BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

“Hauka fa kace Nawaf?”
“Eh Umma yanzu Abba ya fad’a mun.”

Hindu ce tace
“Umma waton abinda tayi mana ne ya koma kanta, da yanzu mune da wannan haukar da kuma wannan abinda Rahma ta koma.”

Hawaye ne suka zubo a idanun Hajiya Fatima sannan tace da Nawaf
“Kuzo muje gidan nasu mu duba ita Hajiyar.”

Hindu ce tace
“Haba Umma meye sa zamu tafi dubata bayan duk abinda ya faru su suka jawa kansu dafa yanzu mune a cikin wannan masifar.”

Kallon ta Umma tayi tace
“Koma menene muje ai Ba zamu biye musu ba duk abinda suka mana mu musaka musu da alkhari shine tsakanin mu da su.”

Badan Hindu taso ba suka fito Umma ce tace
“Wai ina Safnah ne nifa ban ganta ba tunda mukazo Allah yasa dai ba jikin bane.”

Nawaf ne yace
“A’a Umma ba jikin bane tayi barci ne shiyasa ko na tashe ta ne?”
“A’a Ka barta ta huta dan tana buk’atar hutu sosai.”

Haka suka shiga mota suka kama hanyar gidan su Rahma.

Mahaifin su Rahma yana tsaye ya rasa me yake mishi dad’i yajiyo Saratu tana ta faman bige-bige sai faman tarwatsa d’akin take shine abinda ya fito da Hanifa a d’akin ta da gudu.

Ganin mahaifin ta tsaye yasa ta cewa
“Dady lafiya naji a d’akin Momy ana ta fashe fashe?” Ta tambaye sa.

Shiru ya d’anyi sannan yace
“Hanifa sai dai kiyiwa mahaifiyar ku addu’ar samun lafiya domin ta haukace.”

A razane Hanifa tace
“Haukace fa kace Dady?”
“Eh Hanifa….”
Jin fashewar wani k’alba ne yasa su yin shiru suka k’arasa k’ofar d’akin.

Hanifa ce tace
“Dady kabari kar ka bud’e ta kana jin abinda take a nemo malamai ayi mata rukiya inajin aljanu ne.”

“To amman kina jin dai kar tajiwa kanta ciwo kinji dai k’alba take fasawa.” Key d’in ya saka ya bud’e d’akin yana saka kanshi ta jefo mishi k’alban turare a kai nan da nan jini ya wanke mishi fuska.

Da gudu ta fito zata fita kenan su Nawaf suka shigo da hanzari Nawaf ya rik’e ta sannan Mahaifin su Rahma ma yazo suka rik’e ta suka samu suka sakata a d’aki suka rufe.

Mahaifin Rahma ne yace
“Wannan wanne irin masifa ne ace a dare d’aya mutum ya haukace haukan ma ba mai sauki ba mai tsanani Allah Ka shiga mana al’amarin.”

Hajiya Fatima ma hawaye take idan ta tuna da yanzu ita ce cikin wannan masifar.

Hanifa ce wacce sai faman kuka take tace
“Dady duk wannan abinda kaga Momy tanayi itace tajama kanta itama Anty Rahma Allah ya rufa mata asiri dan komai tare sukeyi.” Sai kuma taci gaba da kukan ta.

Cikin rashin fahimtar maganar ta mahaifin su yace
“Kamar ya itace ta jama kanta Hanifa ki mana bayani yanda zamu gane.”

Goge Hawayen ta Hanifa tayi tace
“Dady jiya Momy taje wajen boka ta k’arbi magani akan zasu zubawa Nawaf da Safnah a abinci suci sannan zasu zubawa Hajiya Fatima da Hindu su haukace sharad’in da aka basu shine kar wanda yagani suna zuba wannan maganin, to Dady inajin wani ya gansu ne.”

Hindu ce tace
“Tabbas a gabana Hajiya taje gidan mu tana zuba mana magani a bakin k’ofa ganin haka ne yasa ni k’iran Umma a waya suma suka fito suka gani baki d’ayan mu.”

Zuciyar mahaifin su Hanifa ne ya fara zafi nan da nan idanun sa suka chanza jikin shi ya fara rawa sannan yace
“Daman Saratu ke kika jefa kanki cikin wannan masifar?
To zaman ki a gidan nan ya k’are.”

Yana gama fad’an haka ya tunkari k’ofar d’akin da niyar bud’ewa.

Nawaf ne yace
“A’a Abba kayi hak’uri Ka barta saboda ita batasan halin da take ciki ba,
Ka k’aleta a cikin gida.”

Kallon sa yayi sannan yace
“Haba Nawaf ya za’ayi na zauna da wannan Matar a cikin gida na Matar da take bin bokaye!
Ni a rayuwana na tsani mutumin da yake bin bokaye yake shirka, wallahi Saratu na tsaneki sannan na sakeki saki Uku dan kar ki warke ki dawo mun gida.”

