum Abba.”
Shiru Alhaji yayi dan baisan ma me zai ce musu ba Nawaf ne yace
“Abba lafiya kayi shiru?”
Ajiyar zuci yayi sannan yace
“Nawaf bazamu samu daman zuwa ba domin muma nan ba lafiya ba.”
“Subhallahi!
Abba waye ba lafiya?”
“Saratu ce gashi yanzu haka ta hauka ce.”
“Hauka fa kace Abba!”
“Kwarai kuwa domin yanzu haka ko kaya babu a jikin ta.”
Dif Nawaf ya kashe wayan sannan yace
“Umma mu tafi mubar wannan yarinyar a gun.”
Hajiya Fatima ce tace
“Saboda me zamu tafi mu barta bayan kana ganin halin da take ciki.”
“Umma wannan dai da alamun abinda sukayi ne ya koma kansu yanzu fa mahaifin ta yake sheda mun itama Mahaifiyar tata ta haukace.”