BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

Rahma kuwa tana nan a d’aki kullum kuka ba bakin magana ko tana son abu bata san ya zatayi ta misalta ba.

Haka rayuwar su Rahma da Saratu ya kasance koda ‘yan uwan Saratu sukaji abinda suka ai kamata cewa sukayi bazasu iya zama da ita ba haka suka watse suka barta da Hanifa.

Allah sarki Hanifa ta rasa me yake mata dad’i gashi ita ba zata iya zuwa wajen Momyn ta ita kad’ai ba domin duka take sosai.

Ranan Hanifa zata mik’awa Momyn ta abinci ai kuwa daman tana jiran a bud’e k’ofa ana bud’ewa ta gefa a Hanifa kan kujera ta fita a gudu.

‘Yan UWA suna ganin ta suka bita amman ina sun kasa kamata bata tsaya a ko ina ba sai wajen bokan nata.

A nan ta samu waje ta zauna take rayuwar ta na hauka.

*BAYAN WATA HUDU*

Rahma tana kwace yau ba lafiya saboda ta tashi da bakuda.

Gashi ba daman tashi bare kuma magana haka tayi ta fama har ta fara zubar da jini.

Nawaf ne ya shigo ya sameta cikin wannan halin Umman shi ya kira a waya a fad’a mata cewa tayi gata nan zuwa.

Bata dad’e ba tazo tana zuwa suka d’auke ta zuwa asibiti.

Koda suka kaita su kansu doctors sunji tsoron ta haka suka karbe ta zuwa d’akin haihuwa.

Wani doctor ne ya fito yace da Nawaf
“Wannan bazata iya haihuwa ba sai dai amata ciyata don Babyn ya mutu a cikin.”

Haka su Nawaf suka biya yasa hannu sannan aka shiga da ita.

Haka akayi aiki aka fito da Baby aka mishi sitira aka kaishi.

Rahma da aka fito da ita kuwa ta samu ta fara magana a hankali dan bakin ya fara bud’ewa.

Su Nawaf suna dawowa ta fara neman yafiyar su.

Nan da nan ta fara basu labarin abinda duk suka aikata da Momyn ta.

Nan ta nemi yafiyar Safnah da Nawaf Safnah ta yafe amman Nawaf yace shi Sam bazai yafe mata ba dan sun cutar da su.

Sai da akayi ta rok’on Nawaf sannan ya yafe mata da k’yar.

Cewa yayi
“Na yafe miki iya Wanda zan iya amman tsakanin ki da mahalinccinki ni bazan iya ba,
saboda kin biyewa son zuciyar kika bar sallah har natsawon kwanaki dan burin ki to yanzu meye kika samu?
Duk wannan masifar da kika gani kad’an ne dan bakiga komai ba.”

Haka tayi ta kuka tana nadama.

Bayan sallah’n azahar Allah yayiwa Rahma rasuwa.

Haka aka d’auke ta aka tafi da ita gida aka mata komai aka kaita ma kwancin ta.

 

Bayan wata d’aya Safnah ta haihu ta samu santaleliyar ‘yarta.

Wayyo kuzo kuga murna a wajen Nawaf da su Hajiya da Hindu dan kuwa murna kamar zasu mayar da Safnah ciki.

Safnah kam taga gata ta ko wanne b’angare dan tana damun kulawa.

Ranar suna yarinya taci sunan Hajiya Fatima amman suna kiran ta da *SAMHA* yarinya mai arziki sun samu kaya kamar me.
Tsayawa na fad’a muku yawan kayan bata lokaci ne.

Haka rayuwar su Nawaf da Safnah ya kasace cikin farin ciki da kaunar juna hankalin su a kwance ba abinda yake damun su dan su yanzu summa manta da Rahma.

Saratu kuwa a wajen bokan ta mutu ba sitira ba komai haka suka turata a rami da kayan da yake jikin ta nan.

Su Nawaf kuwa yanzu ya sake samun matsayi a wajen aikin sa kud’i yana shiga mishi ta ko ina hankalin sa kwance basu da damuwar komai.

*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button