Kuka Hanifa ta fara tana cewa
“Haba Dady ya zakamun haka meyesa zaka kori Momy a gidan nan mu zauna da ita ko Allah zai shirye ta amman babu Ka yanke hukuncin ka.” Sai kuma taci gaba da kukan ta.

Hajiya Fatima ce tace
“Haba Alhaji idan rai ya b’aci bai kamata Ka yanke hukunci dawuri haka ba,
Da kayi hak’uri komai a hankali zai dawo dai-dai insha Allah.”

Alhaji bai kulata ba sai ma juyowa wajen Nawaf da yayi yace
“Nawaf dan Allah Ka saki yarinyar nan tabar maka gidan ka cikin da yake jikin ta kuma idan Allah ya sauketa lafiya sai a dawo maka da d’an Ka ko ‘yar ka.”

Kallon sa Nawaf yayi sannan yace
“Abba Ka gafarceni *BA CIKI NA BANE!* bansan da cikin ba dashi tazo gida na yanzu haka cikin yakai wata biyar zuwa shida……..” Kasa k’arasa maganar yayi ganin Alhaji ya fad’i.

Da sauri suka durkusa kanshi suna k’iran sunan shi amman ina ya dafe zuciyar shi Wanda sai zafi yake mishi yana numfashi sama-sama.

Hajiya Fatima ce tace
“Nawaf ka k’ira mai gadi ya taimaka maka ku kaishi mota mu tafi asibiti.”

Haka kuwa suka kira mai gadi suka kama sukayi asibiti da shi.

Tunkan su k’arasa asibiti rai yayi halin sa ya k’arasa yana kalman shahada daga nan basu sake jin motsin sa ba haka suka juya mota suka dawo gida.

Hanifa wacce aka bari a gida tana jin shigowar su taje wajen su amman sai ganin gawan Dadyn ta tayi.

Nan da nan itama ta fad’i sumammiya.
Ruwa aka samu aka yayyafa mata sannan ta farka.

Cewa take
“Dady dan Allah karka mutu Ka barni idan Ka tafi banida kowa su Momy sun haukace kai kuma gashi zaka tafi please Dady Ka tashi????.” Sai kuma taci gaba da kukan.

Hindu ce tazo ta durkusa a gaban ta tace
“Kiyi hakuri Hanifa duk mai rai mamaci ne yanzu Dady ba abinda yake buk’ata a wajen ki sai addu’a saboda haka kiyi shiru kici gaba da addu’ar ki kinji.”

Batayi mata magana sai dai ta rage kukan nata.

Haka Nawaf ya d’auki waya yaki ‘yan UWA da abokan arziki da yake duk ‘yan uwan su a nan suke nan da nan suka cika gidan Tun a daren.

Sai da akanyi mishi wanka aka shirya shi sannan su Nawaf suka dawo gida akan gobe karfe 7 za’ayi zana’iza.

Yana shiga ya tarar da Safnah sai zarya take a parlour ta k’asa tsayawa a waje d’aya.

Sallama yayi ya shigo kallon sa tayi tace
“A ina ka dawo 11:30?”
“A gidan su Rahma.”
“Gidan su Rahma!
Meye ya faru a gidan nasu?”
Nan ya bata labarin duk abinda ya faru har da abinda ya samu Rahma.

Tausayin su ne yakama Safnah sannan tace
“Dan Allah muje na duba Aunty Rahma.”
“OK muje.”
Shi kuwa Nawaf mamakin Safnah ma yake da irin wannan halin nata.

Suna shiga suka sameta kwance inda suka barta d’azo idon ta biyu sai faman hawaye take.

Safnah taji tausayin Rahma sosai dan itama hawayen take.

Nawaf ne yace mata
“Rahma kinga duniya ko?
Kinga dai masifar da ya jefa ki sannan kuma ya haukatar da mahaifiyar ki sanadiyar haka Allah yayiwa mahaifin ku rasuwa saboda bugun da zuciyar shi tayi da yaji labarin abinda kuka aika ta, kinga dai ya kaiku ya baro ku.” Yana gama fad’an haka yaja hannun Matar sa suka bar d’akin.

Kuka Rahma take sosai kamar ranta zai fita haka ta kwana bata ko rintsa ba.

Haka washe gari aka kai shi makwancin sa duniya kenan shi kenan Alhaji ya koma kamar ba’a halicce shi ba.

*”yan uwa gyara zuciyoyin mu karmuyi abu son ran mu domin duniya ba ma tabbata bace yau idan kai ne to fa hak’ika gobe ba kai bane saboda haka mu gyara sallah’n mu, mu yawaita istigifari domin neman rahma wajen Allah*

Haka aka zauna har bakwai sannan aka watse.

Duk wannan kwana kin Saratu tana kulle idan har akan bud’e za’a bata abinci to fa ‘yan zaman makoki sai sun tarwatse saboda duka take direct wajen zata fita, idan aka saka mata kaya kuwa ana barin d’akin zata cire su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button