BA CIKI BANE

Murmushin mugun ta tayi sannan tace
“Nawaf zakaci Uban Ka wallahi.”
*CAB!! ME HAJIYA ZATAYIWA NAWAF NE?*
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????
???????? *BA CIKI NA BANE!*????????
????????????????????????????????
*STORY WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳ
ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 11~15*
Sai da suka sauke Hindu sannan suka wuce gidan su .
Suna shiga kowa d’akin shi ya wuce ba wanda yace da d’an uwan sa uffan.
Rahma tana shiga d’aki wanka ta shiga shaf-shaf tayi ta fito sannan ta zauna a gaban Mirror tana tsara kwalliya.
Tana gamawa ta d’auko akwatin kananan kayan ta ta d’auki wani shegen riga black da White d’in wando Wanda ya matse mata jikin ta sosai sannan ta kama gashin ta da ribom white sannan ta shafe jikin ta da turaren da Momyn ta ta bata tun auren su.
Parlour ta fito ta zauna tana jiran angon ta ya fito dan ita a tunanin ta yau ne first night d’in ta.
Shi kuwa Nawaf yana shiga d’aki kwanciya yayi dan gaba d’aya ji yake ya tsani Rahma baya son ganin ta kawai dai yabi umarnin mahaifiyar Sa ne.
Yana cikin haka ne cikin shi ya fara kukan yunwa dan rabon shi da abinci tun breakfast.
Tashi yayi ya nufi parlour ko ta kanta baibi ba ya wuce dining ba komai a kan dining ganin haka ne yasa shi yin tsaki sannan ya k’araso inda take zaune.
“Da muka dawo baki d’aura mana abinci bane?” Ya tambaye ta.
Wani irin kallo ta mishi sannan tace
“Kamar ya ban gane abinci ba! Ai kai yakamata ka kawo mana saboda yau ne kwanan Ka na farko a gidan nan.”
Wani mugun kallo ya watsa mata sannan yace
“A gidan Uban wa kika ta6a ganin anyi haka?”
“Ai kowa yasan wannan al’ada ce ko wanne ango yana kawo wa.”
Tsaki yaja mata sannan yace mata
“Kinyiwa kanki dan ni zanje naci abinci na ke kuma k’yasan yanda zakiyi” yana gama fad’ar haka ya fice zaibar parlour’n da sauri ta mik’e tasha gaban shi sannan tace
“Ai wallahi baka isa Ka barni da yunwa kai kaje ka cika cikin ka ba bayan nice nake buk’atar abinci ko dan d’an da yake ciki na.”
Wani irin abu yaji ya bigiA zuciyar sa dan bai ta6a tsammani zai aure Matar da zata shigo mishi da cikin shege gidan shi ba katse mishi tunani tayi da
“Kaga malam Ka tsaya kawai na saka hijabi na mu tafi dan nasan bazaka iya barin d’anka da yunwa ba.”……
Katse ta yayi da wata zazzafar mari sannan yace
“Ke kisan irin kalaman da zasu dinga fita a bakin ki, kuma ina mai fad’a miki da babban murya kije ki nemi Uban wannan shegen idan kuwa kika sake danganta ni da shi to ina mai tabbatar miki sai na lahira yafiki jin dad’i” yana gama fad’an haka ya fice ya barta rik’e da kuncin ta.
Sai da ya fita sannan ta dawo ta zauna ta fashe da kuka tana cewa
“Suraj ka cuce ni Ka lalata mun rayuwa ka hanani farin ciki Ka yaudare ni!”…. Sai kuma ta fashe da kuka.
Tana zaune a parlour har k’arfe goma sha d’aya na dare tana jiran Nawaf amman ina shiru ko motsin shi babu ganin hakan ne yasa ta tashi ta shiga bedroom ta kwanta dan ba k’aramin barci take ji ba.
Shi Kuwa Nawaf fita yayi wani k’aramin restaurant da yake ba nisa da gidan shi a kafa ya tafi baije da mota ba, bayan ya gama ya dawo gida ba ta babban parlour ya shiga ba ta wani ramin k’ofa da zata sadashi da d’akin sa yana zuwa yayi wanka ya shirya sannan ya kwanta.
Washe gari da sassafe Nawaf ya tashi ya shirya ya fita dan amsa kiran da mahaifin sa yake mishi daga nan kuma ya wuce office.
6:30 ya k’arasa gidan su a babban parlour’n ya samu Abban su zaune akan sallaya yana addu’a sallama yayi ya shiga ya zauna sai da Mahaifin sa ya shafa addu’ar Sa sannan ya gaida shi.
Kallon shi mahaifin sa yayi sannan yace
“Babana naji wani mummunar labari a bakin mahaifiyar ka ina son naji gaskiyar al’amafin.”
Cikin girmawa Nawaf ya kalli Abban shi sannan yace
“Abba wallahi *BA CIKI NA BANE*bansan da cikin ba Abba tunda nake da Rahma ko hannun ta ban ta6a rik’ewa ba har mukayi aure ba abinda ya shiga tsakanin mu da ita amman nayiwa Umma bayani tak’i amincewa da ni.” Sai kuma ya fashe da kuka.
“Baba idan ba kai bane waye?
Suda bakin su fa suka ce sun rufa maka asiri ne shiyasa akayi auren ba tare da an tuna ba, ko shima ba’ayi ba?”
“Abba kayi hak’uri Wallahi ban aikata komai ba Abba ban ta6a aikata sabon ubangiji ba bare kuma zina amman insha Allah Allah zai bayyana gaskiya.”
“Ameen thumma Amen Baba yanzu Ka tashi Ka shiga cikin gidan kayi Breakfast dan nasan yanzu bakayi ba Ka fito.”
Murmushi yayi sannan yace
“To Abba nagod.” Yana gama fad’an haka ya shiga cikin gidan.
Haka ya shiga suka gaisa da mahaifiyar Sa sannan Hindu ta bada mishi bearkfast bayan ya gama sannan ya musu sallama ya wuce office.
Rahma ce bata tashi a barci ba sai 10:00Am shima yunwa ne ya takura mata dan ko sallan asuba batayi ba.
A gaggauce ta yi sallah sannan ta wuce kitchen dan tasamun abinda zata ci.
Bud’e-bud’e ta fara ko zata samu wani abin amman ina bata samu komai ba har zata fita sai ta gano kwalin indomie hakan ne yasata komawa da sauri dan daman bata iya komai ba bayan indomie.
Cikin mintuna kad’an ta dafa ta soya eggs sannan ta d’auko zuwa parlour.
Tana zama ta fara ci kenan wayan ta ya fara ringing ganin number Momy ne yasata d’auka da sauri
“Hello Momy Ina kwana.”
“Lafiya k’alau wai ke ina kika shiga ne tun d’azu ina kiran wayan ki baki d’auka ba?” Ta tambaye ta.
Sai da ta saki numfashi sannan tace
“Wallahi Momy ina barci ne kuma da na tashi na shiga kitchen ne ban duba wayan ba.”
“To naji yanzu mijin naki ya fita?”
“A’a Momy ban Sani ba dan ni ban ganshi ba tun jiya.”
“To yanzu ki tashi ki shirya mu tafi wajen bokan nan Kinga dai mun màkara.”
Murmushi Rahma Tayi sannan tace
“To Momy gani nan zuwa.”
Bayan nan kuma sukayi sallama.
Misalin k’arfe sha d’aya Rahma taje gidan su basu wani 6ata lokaci ba suka wuce wani jeji wajen wani babban boka.
A nesa sukayi parking motar su sannan suka fara takawa a k’afa.
Sai da sukayi taku mai yawa sannan suka k’arasa wajen bokan.
Lokacin da sukaje ba kowa hakan ne ya basu daman shiga wajen Sa.
Rahma ce tafara sallama wani tsawa ya daka musu suka dakata.
Cikin wani irin murya yace musu
“Ba’a shiga wajen nan da sallama dan mu bama buk’atar imani anan, ko waccen ku tayi asher sannan ta shigo.”
Ai kuwa haka sukayi ko wacce sai da ta zunduma asher sannan suka shiga.
Zama sukayi sannan ya kalle su yace
“Nasan abinda ya kawo ku amman ance wak’a a bakin mai ita tafi dad’i me yake tafe da ku?”
Hajiya Saratu ce tace
“Boka daman munzo ne a biya mana buk’atar mu akan abinda yake damun ‘ya ta.”
“Muna jinki.”
Ai kuwa nan da nan ta fad’a mishi abinda yake tafe da su.
Dariya yayi sannan yace
“Wannan aikin mai sauki ne sai dai kawai kubi sharad’e kuyi abinda nace.”
Cikin rawan jiki Hajiya Saratu tace
“Menene sharad’in boka zamuyi shi.”
Dariya yayi sannan yace
“Sharad’in mu d’aya ne shine bazatayi sallah na tsawon kwana uku ba.”
Cikin sauri Rahma ta d’aga kai ta kalli mahaifiyar ta har zatayi magana Hajiya Saratu tayi sauri tace
“Ai wannan ba komai idan har burin mu zai cika.”